Majalisa Ta Fara Shirin Tsige Gwamna Fubara bayan Sabon Rikici da Wike

Majalisa Ta Fara Shirin Tsige Gwamna Fubara bayan Sabon Rikici da Wike

  • Majalisar dokokin jihar Rivers ta fara daukar matakan tsige Gwamna Siminalayi Fubara tare da mataimakiyarsa, Ngozi Oduh, bisa zargin manyan laifuffuka
  • Mambobi 26 na majalisar sun rattaba hannu kan takardar zargin, suna masu cewa abubuwan da ake tuhumansa da su sun sabawa kundin tsarin mulkin kasa
  • Matakin na zuwa ne a lokacin da rikicin siyasa tsakanin Fubara da ministan Abuja, Nyesom Wike ya sake kunno kai duk da yunƙurin sasanci da aka yi a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers – Majalisar Dokokin Jihar Rivers ta fara shirin tsige gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Oduh.

An karanta zargin ne a yayin zaman majalisar da aka gudanar a ranar Alhamis, 8 ga Janairun 2026 karkashin jagorancin Shugabanta, Rt. Hon. Martins Amaewhule.

Kara karanta wannan

Malami ya fadi manyan Najeriya 3 da za su tilasta wa Atiku janye wa Jonathan

Gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara
Gwamna Siminalayi Fubara a ofis. Hoto: Rivers State Government
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa wannan mataki ya kara dagula yanayin siyasar jihar, musamman ganin yadda aka dade ana fuskantar rikici tsakanin manyan jiga-jigan siyasar Rivers.

Majalisar Rivers na zargin Fubara da laifuffuka

A yayin zaman, Shugaban masu rinjaye na majalisar, Major Jack, ya karanta takardar zargin da ake yi wa Gwamna Fubara, inda aka bayyana cewa ana tuhumarsa da aikata manyan laifuffuka a ofis.

The Cable ta rahoto cewa takardar zargin ta nuna cewa laifuffukan, a cewar mambobin majalisar, sun sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.

An bayyana cewa mambobi 26 na Majalisar Dokokin Jihar Rivers ne suka sanya hannu kan wannan takarda, lamarin da ke nuna karfin goyon bayan matakin a cikin majalisar.

Majalisar Rivers za ta tsige Fubara

Shugaban majalisar, Martins Amaewhule, ya sanar da cewa za a mika wa Gwamna Fubara takardar zargin cikin kwanaki bakwai masu zuwa.

Ya ce wannan mataki na cikin tanadin doka, kuma majalisar za ta bi dukkan matakan da kundin tsarin mulki ya tanada wajen gudanar da shirin tsige gwamnan.

Kara karanta wannan

Ana ta tambayoyi bayan hango tambarin Grok a hoton Tinubu a Faransa

Amaewhule ya jaddada cewa majalisar ba ta daukar wannan mataki da wasa ba, sai dai domin kare doka da martabar jihar.

Ana zargin mataimakiyar Fubara da laifi

Haka zalika, Mataimakiyar Shugabar masu rinjaye ta majalisar, Linda Stewart, ta karanta takardar zargin manyan laifuffuka da ake yi wa mataimakiyar gwamna, Ngozi Oduh.

Takardar ta bayyana cewa ita ma ana tuhumarta da aikata abubuwan da suka saba wa kundin tsarin mulki, lamarin da ya sa aka shigar da sunanta cikin wadanda za a tsige.

Asalin rikicin siyasa a Rivers

Matakin majalisar ya zo ne bayan sake barkewar rashin jituwa tsakanin Gwamna Fubara da tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike, duk da cewa an taba kokarin sasanta su a baya.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya sake tsananta ne bayan wasu sababbin abubuwa da suka faru a siyasar jihar, lamarin da ya kara raba kawuna tsakanin bangarorin biyu.

Ministan Abuja, Nyesom Wike
Nyesom Wike yayin wani bayani a taro. Hoto: Lere Olayinka
Source: Facebook

A baya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taba dakatar da Fubara na wasu watanni kafin daga bisani ya dawo da shi kan kujerarsa, matakin da ya jawo ce-ce-ku-ce a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Bayan shirin barin Kwankwaso, da gaske Abba Kabir zai tarbi Aminu Ado Bayero?

An zargi Wike da raina sarakunan Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa wasu mazauna birnin tarayya Abuja sun yi korafi game da ministan FCT, Nyesom Ezonwo Wike.

Mazauna Abuja sun ce Wike ba ya girmama manyan sarakuna da masu ruwa da tsaki a yankin tun bayan nada shi minista da aka yi.

Sun yi bayanin ne bayan Wike ya ziyarci jihar Rivers ya gana da manyan 'yan siyasa da sarakunan gargajiya yayin bikin sabuwar shekara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng