Atiku Ya Hakura da Takara, Ya ba Obi Damar Tsayawa? An Samu Gaskiyar Zance
- Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi karin haske game da takararsa a zaben 2027
- An yi ta yada wasu rahotannin da ke cewa an bukace shi da ya janye daga takarar shugabancin ƙasa a zaɓen 2027
- Kungiyar Atiku ta jaddada cewa tana shirye-shiryen kalubalantar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓe da ke tafe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya magantu kan taararsa a zaben 2027 da ke tafe.
Atiku wanda ya yi takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2023 ya musanta labarin janye takararsa a zaben da ake tunkara.

Source: Facebook
Atiku ya musanta janye takara ga Obi
Sai dai mai ba Atiku shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya musanta labarin a shafinsa na X.
Ibe ya yi watsi da rahotannin da ke cewa ya yi watsi da burinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Atiku ya bayyana irin waɗannan rahotanni a matsayin ƙarya da ruɗani, bayan wasu labarai sun yi iƙirarin cewa jigon jam’iyyar ADC ya janye takararsa domin bai wa Peter Obi.
Rahoton ya yi zargin cewa Atiku ya goyi bayan Obi ya yi wa’adi guda ɗaya kacal, yana mai cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya fahimci buƙatar daidaiton yankuna a mulkin Najeriya.
A sakon da ya wallafa tare da hoton rahoton a shafinsa, Ibe ya rubuta cewa wannan magana da ake magana karya ce kuma ko kadan babu kamshin gaskiya a ciki.
Ibe ya ce:
“Labarin karya ne, ba ya cikin jadawalinmu!”

Source: Facebook
Atiku da wasu sun nemi sauye-sauye guda biyar
A wani bangare kuma, Atiku ya soki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan gyare-gyaren haraji da take shirin aiwatarwa.
Atiku ya ce ‘yan Najeriya sun riga sun sha wahala sakamakon almubazzaranci, cin hanci da rashawa, rashin ingantaccen shugabanci da girman kai a manufofi.
Ya kara da cewa bai dace gwamnatin Tinubu ta rika gyara gazawar gwamnati ta hanyar dora wa talakawa nauyin biyan kudin kura-kuran gwamnati ba.
Bayan haka, jigon ADC ya jero bukatu guda biyar da hadakar ‘yan adawa ke nema, yayin da Atiku da jam’iyyar ADC suka fara shirye-shiryen kalubalantar Shugaba Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Hakan na zuwa ne yayin ake ta shirye-shiryen gudanar da zaben 2027 duk da yawan ficewa daga jam'iyyun adawa zuwa APC mai mulkin Najeriya.
Atiku ya zargi Tinubu kan kudin kananan hukumomi
A wani labarin, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya taso Bola Ahmed Tinubu a gaba kan batun 'yancin kananan hukumomi.
Atiku Abubakar ya yi zargin cewa akwai abin da shugaban kasar yake son cimmawa shi ya sa ya ki aiwatar da hukuncin Kotun Koli tun tuni.
Ya ce shugaban kasar na nuna baki biyu kan batun 'yancin kananan hukumomi, abin da ya ke fadi da wanda yake aikatawa suka bambanta.
Asali: Legit.ng

