Adeleke Ya Zama Ɗan Takaran da Zai Tsaya wa Jam'iyyar Accord a Zaɓen Gwamnan Osun

Adeleke Ya Zama Ɗan Takaran da Zai Tsaya wa Jam'iyyar Accord a Zaɓen Gwamnan Osun

  • Jam'iyyar Accord ta tantance Gwamna Ademola Adeleke a matsayin ɗan takara guda ɗaya na jam’iyyar za ta tsayar a zaɓen 2027
  • Jam’iyyar ta ce Adeleke ya cika dukkanin sharuddan da ake buƙata don tsayawa takara saboda cancanta da ƙoƙarinsa wajen ci gaban jiha
  • Adeleke, wanda ya sauya sheƙa daga PDP, ya ce sauya shekan zai ƙara ƙarfin gwamnati wajen samar da nagartaccen mulki.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Osun – Kwamiti mai tantance ‘yan takara na jam’iyyar Accord ya amince da Gwamna Ademola Adeleke domin shiga zaben fid-da-gwanin gwamnan jihar Osun.

Wannan amincewa na nufin cewa Adeleke shi kaɗai ne mutumin da zai tsaya takara a karkashin jam’iyyar a zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan

"Ka jefa kanka a matsala": PDP ta zargi Gwamna Fubara da rauni bayan komawa APC

Accord ta kammala tantance Ademola Adeleke
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke Hoto: @AAdeleke_01
Source: Facebook

The Cable ta wallafa cewa wannan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin tantancewa, Ibe Thankgod, wanda shi ne sakataren ƙasa mai kula da shirye-shirye a jam’iyyar, ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Adeleke ya samu takara a Accord

Jaridar The Nation ya bayyana cewa Gwamna Adeleke ya cika dukkanin ka’idojin da ake buƙata kafin a ba da damar tsayawa takara.

Ya ce an kammala dukkannin takardun da ake buƙata tare da hukumomi masu ruwa da tsaki bayan an tantance shi a cikin tsarin jam'iyya.

Sanarwar ta nuna cewa kwamitin ya ba da cikakkiyar amincewa ga Adeleke, tare da tabbatar da shi a matsayin ɗan takara guda ɗaya da zai nemi tikitin jam’iyyar Accord a zaben 2026.

Gwamna Adeleke ya magantu kan sauya sheka

Mai magana da yawun gwamnan Osun, Olawale Rasheed, ya tabbatar da wannan ci gaban da aka samu bayan an sauya sheka.

Kara karanta wannan

An ƙara yawan ƴan sanda a Adamawa don hana faɗan kabilanci

Ya ce an miƙa wa gwamnan takardar sahalewar tsayawa takara bayan an tabbatar da shi a matsayin shi kaɗai ne ɗan takara da zai yi tsaya a jam’iyyar Accord.

Rasheed ya ƙara da cewa Gwamna Adeleke ya tabbatar wa jam’iyyar cewa yana shirye ya jagoranci fafutukar cin zaben 2026 cikin kwanciyar hankali, domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a matakin jiha.

Ademola Adeleke ya zama ɗan takarar gwamna a Accord
Ademola Adeleke, ɗan takarar gwamna a jam'iyyar Accord Hoto: @AAdeleke_01
Source: Twitter

Adeleke ya shiga jam’iyyar Accord ne a ranar Talata, kwanaki kaɗan bayan ya yi murabus daga jam’iyyar PDP.

Ya ce sauya sheƙar da ya yi ya samo asali ne daga buƙatar ci gaba da aiwatar da nagartaccen mulki da kuma samar da romon dimokuraɗiyya ga al’umma.

A cewar Adeleke, jam’iyyar Accord ta ba shi filin da ya dace domin ci gaba da ayyukan da gwamnatinsa ta ke aiwatarwa, musamman ma wadanda suka shafi jin daɗin jama’a.

Adeleke ya sauya sheka zuwa Accord

A baya, mun wallafa cewa Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya tabbatar da cewa ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar Accord, kwanaki kaɗan bayan ficewarsa daga PDP.

A wani babban taron da ya shirya domin bayyana sabon matakinsa, Adeleke ya kuma sanar da cewa zai nemi wa’adi na biyu a matsayin gwamna a zaben 2026 a karkashin Accord.

Kara karanta wannan

'Ba APC ba ce': Gwamna Adeleke ya shiga sabuwar jam'iyya bayan ficewa daga PDP

Ya ce ya shiga jam’iyyar Accord tun ranar 6 ga Nuwamba, inda ya yanke wannan mataki bayan doguwar tattaunawa da neman shawarwari daga jagorori da masu ruwa da tsaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng