Magana Ta Kare: Gwamna Mutfwang Ya Koma APC bayan Ficewa daga PDP, Ya Fadi Dalili

Magana Ta Kare: Gwamna Mutfwang Ya Koma APC bayan Ficewa daga PDP, Ya Fadi Dalili

  • Gwamnan jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang ya yi sabuwar jam'iyya bayan ya raba gari da tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP
  • Caleb Mutfwang ya koma jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya a hukumance a ranar Juma'a, 2 ga wata Janairun 2026
  • Gwamna Mutfwang ya yi cikakken jawabi kan dalilin da ya sanya ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Gwamnan jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya koma jam’iyyar APC a hukumance.

Gwamna Caleb Mutfwang ya koma jam'iyyar APC ne bayan ya fice daga tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP.

Gwamna Mutfwang ya koma jam'iyyar APC
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang Hoto: Caleb Mutfwang
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta kawo rahoton cewa shugaban jam’iyyar APC a jihar Plateau, Rufus Bature, ne ya mika masa katin zama ɗan jam’iyyar APC a ranar Juma’a, 2 ga watan Janairun 2026 a birnin Jos.

Kara karanta wannan

Ana rade radin komawa APC, mataimakin gwamnan Kano ya tura sako ga Abba da Kwankwaso

Meyasa Gwamna Mutfwang ya koma APC?

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Mutfwang ya ce sauya shekar da ya yi zuwa APC na da nasaba da muradun jihar Plateau.

Caleb Mutfwang ya bayyana cewa matakin da ya dauka na sauya sheka zai amfani al’ummar jihar gaba ɗaya.

Gwamnan, wanda ya yi alkawarin mulki na bai ɗaya da kowa duk da sauya jam’iyya, ya yi kira ga al’ummar jihar da su zauna lafiya su kuma kasance tsintsiya madaurinki ɗaya a kowane lokaci, jaridar TheCable ta dauko rahoton.

"Tafiyar da muka fara tafiya ce ta yarda, kuma na yi amanna cewa Plateau za ta samu ribar wannan haɗin gwiwa."
"Na san akwai masu shakku, amma ina cewa ku yi hakuri. Lokaci zai bayyana komai. Ga masu jin tsoro, ina cewa ku kara karfin gwiwa, kada ku ƙmkara tsoro, domin mun zo ne da niyyar zama."
"Mun zo ne domin haɗa hannu, mun zo ne domin yin aiki tare. Ga duk wanda ke cikin fargaba, kamar yadda na faɗa tun da farko, ku kwantar da hankalinku.”

Kara karanta wannan

An sanya ranar da gwamnan Filato zai shiga jam'iyyar APC bayan ya fice daga PDP

- Gwamna Caleb Mutfwang

Gwamna Caleb Mutfwang ya sauya sheka zuwa APC
Gwamna Caleb Mutfwang a wajen sauya shekarsa zuwa APC Hoto: Prof Nentawe Yilwatda
Source: Facebook

Gwamna Mutfwang ya godewa PDP

Gwamnan ya gode wa jam’iyyar PDP, wadda ya fice daga cikinta, bisa ba shi dama da tsari da suka taimaka masa a tafiyarsa ta siyasa.

Ya ce komawarsa APC za ta kara masa kwarin gwiwa wajen samar da ingantaccen shugabanci a jihar.

Gwamna Mutfwang ya kuma gode wa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa irin kaunar da yake nuna wa jihar Plateau, inda ya yi alkawarin mara masa baya a zaɓen 2027.

Gwamna Mutfwang ya yi murabus daga PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya raba gari da jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya.

Gwamna Mutfwang ya tabbatar da ficewarsa daga PDP, yana mai cewa yana bukatar shugabanci mai tsari da ingantacciyar hidima ga al'ummarsa domin kawo abubuwan ci gaba.

Hakazalika, gwamnan ya gode wa shugabannin jam’iyyar PDP da magoya bayanta bisa goyon bayan da suka ba shi tsawon shekaru, yana cewa halin siyasar yanzu ya tilasta masa daukar matakin ficewa daga cikinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng