Kefas: Gwamnan da Fice daga PDP Kwanan nan Ya Yanki Katin Zama Ɗan Jam'iyyar APC

Kefas: Gwamnan da Fice daga PDP Kwanan nan Ya Yanki Katin Zama Ɗan Jam'iyyar APC

  • Gwamnan Taraba, Agbu Kefas, ya yi rajistar zama dan APC a hukumance, inda ya karɓi katin jam’iyya daga shugabannin mazaba
  • Kefas ya ce rajistar ta zama wajibi domin ya samu cikakken ikon jagorantar harkokin APC da kuma karfafa tafiyar mulki a jihar
  • Sauya shekar Kefas na zuwa ne yayin da manyan ‘yan siyasa da ‘yan majalisa a Taraba ke komawa APC gabanin zabuka masu zuwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jalingo – Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya yi rajista a hukumance a jam’iyyar APC a ranar Lahadi, inda ya tabbatar da sauya sheƙarsa zuwa jam’iyya mai mulki.

Shugaban jam'iyyar APC na mazabar mazabar Hospital Ward ne ya yi wa Gwamna Kefas rajista a wani karamin taro a gidan gwamnati da ke Jalingo, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

'Ku yi likimo', Ganduje ya fadawa 'yan APC dabarar nasara a 2027

Gwamna Abdu Kefas ya zama cikakken dan jam'iyyar APC bayan rajista da mallakar kati.
Gwamna kefas Agbu ya na daga sabon katin shaidarsa ta zama dan jam'iyyar APC. Hoto: @GovAgbuKefas
Source: Twitter

Kefas ya tabbatar da shigarsa APC

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Gwamna Agbu Kefas ya bayyana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ba da dadewa ba, na karɓi katin zama ɗan jam’iyyar APC daga Hannun Hon. Umaru Tanko, shugaban APC na Hospital Ward a karamar hukumar Wukari.
“Ina godiya da tarbar da shugabanni da mambobin APC a Taraba suka yi min.”

Dalilin gwamnan na yin rajista da wuri

Da yake jawabi bayan rajistar da kuma karɓar katin jam’iyya, Kefas ya ce ko da yake ya dakatar da bikin sauya sheƙarsa a hukumance wanda aka shirya yi a ranar 19 ga Nuwamba, saboda juyayi kan sace ‘yan makaranta mata a jihar Kebbi, ya ga dacewar daukar wannan mataki domin ya samu damar tafiyar da harkokin jam’iyyar yadda ya kamata.

Gwamna Kefas ya ce:

“Tun da farko na rubuta wa jam’iyya a matakin mazaba, kuma wannan rajista na daga cikin muhimman abubuwan da dole a cikasu. Za ku tuna cewa na dakatar da bikin shiga APC saboda sace ‘yan mata a Kebbi.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: APC ta yi wa gwamna rijista, ya zama cikakken 'dan jam'iyyar

“Ko da an yi bikin, wannan rajistar dole ce a yi ta. Ina gode wa shugabannin jam’iyyar a mazabata da wakilan kwamitin aiki na jiha da suka halarta.”
Gwamna Kefas Agbu ya ce ya yi rajistar APC ne domin ya ja ragamar jam'iyyar tun yanzu.
Gwamna Kefas Agbu yana karbar katin shaidar zama cikakken dan jam'iyyar APC. Hoto: @GovAgbuKefas
Source: Twitter

Tasirin sauya sheƙar gwamnan a Taraba

Gwamnan ya ce an dauki matakin ne domin amfanin jam’iyyar da kuma kyautata tafiyar mulki a Taraba, yana mai jaddada cewa shigarsa APC za ta kara dankon hadin kai da karfafa ginshikin jam’iyyar a jihar.

Ya kuma bayyana cewa za a sanar da jama’a sabuwar ranar da za a gudanar da bikin sauya sheƙarsa a hukumance nan gaba, in ji rahoton jaridar Punch.

Rajistar Kefas na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sauye-sauyen siyasa a jihar Taraba, inda manyan ‘yan siyasa ke sake daidaita shirinsu gabanin zabuka masu zuwa.

'Yan majalisa 15 sun koma jam'iyyar APC

Tun da fari, mun ruwaito cewa,kakakin majalisar dokoki, Izito Benzena, tare da ‘yan majalisar dokokin jihar Taraba 14, sun sauya sheƙa zuwa APC.

Kakakin majalisar Taraba ya bayyana cewa ya fice daga PDP zuwa jam'iyyar APC ba don wata manufa ta kashin kansa ba, sai don maslahar jihar Taraba.

Kara karanta wannan

Bayan komawa APC, Gwamna Fubara ya yi wa Tinubu alkawari kan zaben 2027

Hon. Bonzena ya kuma roƙi magoya bayansa da kada su fassara matakin da wani tunani mara kyau, domin an dauke shi ne da niyyar gyaran jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com