Siyasar Bauchi: Kiristoci Sun Gargadi Nyesom Wike kan Rigimarsa da Gwamna

Siyasar Bauchi: Kiristoci Sun Gargadi Nyesom Wike kan Rigimarsa da Gwamna

  • Kungiyar Christian Youth in Politics (CYP) ta Bauchi ta gargadi Ministan Abuja, Nyesom Wike, da ya nisanci harkokin siyasar Jihar
  • CYP ta zargi Wike da katsalandan a siyasa, amfani da hukumomin tarayya, da matakan da ka iya barazana ga zaman lafiya a Bauchi
  • Kungiyar ta kare Gwamna Bala Mohammed, tana cewa yana da cikakkiyar kariya ta kundin tsarin mulkin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Kungiyar farar hula mai suna Christian Youth in Politics (CYP), reshen Jihar Bauchi, ta gargadi Ministan Abuja, Barrista Nyesom Wike.

Kungiyar ta tura gargadin ne ga a jiya Talata 6 ga watan Disambar 2025 Wike da cewa ya nisanci harkokin siyasar Jihar da rigima da Gwamna Bala Mohammed.

An gargadi Wike game da taba kimar Gwamna Bala
Ministan Abuja, Nyesom Wike da Gwamna Bala Mohammed. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike, Senator Bala Abdulkadir Mohammed.
Source: Twitter

An gargadi Wike kan shiga lamuran Bauchi

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya yi amai ya lashe, ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC

Sakataren kungiyar, Kwamred Ishemu Taimako Ibrahim, ya zargi ministan da katsalandan a siyasa, cewar Leadership.

Taimako ya ce yadda Nyesom Wike ke mu’amala da Gwamna Bala Mohammed na Bauchi na haifar da damuwa kan kundin tsarin mulki da tafiyar dimokuradiyya.

A cewar kungiyar, Gwamna Bala ya riga ya koka a fili kan fuskantar tsoratarwa da danniya ta siyasa, sakamakon amfani da ‘yancinsa na kundin tsarin mulki na shiga harkar siyasa, musamman kin sauya sheka zuwa APC.

Zargin amfani da EFCC da tsoratarwa

Taimako ya bayyana matukar damuwa kan zargin cewa ana amfani da hukumomin yaki da cin hanci, musamman Hukumar EFCC wajen tsoratarwa da gallaza wa Kwamishinan Kudi na Jihar Bauchi saboda dalilan siyasa, maimakon gudanar da bincike na gaskiya bisa hujjoji.

Kungiyar ta ce hakan ya saba wa ka’idojin adalci da dokar kasa, inda ta bukaci hukumomin tsaro da na bincike da su guji goyon bayan danniya ko ramuwar gayya ta siyasa.

Matasan Kiristoci sun gargadi Wike kan sukar Gwamna Bala
Gwamna Bala Mohammed na Bauchi a gidan gwamnatin jihar. Hoto: Senator Bala Abdulkadir Mohammed.
Source: Twitter

Batun kariyar gwamna a kundin tsarin mulki

CYP ta soki rahotannin da ke nuna ana kiran sunan Gwamnan Bauchi kai tsaye ko a kaikaice a binciken laifuffuka, duk da kariyar da kundin tsarin mulki ya bai wa ofishin gwamna a karkashin Sashe na 308 na Kundin Tsarin Mulkin 1999 (da aka yi wa gyara).

Kara karanta wannan

Rigima ta kara zafi, sakataren APC na kasa ya nemi Ministan Tinubu ya yi murabus

Kungiyar ta jaddada cewa ko da yake babu wanda ya fi karfin doka, bai kamata a mayar da hukumomin tsaro jagororin tsoratarwa ko matsin lamba na siyasa ba.

A cewarsu:

“Duk wani abu makamancin haka yana raunana mulkin doka, ‘yancin sauraron adalci, rarrabuwar iko, da dimokuradiyyar Najeriya.”

Nasororin mulkin Bala Mohammed a Bauchi

Kungiyar ta bayyana cewa gwamnatin Bala Mohammed ta samu nasarori masu gamsarwa wajen raya ababen more rayuwa a fadin Jihar Bauchi.

Taimako ya ce a karkashin jagorancinsa, an dauki Bauchi a matsayin daya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Arewa maso Gabas da Arewacin Najeriya, sakamakon shugabanci da ya shafi kowa, hadin kan kabilu, da dabarun shawo kan rikice-rikice.

Alaka ta yi tsami tsakanin Wike, Gwamna Bala

An ji cewa rikici tsakanin gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed da Ministan Harkokin Abuja, Nyesom Wike ya dawo danye.

Gwamna Bala ya zargi Wike da kokarin cinna wuta a jihar Bauchi kamar yadda ya furta a baya ta hanyar amfani da hukumomin gwamnatin tarayya.

Wike ya musanta zargin cewa shi ke haddasa rikici a jihar Bauchi, inda ya bukaci Gwamna Bala ya fuskanci matsalolin da ke gabansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.