Nentawe: Shugaban APC Ya Sake Kada Hantar 'Yan Adawa kafin Zaben 2027

Nentawe: Shugaban APC Ya Sake Kada Hantar 'Yan Adawa kafin Zaben 2027

  • Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi tsokaci kan zaben shekarar 2027 da ake tunkara
  • Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa nasara na tare da jam'iyyar APC a zaben 2027 domin sun shirya sosai
  • Shugaban na APC ya kuma nuna cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na samun karbuwa a kasar nan saboda ayyukan da yake yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi hasashen cewa jam’iyyar za ta samu cikakkiyar nasara a zaben 2027.

Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa karɓuwar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke samu a faɗin kasa na kara karuwa.

Nentawe ya hango nasarar APC a zaben 2027
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Hoto: Prof Nentawe Yilwatda
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce Yilwatda ya yi wannan bayani ne a Abuja yayin da yake karɓar tawagar kungiyar Women Leaders Support Advancement, wata kungiya da ke fafutukar kara samun wakilcin mata a tsarin mulki da gwamnati.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Dalilin APC na kin karbar Gwamna Mutfwang zuwa cikinta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jawabinsa ya zo ne a dai-dai lokacin da APC ke ƙara tunkarar muhimman tarurruka guda biyu da aka shirya gudanarwa a ranar 18 da 19 ga Disamba a fadar shugaban kasa.

Me Nentawe ya ce kan zaben 2027?

Shugaban na APC ya bayyana cewa jam'iyyar ta shirya sosai don tunkarar zaben 2027.

“Jam’iyyarmu ta shirya sosai, kuma da ikon Allah, APC za ta yi nasara mai ban mamaki a 2027.”

- Farfesa Nentawe Yilwatda

Yilwatda ya jaddada cewa manufar Renewed Hope Agenda ta Shugaba Tinubu ta kara buɗe damar siyasa ga mata da matasa, yana mai cewa manufofin gwamnatin suna daidaita da bukatar kasar nan na samun shugabancin da zai dama da kowa.

"An tsara manufar Renewed Hope Agenda ta Shugaba Tinubu ne don magance damuwar mata, matasa, da dukkan ’yan Najeriya da ke neman ingantaccen shugabanci.”

- Farfesa Nentawe Yilwatda

Shugaban APC ya ba mata shawara

Yilwatda ya bukaci mata su ci gaba da mara wa shugaban kasa baya, yana bayyana su a matsayin ginshiƙin haɗin kan APC a matakin kasa.

Kara karanta wannan

Tsohon kakakin PDP na kasa ya bi sahun gwamnoni 5, ya fice daga jam'iyyar

“Ina godiya da jajircewarku, kuma ina karfafa ku da ku ci gaba da yada saƙon APC zuwa kowane yanki. Mata su ne ginshikin siyasa, kuma rawar da kuke takawa tana da matukar muhimmanci.”

- Farfesa Nentawe Yilwatda

Nentawe ya ce APC za ta yi nasara a 2027
Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda da jagororin jam'iyyar. Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

Tawagar matan ta kuma tabbatar da aniyarta ta ci gaba da tallafa wa gwamnatin Tinubu da kuma kara yawan mata a harkokin siyasa.

Hasashen Yilwatda ya zo ne a dai-dai lokacin da APC ke ci gaba da karfafa tasirinta a jihohi da gundumomi, tare da shiryawa sosai domin fafatawa a siyasar 2027.

Dalilin APC na kin karbar Gwamna Mutfwang

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban APC na jihar Plateau, Rufus Bature, ya bayyana dalilin da ya sa jam'iyyar ba ta karbi Gwamna Caleb Mutfwang ba.

Rufus Bature ya bayyana cewa gwamnan bai bi hanyoyin da suka dace ba domin shiva jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Ya bayyana cewa dole ne kafin ya shiga APC ya zo a tattauna a shi domin sanin niyyar da yake da ita kan jam'iyyar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng