Hukumar BOSIEC Ta Sanar da Sakamakon Zaben Kananan Hukumomin Jihar Borno
- Hukumar zabe ta jihar Borno ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomin da aka gudanar ranar Asabar, 13 ga watan Disamba, 2025
- Jam'iyyar APC ta samu nasarar lashe dukkan kujerun ciyamomi da kansilolin a fadin kananan hukumomi 27 na jihar Borno
- Tun a ranar Asabar, Gwamna Babagana Umaru Zulum ya bayyana cewa yana da kwarin gwiwar APC za ta samu nasara a zaben
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Borno, Nigeria - A karshen makon da ya gabata ne hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Borno ta gudanar da zaben kananan hukumomi a fadin jihar da ke Arewa maso Gabas.
Zaben dai ya gudana a fadin kananan hukumomi 27 da ke jihar Borno a ranar Asabar, 13 ga watan Disamba, 2025.

Source: Facebook
An sanar da sakamakon zaben Borno
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa jam’iyyar APC ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi da na kansiloli a kananan hukumomi 27 na Jihar Borno.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Borno (BOSIEC), Dr. Tahir Shettima, shi ne ya sanar da sakamakon zaben a yammacin yau Litinin a Maiduguri.
Dr. Tahir ya jero sakamakon zaben ne yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a hedikwatar hukumar BOSIEC da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
BOSIEC ta ce an yi zabe cikin lumana
Ya kuma tabbatar da cewa jama'a sun ba da hadin kai, an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana a fadin mazabun jihar.
A cewarsa, hukumar BOSIEC da yake jagoranta, ta gudanar da zaben ne bisa tanade-tanaden da suka dace na Dokar Zabe ta 2022.
Ya yaba wa jam’iyyun siyasa da suka fafata zaben, tare da sauran masu ruwa da tsaki da suka hada da jami’an tsaro, kungiyoyin farar hula, ‘yan jarida da kuma kungiyar hadakar jam'iyyu (IPAC) na Jihar Borno.
A cewarsa, zaben ya gudana cikin lumana tare da kammala shi cikin nasara sakamakon bisa jajircewar da masu da tsaki suka yi.

Kara karanta wannan
Matawalle: Kungiya ta ba Tinubu shawarar abin da ya dace da karamin Ministan tsaro
Hukumar BOSIEC ta yabawa Gwamna Zulum
Dr. Tahir ya kuma jinjinawa Gwamna Babagana Umara Zulum, bisa jajircewarsa wajen karfafa dimokuradiyya a matakin kananan hukumomi ta hanyar samar da kudaden da aka yi amfani da su wajen gudanar da zabukan.
Ya bukaci zababbun shugabannin kananan hukumomin da kansiloli da su tabbatar da kafa nagartaccen wakilci ta hanyar kawo alfanun dimokuradiyya ga al’umma a matakin tushe.

Source: Facebook
Tun farko, Zulum, ya bayyana a ranar Asabar, yayin da yake kada kuri’arsa a Mafa, garinsu na haihuwa, cewa jam’iyyarsa APC za ta yi nasara a zaben, cewar rahoton The Cable.
PDP ta tsame kanta daga zaben Borno
A baya, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta ce ba za ta shiga zaben kananan hukumomi da hukumar zabe ta BOSIEC za ta gudanar a jihar Borno a ranar Asabar ba.
Jam'yyar PDP ta dauki wannan mataki ne bayan da ta yi zargin cewa hukumar zaɓen jihar ba za ta yi adalci ba, kuma an tsuga kudi a takardun neman takara.
PDP ta ce BOSIEC ta gaza ba jam'iyyun adawa tabbacin cewa za ta gudanar da sahihin zabe, don haka tana zargin ba za ta yi adalci ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

