Zaben 2027: Jam'iyyar ADC Ta Nuna Shakku kan Tafiyar Atiku da Peter Obi
- Wasu na hasashen akwai matsala a tafiyar hadaka wadda jagororinta suka koma jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya
- Mai magana da yawun ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya nuna shakku kan yiwuwar aiki tare tsakanin Atiku Abubakar da Peter Obi
- Sai dai duk da haka, Bolaji Abdullahi, ya bayyana abin da jam'iyyar ADC ta sanya a gaba a fagen siyasar Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC ta yi tsokaci kan manyan jagororin tafiyar hadaka, Atiku Abubakar da Peter Obi.
Jam'iyyar ADC ta nuna damuwa kan yadda Atiku Abubakar da Peter Obi ba su aiki tare domin tunkarar zaɓen 2027.

Source: Facebook
Mai magana da yawun ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa a shirin Morning Show na tashar Arise Tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me ADC ta ce kan Atiku da Peter Obi?
Lokacin da aka tambaye shi kan batun, Bolaji Abdullahi ya yi amanna cewa jam’iyyar na cikin damuwa dangane da rashin haɗin gwiwa tsakanin Obi da Atiku.
“Ba zan iya bayyana lamarin da kalmomi masu tsanani ba har in ce shi ne babbar barazana ga dimokuraɗiyya a wannan lokaci. Amma shin matsala ce? Eh. Shin ƙalubale ne? Eh. Kuma shin muna damuwa da shi? Eh.”
- Bolaji Abdullahi
Mai magana da yawun ADC ya kuma bayyana cewa a halin yanzu jam’iyyar ba ta tattauna batun ɗan takarar shugaban kasa ba, sai dai ta fi mayar da hankali ne kan ƙarfafa tsarin jam’iyyar a faɗin kasa.
“A wannan lokaci, babu wani a ADC da ke tattaunawa kan wanda zai zama ɗan takarar shugaban kasa.”
“Akwai aiki mai yawa a gabanmu, na tabbatar da kasancewarmu a kasa da kuma samun damar tsayawa takara a dukkan jihohi 36 da babban birnin tarayya, Abuja.”

Kara karanta wannan
Sanusi II ya yi wa 'yan siyasa tonon silili, ya fadi illar da suka yi wa Najeriya
“Mun kuma yi kokarin jaddada cewa batun ba wai Atiku Abubakar da Peter Obi kaɗai ya shafa ba. A yanzu haka, babu wanda ke tattauna batun ɗan takarar shugaban kasa a ADC.”
“Abin da ya fi ɗaukar hankalinmu a cikin watannin da suka gabata shi ne kafa ingantaccen tsari a faɗin ƙasa. Amma mun san cewa wannan matsala ce da dole mu fuskanta nan gaba.”
Matsayar jam'iyyar ADC kan zaben 2027
Bolaji Abdullahi ya ce idan lokacin zaɓen ya yi, jam’iyyar za ta yi kokarin cimma yarjejeniyar samar da dan takara ta hanyar maslaha.
“Mafi muhimmanci shi ne, idan mun kai lokacin, mu yi kokarin samar da matsaya guda. Idan ba mu samu yarjejeniya ba, to za mu buɗe ƙofa kowa ya shiga takara.”
“Ba wai Atiku da Peter Obi kaɗai ke da sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa ba, akwai wasu mutane ma da ke da wannan buri.”
- Bolaji Abdullahi
A farkon wannan wata, Peter Obi ya bayyana cewa haɗin gwiwar ADC na fuskantar tangarɗa, sakamakon rashin cimma matsaya kan batutuwan rabon kujeru da kuma karba-karba kan manyan mukamai.
Duk da cewa Obi bai yi rajista a hukumance a ADC ba tukuna, Atiku Abubakar ya riga ya karɓi katin zama mamba na jam’iyyar.
Atiku Abubakar ya ba matasa shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ba matasan Najeriya shawara.
Atiku Abubakar ya bukaci matasan da su kauce wa karaya kan yunkurin gina kasa ɗaya ta hanyar tattaunawa da jajircewa.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya shawarci matasa kada su fada cikin bakin ciki da takaici duk da kalubalen tattalin arziki da zamantakewa da ake fama da su.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

