"Abin da Ya Fi Mani Ciwo game da Sauya Shekar Gwamna Abba zuwa APC," Kwankwaso

"Abin da Ya Fi Mani Ciwo game da Sauya Shekar Gwamna Abba zuwa APC," Kwankwaso

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna damuwarsa kan shirin gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf na komawa jam'iyyar APC
  • Jagoran NNPP na kasa ya tabo babban abokin hamayyarsa a Kano, tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje
  • Kwankwaso ya yi wa masu zuga Gwamna Abba ya koma APC shagube, yana mai cewa ya kamata su sa shi ya bar wa NNPP kujerar gwamna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Tsohon dan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana bacin ransa kan shirin Gwamna Abba Kabir Yusuf na komawa APC.

Jagoran NNPP ya tabbatar wa al'ummar Kano da sauran mabiyansa da ke fadin Najeriya cewa ba shi da shirin sauya sheka tare da Abba Gida-Gida.

Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.
Jagoran NNPP na kasa, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: @SaifullahiHon
Source: Facebook

A wani rahoto da Freedom Radio ta wallafa a Facebook, Kwankwaso ya ce babban bakin cikinsa shi ne yadda Abba zai dauki gwamnatin da suka sha wahala suka kafa ya mika wa 'yan APC.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Kwankwaso ya bi hanyoyi 2, ya yi yunkurin tsige Abba daga kujerar gwamnan Kano

Ya ce babban abin bacin ran, gwamnatin za ta koma tsagin tsohon shugaban APC na kasa kuma tsohon gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wanda babban abokin hamayya ne ga Kwankwaso.

Gwamna Abba na shirin komawa APC

Ya fadi haka ke a wani faifan bidiyo da DCL Hausa ta wallafa, mai dauke da jawabin Kwankwaso a wurin taron masu ruwa da tsaki na Kwankwasiyya, wanda ya gudana jiya Juma'a.

Kalaman Kwankwaso na zuwa ne a lokacin da jita-jita ta fara tabbata cewa Gwamna Abba zai tattara magoya bayansa, ya koma jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Bayanai daga majiyoyi daban-daban sun nuna cewa Abba zai sauya sheka zuwa APC a mako mai zuwa, matukar ba a samu wani sauyi daga baya ba.

A martanin da ya yi kan shirin Abba, Kwankwaso ya ce babu sa hannunsa kuma ba da shi za a yi wannan tafiya ba.

Abin da ya fi yi wa Kwankwaso ciwo

Ya kuma numa matukar bacin ransa kan matakin da gwamnan Kano ke shirin dauka, yana mai cewa bai kamata ya dauki wahalar da suka yi ya mika wa Ganduje ba.

Kara karanta wannan

Kano ta dauki zafi, Kwankwaso ya fito ya yi magana kan komawa APC tare da Gwamna Abba

A kalamansa, Injiniya Kwankwaso ya ce:

"Ba abu mai ciwo sama da a dauki akushin wannan Gwamnati da mu ka kafa, a kai wa Ganduje."
Kwankwaso da Ganduje.
Jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso da tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje Hoto: @KwankwasoRM
Source: Twitter

Haka kuma, Kwankwaso ya soki wadanda suka zuga Gwamna Abba ya bar NNPP zuwa APC, yana mai tsokanarsu da cewa ya kamata su zuga shi ya bar kujerar gwamna a inda ya same ta.

Yadda Kwankwaso ya nemi a tsige Abba

A baya, kun ji cewa ana zargin jagoran NNPP na kasa, Rabiu Kwankwaso ya yi yunkurin tsige gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf amma bai cimma nasara ba.

Wata majiya ta ce Kwankwaso ya tsara sauke Abba daga mulkin Kano ta hanyoyi biyu, wadda hanya ta farko ita ce hana gwamnan tikitin neman wa'adi na biyu a zaben 2027.

Hanya ta biyo ita ce amfani da 'yan Majalisar dokokin Kano, wadanda suka shaida wa Kwankwaso cewa suna tare da mai girma gwamna.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262