NNPP Ta Fadi Abin Zai Iya Faruwa da Ita idan Abba Kabir Ya Fice zuwa APC
- Jam’iyyar NNPP a Najeriya ta yi tsokaci game da rade-radin cewa Gwamna Abba Kabir zai iya barin cikinta zuwa APC
- NNPP ta ce za ta tsallake rikicin siyasa a Kano duk da jita-jitar cewa Gwamnan na shirin sauya sheka zuwa APC
- Shugabancin NNPP na kasa ya rushe dukkan tsare-tsaren jam’iyyar a Kano daga matakin jiha zuwa gunduma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Sakataren Yada Labarai na Kasa na Jam’iyyar NNPP, Ladipo Johnson ya magantu kan rigimar siyasa da ta kunno kai a Kano.
Johnson ya bayyana cewa jam’iyyar za ta iya tsallake rikicin da ke addabar ta a Jihar, duk da rade-radin cewa Gwamna Abba Kabir na shirin sauya sheka.

Source: Facebook
NNPP ta yi magana kan rikicin siyasar Kano
Da yake magana a wata hira da ARISE News, Johnson ya ce matakin an dauke shi ne domin dawo da doka da oda tare da kare kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Johnson ya ce rushe dukkan tsare-tsaren jam’iyyar a Kano, daga matakin jiha zuwa kananan hukumomi da mazabu, ba zai kawo karshen NNPP ba, ko da kuwa gwamnan ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar.
Rahoton ya ce rikicin siyasar ya kunno kai ne tsakanin jagoran NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano, da kuma Gwamna Abba Yusuf, sakamakon jita-jitar komawar gwamnan zuwa jam’iyyar APC mai mulki a kasa.
Kwankwaso ya nuna adawa da wannan mataki, lamarin da ya kara rura wutar rikicin cikin jam’iyyar.
A sakamakon haka, Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) na NNPP ya yanke shawarar rushe shugabancin jam’iyyar a Kano gaba daya.
Ya ce:
“Mun yarda kuma mun san cewa za mu tsira komai ya faru. Abin takaici, mun samu matsala a Jihar Kano.”

Source: Facebook
'Musabbabin rikicin NNPP a jihar Kano'
Johnson ya bayyana cewa rikicin ya fara ne lokacin da wasu mambobin jam’iyyar suka yi yunkurin dakatar ko tsige shugaban jam’iyyar na jiha ta hanyoyin da ba su dace da kundin tsarin mulki ba.
A cewarsa, kundin tsarin mulkin NNPP bai yarda a tsige shugaba a matakin jiha daga mazabarsa ba, don haka shugabancin kasa ya tsoma baki domin gyara kura-kuran da aka yi.

Kara karanta wannan
Kwankwaso ya tara 'yan Kwankwasiyya a;hali Abba na shirin hada kai da Ganduje a APC
Ladipo ya kara da cewa shugabancin ya ga dacewar rushe dukkan tsare-tsaren jam’iyyar a Kano domin samar da kwanciyar hankali.
Dangane da fargabar cewa wannan mataki zai hanzarta sauya shekar Gwamna Yusuf zuwa APC, Johnson ya ce bai yarda da hakan ba.
Ya bayyana cewa daya daga cikin manyan hadiman gwamnan ya taba cewa gwamnan da Kwankwaso za su koma APC tare, amma jagoran ya musanta hakan.
Kotu ta hana Dungurawa kiran kansa shugaban NNPP
Mun ba ku labarin cewa jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano ta samu kanta cikin rikici biyo bayan dakatar da shugabanta, Hashimu Sulaiman Dungurawa.
Batun dakatar da Hashimu Sulaiman Dungurawa ya kai gaban kotu, inda aka yanke hukunci a kan takaddamar da ake yi.
Mai shari'a Zuwaira Yusuf ta hana Dungurawa bayyana kansa a matsayin shugaban jam'iyyar NNPP na reshen jihar Kano.
Asali: Legit.ng
