NNPP Ta Yi Sabon Shugaba bayan Gudanar da Babban Taronta Na Kasa
- Jam'iyyar NNPP mai adawa a Najeriya ta tara manyan jiga-jiganta domin gudanar da babban taronta na kasa a Abuja
- An gudanar da babban taron ne domin zabar shugabannin da za su ci gaba da jan ragamar jam'iyyar har na tsawon shekara hudu
- A yayin babban taron, an zabi shugaban NNPP na kasa tare da mambobin kwamitin gudanarwa na kasa (NWC)
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam’iyyar NNPP ta gudanar da babban taronta na kasa inda ta zabi shugabannin da za su ja ragamarta.
Jam'iyyar NNPP ta sake zaɓen Ajuji Ahmed a matsayin shugabanta na kasa.

Source: Twitter
Jaridar TheCable ta ce an sake zaɓen Ajuji Ahmed ne a ranar Asabar, 20 ga watan Disamban 2025 a babban taron jam’iyyar na ƙasa da aka gudanar a Abuja.
NNPP ta zabi shugabanni
Ajuji Ahmed zai ci gaba da rike mukamin shugabancin jam'iyyar NNPP na tsawon shekaru huɗu masu zuwa, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar da hakan.
Jam’iyyar NNPP ta kuma sake zaɓen sauran mambobin kwamitin gudanarwa na kasa (NWC).
Daga cikinsu akwai Abba Kawu, mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa (Arewa); Onu Nwaze, mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa (Kudu); Dipo Olayokun, sakatare na kasa; da Oladipo Johnson, sakataren yaɗa labarai na ƙasa.
Sauran da aka sake zaɓa sun haɗa da Ibrahim Muhammad, mataimakin sakatare na kasa; Bala Mohammed, sakataren tsare-tsare na ƙasa; Ahmed Balewa, ma’aji na kasa; Akpan Ekan, sakataren kuɗi na kasa.
Hakazalika an zabi Maryam Yasin, shugabar mata ta kasa; Muhammad Musa, shugaban matasa na kasa; Magaji Ibrahim, mai bada shawara kan harkokin shari’a na kasa; da Mustapha Danhajia, sakataren walwala na kasa.
Haka kuma an zaɓi Sadiq Abubakar, mai binciken kuɗi na kasa, Bashir Abacha, jami’in hulɗa na kasa, Shehu Bello, mataimakin shugaban jam'iyya na kasa (Arewa maso Yamma), Abubakar Abdulrahman, mataimakin shugaban jam'iyya na kasa (Arewa ta Tsakiya).

Source: Facebook
Daga cikin wadanda aka zaba kuma akwai Stanley Ijeh, mataimakin shugaban jam'iyya na kasa (Kudu maso Kudu), Ademola Ayaode, mataimakin shugaban jam'iyya na kasa (Kudu maso Yamma); Collins Onuoha, mataimakin shugaban jam'iyya na kasa (Kudu maso Gabas) da Abdulrahman Auwal, wakilin masu nakasa.
Shugaban kwamitin shirya babban taron na kasa, Bala Mohammedo, ya ce an gudanar da zaɓen ne bisa ka’ida da kuma bin dokoki da sharuɗɗan hukumar zaɓe ta INEC.
Shugaban NNPP ya yi jawabi
A nasa jawabin, Ajuji Ahmed ya ce an sake gina NNPP domin ta zama babbar jam’iyya mai tasiri a tsarin dimokuraɗiyyar kasar nan.
“Idanun kowa na kan babbar jam’iyyarmu domin ta nuna hanya mai kyau wajen samar da dimokuraɗiyya mai ɗorewa da ci gaba a Najeriya.”
"Kasarmu na bukatar sabon farawa, kuma ’yan kasa sun cancanci sabon tsari mai inganci, wanda NNPP kaɗai ke da ikon bayarwa.”
- Ajuji Ahmed
Mambobin NNPP sun koma APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar NNPP ta rasa wasu daruruwan mambobi da take da su a jihar Kano.
Jam’iyyar APC ta karɓi sababbin mambobi 774 da suka sauya sheka daga jam’iyyar NNPP a gundumar Rimin Gado da ke jihar Kano.
Shugaban mutane 774 da suka koma APC, Mohammad Karofin-Yashi, ya bayyana cewa matakin da suka dauka ya samo asali ne daga ganin irin ci gaban da jam’iyyar APC ke kawowa jihohi.
Asali: Legit.ng


