'Babu Wani Mahaluki': Atiku Ya Magantu kan Janye Takarar Shugaban Kasa a 2027
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi magana game da burin takararsa a zaben 2027
- Atiku ya bayyana cewa ba zai janye daga takarar shugaban kasa na 2027 ba, yana zargin APC da katsalandan
- Ya ce ana kokarin lalata jam’iyyar ADC daga waje domin hana ta samar da ingantacciyar hamayya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya yi karin haske kan janye takara a zaɓen 2027.
Atiku Abubakar ya sha alwashin ba zai janye daga takarar shugaban kasa a zaben 2027 ba da ke tafe.

Source: Twitter
Atiku ya bugi kirji kan takara a 2027
Atiku ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata, wadda mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya sanya hannu, cewar Tribune.
A cikin sanarwar mai taken “Dimokuradiyyar Najeriya na cikin hadari,” Atiku ya zargi fadar shugaban kasa da jam’iyyar APC da tsoma baki.
Ya ce ana kokarin tsoma baki ne musamman wajen zabar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, gabanin zaben 2027.
Atiku ya kuma zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da yunkurin mayar da Najeriya kasa mai jam’iyya daya, ta hanyar raunana jam’iyyun adawa.
Ya ce wasu da ke da alaka da fadar shugaban kasa na kokarin tayar da rikici a cikin ADC ta hanyar yin katsalandan a harkokinta.
Sanarwar ta bayyana cewa duk masu neman takarar ADC za su gabatar da kansu a taron jam’iyya domin zaben dan tuta cikin gaskiya.
"Jam’iyyar ADC na kan aikin ceto kasa, Atiku Abubakar, tare da sauran masu kishin kasa, na da muhimmiyar rawa a wannan yunkuri.
" Duk wani kira a fili ko a boye da ake yi wa Atiku ya janye, hakan kira ne ga burin mulkin danniya kuma cin amanar al’ummar Najeriya."
- Cewar sanarwar

Source: Facebook
Atiku ya fadi kudirin jam'iyyar ADC
Atiku ya ce jam’iyyar ADC ta tabbatar da kudurinta na gudanar da sahihin tsari mai adalci da gaskiya wajen zabar dan takara.
Sanarwar ta ce ‘yan Najeriya sun shafe kusan shekaru uku suna fuskantar matsin tattalin arziki da kuncin rayuwa karkashin mulkin Tinubu.
Atiku ya ce gwamnatin APC na kokarin murkushe jam’iyyun adawa domin barin kanta ita kadai a fagen siyasar kasar nan.
Ya yaba wa shugabannin da suka fahimci hadarin da ke tafe, suka dunkule karkashin ADC domin samar da sahihiyar madadin kasa.
Atiku ya ce ADC na aikin ceto kasa, kuma shi tare da sauran masu kishin kasa suna da muhimmiyar rawa a wannan tafiya, cewar The Guardian.
Ya bayyana cewa idan akwai wanda ya dace ya janye daga mulki, to Shugaba Tinubu ne, wanda ya ce shugabancinsa ya kassara al'umma.
Atiku ya yi maraba da Obi a ADC
Mun ba ku labarin cewa Atiku Abubakar ya yi magana kan sauya shekar da tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, ya yi zuwa ADC.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa shigowar Peter Obi zuwa ADC, babban ci gaba ne ga bangaren adawa.
Atiku ya yi fatan cewa shigowarsa za ta kara karfin bangaren adawa domin kalubalantar masu rike da mulki da kawo ci gaba.
Asali: Legit.ng

