Nentawe: Shugaban APC Ya Fadi Abin da Ya Koya wajen Shugaba Tinubu

Nentawe: Shugaban APC Ya Fadi Abin da Ya Koya wajen Shugaba Tinubu

  • Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya taka muhimmiyar rawa a siyasar da yake yi
  • Shugaban na APC ya bayyana cewa Tinubu ya koya masa abubuwa sosai wadanda suka shafi harkokin siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana abin da yake koyo a wajen Shugaba Bola Tinubu.

Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa yana koyon harkokin siyasa ne daga Shugaba Bola Tinubu.

Nentawe ya yaba Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Hoto: @DOluaegun, @OfficialAPCNg
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta ce Yilwatda ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 27 ga watan Disamban 2025 yayin nadin da aka yi masa da sarautar gargajiya mai taken “Kaeh-rit”.

An yi masa nadin sarautar ne a karamar hukumar Kanke ta jihar Plateau, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da labarin.

Kara karanta wannan

Wike ya fadi abin da Shugaba Tinubu ya fi shi samu a fagen siyasar Najeriya

Abin da Nentawe ya koya a wajen Tinubu

Da yake jawabi bayan kammala bikin, Yilwatda ya ce ci gaban siyasar da ya samu ya samo asali ne daga tasirin Shugaba Tinubu, wanda ya bayyana a matsayin daya daga cikin fitattun jagororin siyasa mafi nagarta a Najeriya.

“Daga shugaba mafi kwarewa nake koyo, Asiwaju Tinubu. Shugaban kasa na daga cikin mafi kyawun ’yan siyasa da mutum zai koyi abu daga gare su. Tun lokacin da ya dauke ni a matsayin dansa, na koyi abubuwa da dama daga gare shi."
“Yana koyar da ni, kuma ina koyo. Idan kuna ganin ina samun nasara, to saboda ina koyo ne daga mafi kwarewar dan siyasa da Najeriya ta taba samarwa."
"To me zai hana? Zan yi aiki tukuru domin na cimma irin abin da ya cimma, domin ni ma na zama daya daga cikin fitattun ’yan siyasa a Najeriya."

- Farfesa Nentawe Yilwatda

A matsayin wani bangare na bukukuwan nadin sarautar, shugaban na APC ya bayar da gudummawar kudi naira miliyan 10, da iri da sauran kayan aikin noma ga manoma a karamar hukumar Kanke domin karfafa samar da abinci.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaba Tinubu ya nemi daukin kasar waje bayan Amurka

Ya ce wannan mataki ya yi daidai da ajandar Shugaba Tinubu na inganta tsaron abinci da rage talauci a kasa.

Me Nentawe ya ce kan sauya shekar gwamnan Plateau?

Yilwatda ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa cewa jihar Plateau za ta samu karin ci gaba bayan sauya shekar Gwamna Caleb Mutfwang zuwa jam’iyyar APC.

Nentawe ya ce ya koyi siyasa wajen Tinubu
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Hoto: Prof Nentawe Yilwatda
Source: Twitter

Ya jaddada cewa APC tana tafiya ne bisa tsarin ba kowa dama, inda dukkan mambobi ke da hakki iri daya, ba tare da la’akari da lokacin da suka shiga jam’iyyar ba.

“Duk wanda ya shigo APC a yau yana da hakki iri daya da wanda ya shafe shekaru aru-aru a cikinta, domin ba ma bambanta tsakanin mambobinmu."
“Wasu na cewa idan ka shiga jam’iyya, za su ce su ne ’yan asalin jam’iyyar saboda sun dade a ciki."
“Ba mu da wannan a APC. Yayin da gwamnati ta shigo tare da magoya bayanta, za mu zama iyali daya tilo da za su yi aiki tare domin amfanin jihar Plateau."

- Farfesa Nentawe Yilwatda

Wannan sarauta ita ce ta biyu da shugaban na APC ya samu cikin kasa da makonni biyu, bayan wata girmamawa da al’ummar kabilar Tiv a jihar Benue suka yi masa kwanan nan, bisa gudummawar jin kai da yake bayarwa.

Kara karanta wannan

Babban limami ya fito ya gayawa Tinubu gaskiya kan mulkin Najeriya

Shugaban APC ya yi nade-nade

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi muhimman nade-nade.

Farfesa Nentawe Yilwatda, ya amince da naɗin masu ba da shawara na musamman da manyan mataimaka na musamman.

APC ta ce ana sa ran waɗanda aka naɗa za su yi amfani da ƙwarewarsu da kwarewar aiki wajen tallafa wa ayyukan shugaban jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng