ADC Ta Ba Peter Obi Zabi 2 kan Shigowa Cikinta bayan Ya Fito Ya Ragargaji Hadaka
- Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi ya fito ya soki jam'iyyar ADC kan rashin raba tsarin karba-karba
- Peter Obi ya bayyana cewa rashin raba jadawalin mukamao ya sanya tafiyar hadaka wadda ta dunkule zuwa ADC ke tafiyar hawainiya
- Sai dai, jam'iyyar ADC ta hannun mai magana da yawun bakinta na kasa ta fito ta yi wa tsohon gwamnan na jihar Anambra martani
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC mai adawa ta yi wa tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, martani kan wasu kalamai da ya yi.
Jam'iyyar ADC ta bukaci Peter Obi da ya hanzarta yanke hukunci kan ko yana son shiga jam’iyyar ko a’a.

Source: Twitter
Mai magana da yawun jam'iyyar ADC na kasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da jaridar The Punch.
Jam’iyyar ta ce kodayake Peter Obi muhimmin jigo ne a tafiyar siyasar da suke ginawa, ba za su tilasta masa shiga jam’iyyar ba.
Peter Obi ya ce hadakar ADC na tangal-tangal
Peter Obi dai ya ce hadakar ADC tana tangal-tangal ne saboda har yanzu ba ta warware batutuwan rabon mukamai da tsarin karba-karba ba.
Duk da wannan matsala, Peter Obi ya bayyana kwarin gwiwa a kan manyan shugabannin da ke jagorantar hadakar, ciki har da tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Wane martani ADC ta yi wa Peter Obi?
Bolaji Abdullahi ya ce jam’iyyar ba ta kai ga tattaunawar yankin da zai samu tikitin shugaban kasa ba.
A cewarsa, abin da ya fi muhimmanci yanzu shi ne gina jam’iyya mai karfin zama madogara ga ‘yan Najeriya.
“Ba yanzu ne lokacin yin maganar karba-karba ba. ‘Yan Najeriya na jiran mu fada musu abin da za mu yi dabam."
- Bolaji Abdullahi
Ya kara da cewa idan batun karba-karba shi ne sharadin Peter Obi na shiga jam’iyyar, to watakila sai ya jira lokacin da za su kai wannan matakin.
Duk da haka, Bolaji Abdullahi ya jaddada cewa jam’iyyar na son Peter Obi ya shiga cikin hadakar siyasar.
“A wurinmu, muna son Peter Obi ya kasance tare da mu domin gina jam’iyya da za ta sake fasalin siyasar Najeriya ta zama abar dogaro.”
- Bolaji Abdullahi
Ya ce lokaci na zuwa da za a tattauna batutuwan da Peter Obi ke dauka a matsayin masu fifiko, amma yanzu jam’iyyar na kan tsarin gina karfinta.

Source: Facebook
“Za mu karfafa masa gwiwa ya yanke hukunci. Amma muna da wasu muhimman abubuwa da muke mayar da hankali a kansu.”
- Bolaji Abdullahi
Bolaji Abdullahi ya kuma musanta cewa hadakar ADC na cikin rudani ko rashin kwanciyar hankali.
Peter Obi ya soki Shugaba Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter Obi, ya ragargaji Mai girma Bola Tinubu.
Peter Obi ya soki shugaban kasan ne kan sunayen mutanen da ya mikawa majalisar dattawa domin tantancewa su zama jakadun Najeriya.
Tsohon dan takarar shugaban kasar ya bayyana takaicinsa kan jerin sunayen, yana mai cewa akwai wasu mutanen da ba su dace ba.
Asali: Legit.ng


