APC Ta Manta da Rawar da Wike Ya Taka, Ta Fadi Jagoran Jam'iyyar a Rivers

APC Ta Manta da Rawar da Wike Ya Taka, Ta Fadi Jagoran Jam'iyyar a Rivers

  • Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya raba fada game da wanda zai jagoranci jam'iyyar APC a Rivers
  • Yilwatda ya ayyana Gwamna Siminalayi Fubara a matsayin jagoran jam’iyyar APC a Jihar Rivers bayan gwamnan ya dawo cikinta
  • Tsoho ministan ya ce dole Fubara ya yi aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki domin haɗin kai da tafiyar da jam’iyya yadda ya kamata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Port Harcourt, Rivers - Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya fadi wanda zai zama jaogran jam'iyyar a Rivers.

Yilwatda ya bayyana Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, a matsayin jagoran jam’iyyar APC a jihar.

An ayyana jagoran APC a Rivers
Ministan Abuja, Nyesom Wike da Gwamna Siminalayi Fubara. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike da Sir Siminalayi Fubara.
Source: Facebook

Jam'iyyar APC ta fadi jagoranta a Rivers

Yilwatda ya faɗi hakan ne yayin wata hira da ya yi a shirin 'Hard Copy' na gidan talabijin na Channels.

Kara karanta wannan

PDP ta kausasa harshe kan ficewar Gwamna Mutfwang zuwa jam'iyyar APC

Ya ce tsarin APC ne ta amince da gwamnonin da ke kan mulki a matsayin shugabannin jam’iyya a jihohinsu.

Sai dai shugaban jam’iyyar ya jaddada cewa dole ne Gwamna Fubara ya haɗa kai da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da shigar kowa da kowa da kuma kyakkyawan tsari a cikin jam’iyyar.

Ya ce:

“Gwamna Fubara shi ne jagoran APC a Jihar Rivers, amma dole ne ya daidaita aiki da dukkan sauran mutane a jihar.
"A dukkan jihohi, gwamnonin da ke kan mulki ne ke jagorantar jam’iyya, amma muna buƙatar su tabbatar da haɗin kai.”
An ayyana Gwamna Fubara a matsayn jagoran APC a Rivers
Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers. Hoto: Sir Siminalayi Fubara.
Source: Facebook

Yadda ake zaben fitar da gwani a APC

Da aka tambaye shi ko APC za ta goyi bayan Fubara idan ya nemi wa’adi na biyu, Yilwatda ya ce dole ne gwamnan ya bi tsarin jam’iyya na zaɓen fitar da gwani, kamar yadda aka yi a Jihar Ekiti, inda gwamna mai ci ya fafata da sauran ’yan takara kafin ya zama ɗan takarar APC.

Ya ƙara da cewa duk tattaunawa da ta shafi harkokin APC a Jihar Rivers za a yi ta ne da Gwamna Fubara, ba da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ba, wanda har yanzu mamba ne a jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Gwamna Mutfwang ya koma APC bayan ficewa daga PDP, ya fadi dalili

“Idan tattaunawa ne da mambobin APC. Nyesom Wike ba mamba ba ne na jam’iyyarmu, don haka ba za mu tattauna da shi kan harkokin jam’iyyar APC ba.”

- In ji Yilwatda.

Ya kuma ƙaryata ra’ayin cewa Wike na da tasiri a siyasar APC a Rivers, yana mai cewa jam’iyyar ta fi mayar da hankali ne kan ’ya’yanta, ba waɗanda ba mambobi ba.

Wike ya caccaki Fubara kan siyasa

An ji cewa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya zargi Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, da karya yarjejeniyar da Bola Tinubu ya sasanta su.

Wike ya ce nan ba da jimawa ba zai fallasa cikakkun bayanan yarjejeniyar da aka cimma a gaban Shugaban kasa domin kawo karshen rikicin.

Ministan ya gargadi Fubara kan makomarsa ta siyasa, yana mai cewa magoya bayansa sun shirya “gyara kuskuren” zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.