APC: Atiku da Manyan 'Yan Adawa Sun Taso Tinubu a Gaba game da Mamaye Najeriya
- Manyan ‘yan adawa sun gargadi Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu kan barazanar jam’iyya ɗaya da ya ce ana yi wa Najeriya
- Wadanda suka bayyana takaicinsu sun hada da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar da kuma Sanata David Mark
- Sun zargi gwamnati da amfani da hukumomin tsaro da yaki da cin hanci don tsoratar da 'yan adawa gabanin babban zaben 2027
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Manyan jagororin adawa sun gargadi Shugaba Bola Tinubu, inda suka zarge gwamnatinsa da sanda a kokarinta na mayar da Najeriya tsarin jam’iyya ɗaya.
Sun yi zargin cewa gwamantin APC na amfani da hukumomin gwamnati wajen tsoratar da abokan adawa gabanin zaɓen 2027. Sun ce wannan yanayi na barazana ga makomar dimokuraɗiyyar ƙasa.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa a cikin sanarwar haɗin gwiwa, jagororin sun bayyana damuwa cewa hukumomin yaki da cin hanci da na tsaro suna kokarin muzguna wa 'yan adawa ba dalili.
Atiku da sauran 'yan adawa sun soki Tinubu
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa manyan 'yan adawa suun ce wannan fahimta da ake yi wa hukumomin tsaro da na yaki da rashawa na lalata amincewar jama’a ga hukumomin ƙasa.
Sanarwar ta samu sa hannun tsohon Shugaban Majalisar Dattawa David Mark; tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi.
Sauran wadanda suka sa wa sanarwar hannu sun hada da tsohon Mataimakin Shugaban PDP, Cif Bode George; tsohon Shugaban APC na ƙasa, Cif John Odigie-Oyegun; da Mallam Lawal Batagarawa.
'Yan adawa suna zargin APC da murkushe adawa
A cewarsu, akwai ɓoyayyen shiri na kawo dukkannin gwamnatocin jihohi ƙarƙashin jam’iyyar mai mulki, ba ta hanyar sahihin zaɓe ba, sai dai ta hanyar matsin lamba da binciken yaki da cin hanci.
Sun nuna cewa sauya sheƙar gwamnonin adawa zuwa APC a baya-bayan nan ya ƙara ƙarfafa zargin jama’a cewa tilas ne ke jawo sauyin, ba akida ko ra’ayi ba.
Sun ce wannan lamari ya wuce gwamnonin da ke kan mulki, ya shafi manyan ‘yan adawa da ke tattaunawar haɗin gwiwa don 2027.

Source: Facebook
Jagororin sun zargi EFCC da kasancewa mai rauni ga tasirin siyasa, inda ake watsi da zarge-zarge kan ‘yan jam’iyya mai mulki, yayin da ake gaggauta bincike da shari’ar kafafen watsa labarai kan ‘yan adawa.
Sun tuna da maganar da aka taɓa dangantawa da tsohon shugaban APC cewa ana iya yafe zunuban masu sauya sheƙa.
'Yan adawa sun yi gargaɗin cewa wannan hali na lalata amincin yaƙi da cin hanci, yana raunana hukumomi, kuma na iya haddasa tashin hankali yayin da zaɓe ke gabatowa.
Atiku Abubakar ya gana da Goodluck Jonathan
A baya, mun wallafa cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya kai ziyara ga tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, a gidansa da ke birnin tarayya Abuja.
Atiku Abubakar ya kai ziyarar ne a ranar Asabar, 6 ga watan Disamban 2025, inda manyan jagororin biyu suka yi ganawar sirri da ta ja hankalin masu bibiyar siyasar Najeriya.
Atiku Abubakar ya bayyana a cewarsa, abin farin ciki ne sake haɗuwa da tsohon Shugaban Kasa, Jonathan bayan dawowarsa daga wata muhimmiyar tafiya a ƙasashen wajen Najeriya.
Asali: Legit.ng


