PDP Ta Yi Rashi, Tsohon Sanata Ya Fice daga Jam'iyyar bayan Shekara 20

PDP Ta Yi Rashi, Tsohon Sanata Ya Fice daga Jam'iyyar bayan Shekara 20

  • Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta gamu da koma baya biyo bayan ficewar wani tsohon sanata daga cikinta a Sokoto
  • Sanata Abdallah Wali ya yi murabus daga jam'iyyar hamayya ta PDP bayan ya kwashe fiye da shekara 20 a cikinta
  • Tsohon sanatan ya yi godiya ga jam'iyyar bisa damarmakin da ta ba shi a tsawon lokacin da ya kwashe yana cikinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Tsohon Sanata kuma masani kan harkokin diflomasiyya, Abdallah M. Wali, ya fice daga jam’iyyar PDP.

Abdallah Muhammad Wali ya fice daga PDP ne bayan shafe sama da shekaru 20 yana tare da jam’iyyar.

Jam'iyyar PDP ta rasa tsohon sanata a jihar Sokoto
Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Kabiru Tanimu Turaki Hoto: Kabiru Tanimu Turaki SAN
Source: Instagram

Jaridar TheCable ta ce tsohon sanatan ya bayyana ficewarsa daga PDP ne a cikin wata wasika da ya fitar.

Sanata Abdallah Wali ya bar PDP

Ficewarsa dai na cikin wata wasika mai ɗauke da kwanan wata 31 ga Disamba, 2025, wadda ya aike wa shugaban PDP na mazabar Sanyinna a karamar hukumar Tambuwal ta jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

An dakatar da shugaban jam'iyyar PDP da aka gano yana biyayya ga ministan Abuja

A cikin wasikar, Abdallah Wali ya bayyana cewa murabus ɗinsa ya fara aiki nan take, jaridar The Punch ta kawo labarin.

“Ina sanar da ficewa ta daga jam’iyyar PDP, tare da dukkanin sassan jam’iyyar da nake cikinsu. Wannan murabus ɗin ya fara aiki nan take.”

- Abdallah Wali

'Dan siyasar ya gode wa PDP bisa damar da ta ba shi na hidima ga jam’iyyar da kasa a matsayi daban-daban.

Haka kuma, ya gode wa magoya bayansa bisa tsayawa tare da shi na fiye da shekaru 20, yana mai bayyana goyon bayansu a matsayin abin alfahari da ba za a iya misaltawa ba.

An kuma aika kwafin wasikar murabus ɗin zuwa ga shugaban PDP na karamar hukumar Tambuwal, da kuma shugaban jam’iyyar na jiha a Sokoto.

Har ya zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoto, Abdallah Wali bai bayyana inda zai dosa a siyasa ba.

Sanata Abdallah Wali ya yi murabus daga jam'iyyar PDP
Tsohon sanata a Sokoto, Abdallah Wali Hoto: Alh Showshow Mai Matawallen
Source: Facebook

Tsofaffin sanatoci na barin jam'iyyar PDP

A ranar 26 ga Disamba, Gilbert Nnaji, tsohon sanata kuma tsohon shugaban kwamitin majalisar dattawa kan sadarwa, shi ma ya fice daga jam’iyyar PDP bayan shafe shekaru 27.

Kara karanta wannan

PDP ta kausasa harshe kan ficewar Gwamna Mutfwang zuwa jam'iyyar APC

Tsohon sanatan ya sanar da ficewarsa ne a cikin wasikar da ya aike wa shugaban PDP na mazabar Umuenwene a Iji Nike, karamar hukumar Enugu ta Gabas.

Sanata Gilbert Nnaji ya ce shawarar da ya yanke ta kasance mai wahala, la’akari da burin cigaban kasa da damar da PDP ta ba da a baya domin Najeriya.

PDP ta fusata kan ficewar Gwamna Mutfwang

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta yi martani mai zafi kan ficewar gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, zuwa APC mai mulki a Najeriya.

PDP ta ce ta ɗauki ficewar Gwamna Caleb Mutfwang daga jam’iyyar a matsayin cin amana da kuma yaudarar al’ummar da suka yarda da shi duk da kalubalen da ya fuskanta.

Jam'iyyar ta ce babu wani dalili mai karfi a kundin tsarin mulki da zai halasta wannan mataki da gwamnan ya ɗauka na barin PDP da komawa jam’iyyar APC, ba tare da sauka daga kujerar gwamna nan take ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng