El Rufa'i Ya Yi Karin Haske game da Goyon Bayan Obi ko Atiku a Zaben 2027

El Rufa'i Ya Yi Karin Haske game da Goyon Bayan Obi ko Atiku a Zaben 2027

  • Tsohon jigon APC, Malam Nasir El-Rufai ya musanta rahotannin da ke cewa ya bayyana yankin da kamata ya fito da Shugaban 'Kasa a 2027
  • Tsohon gwamnan ya ce bai taɓa goyon bayan wani ɗan takara ko yankin ƙasa ba a cikin jawabi ko rubutunsa game da siyasar kasar nan
  • Tsohon gwamna na Kaduna, El-Rufai ya gargadi ‘yan jarida da jama’a kan yada bayanan da ba a tantance su ba a kafafen sada zumunta

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna –Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya karyata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa ya bayyana yankin da ya dace ya fito da shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

El-Rufai ya bayyana irin waɗannan rahotanni a matsayin labaran ƙarya da aka ƙirƙira domin yaudarar jama’a da rikita tunanin ‘yan ƙasa.

Kara karanta wannan

An fara gunaguni bayan mai tsaron Tinubu ya zama Birgediya Janar a soja

Nasir El-Rufa'i ya musanta goyon bayan dan takara a zaben 2027
Nasir El-Rufa'i, Atiku Abubakar da Peter Obi Hoto: ADC 2027 Coalition
Source: Twitter

A rubutun da ya wallafa a shafin Facebook, El-Rufa'i ya yi tir da wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa ya ce lokaci ya yi da yankin Kudu zai sake fitar da shugaban ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasir El-Rufa'i ya karyata nuna dan takararsa

Har ila yau, rahotannin sun yi zargin cewa yana goyon bayan tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, maimakon tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar.

Sai dai, El-Rufai ya musanta duk waɗannan rahotanni. Ya ce bai taɓa yin irin wannan magana ba, ko a jawabi, ko a hira, ko a rubutunsa na kafafen sada zumunta.

A cewarsa, yana da shafuka na gaskiya da yake amfani da su wajen faɗar ra’ayinsa kai tsaye, kuma duk abin da bai fito daga waɗannan hanyoyi ba, ba nasa ba ne.

El-Rufa'i ya gargadi jama'a game da yada karya

El-Rufai ya kuma yi Allah-wadai da jingina shi da ra’ayoyi ko sharhi da wasu suka rubuta, wanda ya ke ganin hakan bai dace ba sam.

Kara karanta wannan

APC: Atiku da manyan 'yan adawa sun taso Tinubu a gaba game da mamaye Najeriya

El-Rufa'i ya gargadi masu yada labarin karya
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i Hoto: Nasir El-Rufa'i
Source: Facebook

Tsohon gwamnan ya soki abin da ya kira siyasar rashin tarbiyya da kuma yin amfani da kafafen sada zumunta wajen yaɗa labaran ƙarya.

Ya buƙaci ‘yan jarida da jama’a su koma bin ƙa’idar tantance labarai kafin wallafawa ko rabawa. Ya ce a wannan zamani da ake fama da ruɗani da ƙarya, tabbatar da sahihancin bayani ya fi komai muhimmanci.

El-Rufai ya yi gargaɗi cewa al’umma za su tagayyara idan shugabannin kafafen yaɗa labarai suka ƙi yin bincike, suka rungumi jita-jita daga masu rashin kishin gaskiya a kafafen sada zumunta.

Ya jaddada cewa babu wani ra’ayi da ya kamata a jingina masa, sai wanda ya faɗa a fili a shafukansa na gaskiya ko a hirarraki da kafafen yaɗa labarai masu sahihanci.

El-Rufa'i ya koma jam'iyyar ADC

A baya, mun wallafa cewa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shiga jam’iyyar hamayya ADC a hukumance, watanni bayan barinsa jam’iyyar APC mai mulki da SDP a Najeriya.

Kara karanta wannan

"Sako ya kai ga Shugaban Ƙasa:" Sheikh Asada ya shirya zuwa kotu da Matawalle

Rahotanni sun nuna cewa El-Rufai ya kammala rajistarsa ta shiga ADC tare da karɓan katin zama zama cikakken 'dan jam'iyya a ofishin da ke mazabarsa ta Unguwar Sarki a birnin Kaduna.

Ana kallon shiga ADC a matsayin wani muhimmin mataki a sabon shafin siyasar El-Rufai, musamman ganin yadda jam’iyyar ke ƙoƙarin ƙarfafa matsayinta a matsayin wata dandalin adawa gabanin babban zaɓen 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng