Yahaya Bello na Tsara Yadda Gwamna Ododo ke Tafiyar da Mulki a Kogi
- Gwamna Usman Ododo, ya ce yana tafiyar da gwamnatinsa yadda Yahaya Bello ya so kuma yana aiki yadda ya kamata wajen samar da sakamako mai kyau
- Ya bayyana cewa shi ma ya taba zama cikin wani gungu na siyasa (cabal) a zamanin Yahaya Bello, amma waccan gungun bai yi tasiri kamar na shi ba
- Ododo ya ce idan gungun da aka kafa zai taimaka wajen gudanar da mulki, to babu laifi a samu irinsu da dama matukar suna aiki domin farfado da jihar Kogi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kogi – Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya bayyana cewa yana tafiyar da wani gungu a cikin gwamnatinsa, yana mai cewa wannan tsarin ne ke taimaka masa wajen samun nasara a ayyukan da yake aiwatarwa.
Ododo ya fadi haka ne yayin da yake jawabi ga jama’a a wajen kaddamar da wani aiki a jihar, inda ya ce ba ya boye gaskiyar cewa yana da wadanda da ke taimaka masa wajen yanke shawara da aiwatar da manufofi.

Source: Twitter
The Cable ta rahoto cewa Ododo ya kara da cewa, sabanin yadda ake kallon samar da makusanta a siyasar Najeriya a matsayin wata kungiya mai illa, nasa suna aiki ne yadda ya kamata
Ododo ya yi magana kan mulkin Yahaya Bello
Daily Post ta rahoto gwamnan ya bayyana cewa shi ma a baya ya taba zama cikin wani gungu a karkashin tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello.
A cewarsa:
“Ni ma na taba zama cikin cabal, amma namu a wancan lokacin ba su iya aiki kamar yadda wannan yake aiki a yanzu ba.”
Ya ce wannan ne ya sa yake jaddada cewa ba samar da gungun masu fada a ji ne matsala ba, illa yadda ake tafiyar da shi da irin rawar da suke takawa a mulki.
Yahaya Bello ya zabawa Ododo jami'ai
Ododo ya bayyana sunan shugabar makusantansa cewa ita ce Hajiya Dr. Habibat Tijani Aliyu, babbar akantar jihar, yana mai cewa tsohon gwamna Yahaya Bello ne ya amince da nadinta.
Ya ce:
“Shugabar makusanta na, wadda Mai Girma Alhaji Yahaya Bello ya amince da ita, ita ce Hajia Dr. Habibat Tijani Aliyu.”
Gwamnan ya ce babban mai binciken kudi na jihar na cikinsu, haka nan shugaban jam’iyya, da kuma kwamishinan kananan hukumomi da harkokin sarauta duk na cikin makusatan sa.
Ododo ya ce nasarar mulki na rataye ne a kan yadda kungiyoyin da ke kusa da shugaba ke aiki. Ya ce idan makusantan gwamna za su taimaka wajen tafiyar da gwamnati cikin tsari da gaskiya, to babu laifi a samu irin hakan.

Source: Twitter
Ododo ya zama gwamna ne bayan ya taba rike mukamin babban mai binciken kudi na kananan hukumomi a zamanin Yahaya Bello, wanda ya mulki Kogi daga 2016 zuwa 2024.
Yahaya Bello na tare da Bola Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya yi magana game da cewa ya samu sabani da Bola Tinubu.
A cewar Yahaya Bello, babu wani abu maras dadi da ya faru tsakaninsa da shugaba Tinubu, kamar yadda wasu ke fada.
Tsohon gwamnan ya ce yana tare da Tinubu dari bisa dari kuma yana goyon bayan ayyukan da gwamnatinsa ke yi a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


