Bayan Shiga APC, Gwamna Fubara Ya Bayyana Shirinsa kan Tazarcen Tinubu a Zaben 2027

Bayan Shiga APC, Gwamna Fubara Ya Bayyana Shirinsa kan Tazarcen Tinubu a Zaben 2027

  • Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya sake jaddada goyon bayansa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Siminalayi Fubara ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya riga ya samu goyon bayan mutanen jihar Rivers
  • Gwamnan ya nuna cewa Shugaba Tinubu ya kusa samun kaso 100 na goyon baya a jihar mai arzikin man fetur

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Rivers - Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya yi magana kan shirin tazarcen Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Gwamna Fubara ya ce shirye-shiryen neman goyon baya ga Bola Ahmed Tinubu gabanin babban zaɓen 2027 sun kai kusan kashi 70 cikin 100 a faɗin jihar.

Fubara ya nuna goyon baya ga Tinubu
Gwamna Siminalayi Fubara da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: @SimFubaraKSC, @DOlusegun
Source: Twitter

Jaridar The Punch Gwamna Fubara ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin kaddamar da aikin titin Ogbakiri mai tsawon kilomita 9.7 a jaramar hukumar Emuoha.

Kara karanta wannan

Wuju Wuju: Abba Kabir ya kwarara yabo ga Tinubu, ɗan majalisar APC a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna SImi Fubara ya samu yabo

Gwamnan ya ce kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar APC ya amince da karfin tsarinsa da kuma jajirtattun magoya bayansa, wanda a cewarsa za su samar da goyon bayan da ake buƙata ga shugaban kasa a 2027.

Ya ce kwarin gwiwarsa na karuwa ne sakamakon irin tarba da goyon bayan da yake samu a yayin kaddamar da ayyuka a sassa daban-daban na jihar.

Me Fubara ya ce kan Bola Tinubu?

Da yake jawabi ga taron jama’a, Gwamna Fubara ya ce:

“Bisa yardar Allah jiya (Laraba) na kai ziyara kwamitin gudanarwa na kasa na babbar jam’iyyarmu, kuma bayan taron, sun ba ni sako wanda yanzu nake isarwa gare ku."
“Sun ce mun san kai gwamna mai aiki tukuru ne. Mun san kana da sahihin goyon baya daga tushe, ka mika wannan goyon bayan zuwa nasarar jagoranmu, Bola Ahmed Tinubu."
"Na kuma faɗa musu a taron cewa kada su damu, abin da ya fi muhimmanci shi ne muna da ‘sojoji’" gaskiya.

Kara karanta wannan

Sarki ya hada tawaga zuwa wajen Tinubu, sun goyi bayan tazarcensa a 2027

“Yau kuma ina farin ciki da abin da nake gani a nan, muna da goyon bayan karamar hukumar, daga shugaban karamar hukuma, shugabannin gargajiya, sarakuna da kowa a nan, aikinmu ya riga ya kai kashi 70 cikin 100.”
Gwamna Fubara ya ce Tinubu ya samu goyon baya a Rivers
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara a ofis Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Source: Facebook

Fubara ya tuno kalubalen da ya fuskanta

Da yake tsokaci kan titin Ogbakiri, Gwamna Fubara ya bayyana aikin a matsayin muhimmin shiri da aka fara a wani lokaci mai matuƙar kalubale a gwamnatinsa.

Ya tuno cewa an biya kashi na farko na kuɗin aikin ne a lokacin da hukuncin kotu ya hana gwamnatin tarayya sakin kudaden da doka ta tanada ga jihar Rivers.

Fubara ya tabbatar wa mazauna yankin cewa an kammala titin kamar yadda aka yi alkawari duk da kalubalen da aka fuskanta, tare da yin alkawarin duba yiwuwar faɗaɗa hanyoyin ciki da kuma haɗa sabon titin da Degema ta hanyar gina wata gada da ake shirin yi.

Kudin da Gwamna Fubara ya tarar

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Rivera, Sminalayi Fubara, ya ce ya tarar da biliyoyi bayan ya dawo kan mulki.

Gwamna Fubara ya bayyana cewa ya tarar da N600bn a asusun jihar Rivers bayan an cire dokar ta baci na kimanin watanni shaida.

Kara karanta wannan

NLC: Ajaero ya fadi sabon alkawarin da Tinubu ya dauka game da rashin tsaro

Hakazalika, kwararren akantan ya bayyana cewa ya bar N300bn a asusun gwamnati kafin a ayyana dokar ta baci a jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng