Sanata Natasha Ta Tona Yadda Ake Neman Ta Shiga APC daga Fadar Shugaban Kasa
- Sanata Natasha Akpoti ta bayyana matsayarta game da niyyar komawa jam’iyyar APC, duk da tulin yan siyasa da ke sauya sheka
- Natasha ta ce ta fuskanci kalubale a siyasa saboda batun jihar da mijinta ya fito, tana kira ga mata su jajirce duk da wahalhalun siyasa
- Ta jaddada cewa babu wata barazana ko zuga da za ta sa ta koma APC, tana cewa kasancewarta a jam’iyyar a baya ba hujjar komawa ba ce
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lokoja, Kogi - Sanata Natasha Akpoti ta fito da maganganu game da yiwuwar komawa jam'iyyar APC a Najeriya.
Natasha ta tabo batun kalubale da take fuskanta a siyasa duba da jihar da mijinta ya fito game da takarar wata kujera a rayuwarta.

Source: Facebook
Natasha ta magantu kan yiwuwar komawa APC
Natasha ta bayyana haka yayin hira ta musamman a wani bidiyo da TheCable ta bibiya kuma ta wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin hirar, Natasha ta ce ba za ta taba komawa APC ba saboda wasu dalila nata na karan kanta.
Sanatar ta ce har yanzu akwai wasu daga fadar shugaban kasa da ke ci gaba da yi mata tayin ta dawo APC.
Ta ce:
"Har lokacin da na yi aure, ana ce min mijinki daga jihar Delta yake, ya kamata ki je can ki yi takarar zabe, ke ba yar Kogi ba ce yanzu.
"Daman na shirya fusknatar haka, zan fadawa duk wata mace za ta iya fuskantar matsaloli kuma zai zama mai wahala amma ki jajirce."

Source: Facebook
Yadda ake zawarcin Sanata Natasha zuwa APC
Da aka tambaye ta maganar sake komawa APC, Natasha ta ce tabbas ta taba kasancewa a APC na dan wani lokaci amma yanzu zai yi wahala.
A cewarta:
"A'a, ba zan koma APC ba, a baya, na kasance a APC na wani lokaci, me yasa zan koma APC?.
"Babu abin da zai sanya ni kawai na bi zuga don suna komawa APC, babu wata barazana da za ta sanya ni komawa APC.
"Wasu daga fadar shugaban kasa suna yawan min tayi na koma APC lokuta da dama, jiya ma wani ya min magana kan haka."
Natasha ta fadi yadda take ji a PDP
Natasha ta ce tana jin dadin inda take a siyasance kuma bata da niyyar shiga APC mai mulkin Najeriya.
Wannan martani na ta na zuwa yayin da APC ke ci gaba da kwashe yan siyasa daga jam'iyyun adawa daban-daban zuwa cikinta.
Rigimar Natasha da Akpabio ta dawo sabuwa
Kun ji cewa za a fafata shari'a tsakanin shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan.
Sanata Godswill Akpabio ya yanke shawarar shigar da kara gaban kotu kan zargin da Sanatar Kogi ta yi masa na yunkurin cin zarafinta.
Natasha ta yi farin ciki kan karar da shugaban majalisar dattawan ya shigar da ita, inda ta nuna cewa hakan ya sanya ta samu wata babbar dama.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

