Wata Sabuwa: Wike Ya Hango Abin da Zai Zama Karshensa a Siyasa
- Dambarwar siyasar jihar Rivers ta kara zafi tsakanin Ministan birnin tarayya Abuja da Gwamna Siminalayi Fubara
- Wike ya bayyana cewa ba zai sake maimaita kuskuren da ya yi ba wajen bari Gwamna Fubara ya yi tazarce a zaben 2027
- Ministan ya bayyana babbar barazanar da zai fuskanta a siyasance idan har Gwamna Fubara ya samu damar yin tazarce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Rivers - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan makomarsa a siyasa.
Wike ya bayyana cewa makomar siyasarsa za ta lalace matuka idan gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya samu wa’adi na biyu a mulki.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce Wike ya fadi hakan ne a ranar Asabar, 3 ga watan Disamban 2025 yayin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki a wani taro da aka gudanar a karamar hukumar Okrika ta jihar Rivers.
Menene zai kawo karshen siyasar Wike?
Ko da yake bai ambaci sunan gwamnan kai tsaye ba, Ministan ya bayyana cewa tuni an yanke shawara mai tsauri game da zaben gwamna na 2027, jaridar TheCable ta dauko labarin.
“Mun riga mun yanke shawara game da Tinubu. Amma game da wancan (sake zaben Fubara), ba zai yiwu ba."
"Domin idan muka sake yin kuskure, to siyasar mu za ta mutu. Ba zan bari a binne ni a siyasa ba. Ba zan sake yarda a yi irin wannan kuskure ba. Saboda haka, kowa ya sani mun riga mun yanke shawara."
- Nyesom Wike
Ministan ya kara tsananta sukar Fubara tun bayan da gwamnan ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a watan da ya gabata.
Wike ya zargi gwamnan da karya sharuddan yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma kafin a dage dokar ta-baci a jihar, wadda ta bai wa Fubara damar komawa kan kujerarsa.
Wike na adawa da tazarcen Gwamna Fubara
A ranar Talata, 30 ga watan Disamban 2025 Wike ya ce “kuskuren shugabanci” da aka yi a jihar Rivers za a gyara shi a shekarar 2027, inda ya yi alkawarin bayyana cikakkun bayanai na yarjejeniyar zaman lafiyar da ta mayar da Fubara kan mulki.
A wata magana da ya yi wacce ke nuni ga Fubara, Ministan ya ce shugabanni an zabe su ne domin bauta wa muradin jama’a, ba wai bin son zuciya ba.
“Ba za mu sake yin kuskure iri daya a matakin jiha ba a 2027. Amma za mu yi bayani dalla-dalla idan lokaci ya yi."
- Nyesom Wike
Haka kuma, a ranar Juma’a, 2 ga watan Janairun 2025 yayin wani taro da masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Ogba/Egbema/Ndoni, Wike ya ce goyon bayan da Fubara ke bai wa Tinubu ba zai taimaka masa ya samu wa’adi na biyu ba.

Source: Twitter
Ya jaddada cewa shi kansa ya goyi bayan Tinubu tun kafin gwamnan ya shiga APC.
“Idan ka yi wasa da na farko ka yi nasara, kana tunanin za ka yi na biyu ka yi nasara? Ba a cin kasuwa biyu a rana daya."
"Saboda haka, duk wanda yake tabbatar maka cewa komai zai yi tafi daidai da zarar ka rera wakar kamfen [ta Tinubu], to ka yi kuskure."
- Nyesom Wike
Jam'iyyar ADC ta caccaki Wike
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC reshen jihar Rivers ta yi martani mai zafi kan sukar da Nyesom Wike ya yi a kanta.
Jam'iyyar ADC ta bayyana cewa Nyesom Wike, ba ya cikin kowace jam’iyyar siyasa, don haka ba shi da ikon magana a madadin kowace jam’iyya.
ADC ta bayyana cewa Wike yana yin maganganu ne saboda takaicin da yake ji na kasa sarrafa gwamnan jihar Rivers.
Asali: Legit.ng


