Mataimakiyar Gwamna da Sakataren Gwamnati Sun Fice daga PDP zuwa APC a Ribas

Mataimakiyar Gwamna da Sakataren Gwamnati Sun Fice daga PDP zuwa APC a Ribas

  • Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya na ci gaba da mamaye jihar Ribas bayan sauya shekar Gwamna Siminalayi Fubara
  • Mataimakiyar gwamnan Ribas, Farfesa Ngozi Odu da sakataren gwamnati, Dr Benibo Anabraba sun fice daga PDP zuwa APC
  • Farfes Udo ta zagaye duka yankunan karamar hukumar Ogba/Egbema/Ndoni domin wayar da kan jama'a kan shirin rijistar zama mamba a APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers, Nigeria - Mataimakiyar gwamnan jihar Ribas, Farfesa Ngozi Odu, da Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Dr Benibo Anabraba, sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC a hukumance.

Mataimakiyar gwamnan ta yi rajista a matsayin mambar APC a mazabarta da ke karamar hukumar Ogba/Egbema/Ndoni watau ONELGA.

Ngozi Odu
Mataimakiyar gwamnan jihar Ribas, Farfesa Ngozi Odu Hoto: Ngozi Odu
Source: Facebook

Mataimakiyar gwamnan Ribas ta yanki katin APC

The Nation ta ruwaito cewa ta kammala rajistar ta yanar gizo a rumfa ta 11, mazaba ta 8, Akabuka a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya kafe kan komawa APC, an ji adadin jiga jigan da za su tafi tare da shi

Sannan rahotanni sun nuna cewa Farfesa Ngozi ta zagaya yankuna shida na ONELGA domin wayar da kan jama’a kan shirin rajistar APC ta yanar gizo da ake ci gaba da yi.

Ta bukaci al’ummar yankin da su nuna goyon bayansu ga Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Siminalayi Fubara ta hanyar yin rajista da mallakar katin jam’iyyar APC.

Dalilin komawar Ngozi Odu APC

A cewarta, ta yi rijistar zama cikakkiyar mamba a APC ne domin hadewa da Gwamna Fubara, wanda tuni ya koma jam'iyya mai mulki.

“Yau na fito ne domin wayar da kan jama’a, kuma a duk inda muka je mun tarar da tulin jama’a da suka fito domin tarbar mu.
Sun ce duk inda na je, su ma can za su je, haka kuma duk inda Gwamna Fubara da Shugaba Tinubu suka dosa, su ma za su bi,” in ji ta.

Ngozi Odu ta ce ta yi rangadi a dukkan yankuna shida na karamar hukumar, wato Egi, Omoku, Osomini, Igburu, Egbema da Ndoni, inda ta kara da cewa yawan jama’ar da suka fito da irin ya nuna yadda APC ke kara samun karbuwa a yankin.

Kara karanta wannan

An dakatar da shugaban jam'iyyar PDP da aka gano yana biyayya ga ministan Abuja

Mataimakiyar gwamnan ta kuma karbi mambobin LP da suka sauya sheka zuwa APC a Ndoni, kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto.

Jam'iyyar APC.
Tutar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Hoto: @OfficialAPC
Source: Twitter

Sakataren gwamnatin Ribas ya bar PDP

A bangarensa, Sakataren Gwamnatin Jihar Ribass, Dr Benibo Anabraba, ya fice daga PDP a cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata 5 ga Janairu, 2026, wadda ya aikewa shugaban PDP na mazabarsa a karamar hukumar Akuku-Toru.

A cikin wasikar, Dr Anabraba ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin PDP bayan dogon nazari kan halin da jam'iyyar ke ciki. Ya kuma sanar da shiga APC.

An dakatar da shugaban PDP na Ribas

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar PDP reshen jihar Ribas ta dakatar da shugaban kwamitinta na rikon kwarya, Robinson Ewor.

Rahotanni sun nuna cewa an dakatar da shugaban jam'iyyar PDP na Ribas, Robinson Ewor ne bayan ya fito fili ya bayyana goyon bayansa ga Ministan Abuja, Nyesom Wike.

Tun farko, Mista Ewor ya zargi Gwamna Siminalayi Fubara da yaudarar shugabannin jam’iyyar da magoya baya yayin takaddamar siyasar da ta dabaibaye jihar, lamarin da PDO ba ta ji dadinsa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262