Gwamnatin Tinubu Ta Yi Karin Haske game da Zargin Shirin Yi wa Ƴan Adawa Ɗauki Ɗai Ɗai
- Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris ya yi magana game da zargin cewa gwamnati ta yi shirin cafke ko kai ’yan adawa kotu saboda siyasa
- Gwamnati ta ce takardar da ke yawo game da “ADP4VIP” ƙarya ce tsagwaron ta kuma babu wani shiri da ake yi a kan daƙile ƴan adawa
- Ya gargadi jama’a kan yaɗa ƙarya a kan cewa an yi wani shiri na kame ƴan adawa yayin da ake tunkarar zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Ministan yaɗa labarai da wayar da kan ƴan ƙasa, Mohammed Idris, ya musanta jita-jitar da ke cewa gwamnatin tarayya na da shirin cafke, tsarewa ko gurfanar da ’yan adawa a kotu ba bisa ƙa’ida ba.
Mohammed Idris ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, yana mai cewa wata takarda da ke yawo a kafafen sada zumunta wadda ke ɗauke da irin waɗannan zarge-zarge ƙarya ce.

Source: Facebook
The Cable ta wallafa cewa a cewar ministan, takardar ta yi ƙoƙarin nuna kamar an kafa wani shiri na haɗin gwiwar hukumomi da ake kira “ADP4VIP — Arrest, Detain, Prosecute for Very Important Persons”.
Gwamnati ta ƙaryata shiri kama ƴan adawa
Daily Post ta wallafa cewa sanarwar ta ce wannan shiri wai zai haɗa da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Hukumar ICPC don muzguna wa jama'a.
Haka kuma ya ce babu shiri da Hr Bibiyar Kuɗin Haram (NFIU), tare da haɗin gwiwar Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro a kan ’yan adawa.
Mohammed Idris ya ce wannan zargi ba shi da tushe balle makama, yana mai jaddada cewa babu wani irin wannan shiri da aka taɓa ƙirƙira ko tattaunawa a kai.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta maida hankali ne kan aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziƙi, ƙarfafa tsaro, faɗaɗa damar kasuwanci.

Source: Twitter
Ministan ya ce:
“Ƙoƙarin wasu ’yan adawa na mayar da ɗaukar matakin doka da bin ka’ida kamar ana tsangwamar siyasa, wata dabara ce mai haɗari da ake amfani da ita domin kare wasu da ake kira manyan mutane daga fuskantar dokokin ƙasa da hukumomin yaƙi da cin hanci.”
Gwamnati ta gargadi jama’a kan yaɗa ƙarya
Ministan ya tunatar da cewa sashe na 40 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya tanadi ’yancin haɗuwa da yin taro ga kowane ɗan ƙasa, kuma ba za a tauye wannan hakki ba.
Ya ce Shugaba Tinubu ya rantse wajen kare kundin tsarin mulki da kuma tabbatar da wadannan ’yancin ba tare da wani yunkuri na hana ƴan adawa cin gajiyarsa ba.
Ya kuma jaddada cewa gwamnati na ci gaba da mutunta bin doka da oda, da kuma ’yancin hukumomin tsaro da na shari’a, yana mai cewa waɗannan hukumomi na aiki ne bisa ƙwarewa.
Ministan ya gargadi ’yan siyasa da al’umma gaba ɗaya da su guji yaɗa bayanan ƙarya, ruɗani da labaran bogi, musamman yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.
Majalisa ta miƙa buƙata ga gwamnatin Tinubu
A baya, mun wallafa cewa Majalisar Wakilan Najeriya ta buƙaci a dakatar da aiwatar da sababbin dokokin gyaran haraji da aka amince da su kwanan nan, biyo bayan zargin yi masa canje-canje.
Wannan buƙata ta zo ne duk da cewa Majalisar Tarayya ta riga ta amince da dokokin tare da tura su ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda aka ce ya sanya musu hannu.
Sai dai daga bisani aka fara zargin cewa nau’ukan dokokin da aka wallafa ba su yi daidai da waɗanda ’yan majalisa suka amince da su ba, lamarin da ya tayar da ƙura a Najeriya.
Asali: Legit.ng


