NNNP, Kwankwaso Sun Amince Ƴaƴan Ƴan Majalisun Kano da Suka Rasu Su Gaje Su
- Jam’iyyar NNPP ta amince ‘ya’yan marigayi ‘yan majalisar Kano da suka rasu su nemi takara a madadinsu
- Yayan yan majalisun da suka rasu sun hada da Sa’ad Aminu Sa’ad da Nabil Aliyu Daneji wadanda aka sanar sun bar duniya a rana daya
- Amincewar ta biyo bayan shawarwari da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya jagoranta, tare da manyan shugabannin jam’iyya da iyalan marigayin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Jam’iyyar NNPP ta yi wa iyalan yan majalisun jihar Kano da suka rasu tayin neman kujerun iyayensu.
Jam'iyyar ta amince Sa’ad Aminu Sa’ad da Nabil Aliyu Daneji, ‘ya’yan yan majalisar Kano, su fafata neman kujerun mahaifan na su.

Source: Facebook
NNNPP ta magantu kan kujerun yan majalisar Kano
Shugaban NNPP na Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa, ya ce an cimma yarjejeniyar ne bayan tattaunawa da shugabannin jam’iyya da iyalan marigayan, cewar Leadership.
Kujerun Majalisar Dokokin birnin Kano da Ungogo sun zama babu kowa ne bayan rasuwar ‘yan majalisar da ke wakiltarsu a ranar 24 ga Disamba, 2025.
Amincewar ta biyo bayan shawarwari da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya jagoranta, inda manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar suka cimma matsaya.
Dungurawa ya bayyana cewa Kwankwaso ya karɓi baƙuncin taron a gidansa da ke Kano, inda aka tattauna hanyoyin cike guraben majalisar cikin mutunci.
Ya ce:
"An samu fahimta da girmamawa a kowane bangare, mun zauna, mun yi magana cikin gaskiya, sannan muka amince da tsarin.”

Source: Facebook
Kwankwaso ya fadi musabbabin daukar matakin
Kwankwaso ya ce matakin na nufin girmama ayyukan ‘yan majalisar da suka rasu tare da nuna jajircewar jam’iyyar kan adalci da dimokuraɗiyyar cikin gida.
Ya jaddada cewa amincewar ba ta nufin ba wa kowa kujera kai tsaye ba, domin dole su fafata ta hanyar tsarin jam’iyya.
Ya kara da cewa Sa’ad da Daneji za su fuskanci tantancewa da zaɓe kamar sauran masu neman takara ba tare da wani fifiko ba.
Dungurawa ya bayyana fatan cewa ‘ya’yan za su ci gaba da kyawawan ayyukan hidima da jajircewar da iyayensu suka yi suna a kai, cewar Daily Post.
Ya bukaci mambobin jam’iyyar su goyi bayan tsarin, yana mai tabbatar da cewa za a gudanar da zaben maye gurbin cikin kwanciyar hankali da bin ƙa’idoji.
NNPP ta ce za a gudanar da dukkan matakan ne bisa dokokin jam’iyya da ka’idojin zaɓe, tare da mutunta doka da tsarin dimokuraɗiyya.
Aminu Ado ya jajanta rasuwar yan majalisun Kano
Mun ba ku labarin cewa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya nuna matuƙar alhini kan rasuwar ‘yan majalisar Kano guda biyu.
'Yan majalisar da suka rasu, Aminu Sa’ad Ungogo da Sarki Aliyu Daneji, sun wakilci Ungogo da birnin Kano, inda suka yi aiki da kishin jama’a.
Sarkin ya yi addu’ar Allah ya gafarta musu, ya ba iyalansu haƙuri, tare da miƙa ta’aziyya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da Majalisar Kano.
Asali: Legit.ng

