Zaben 2027: Sanata Barau Ya Samu Tagomashi kan Takarar Gwamnan Kano
- Ana ganin cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin zai fito takarar gwamnan jihar Kano a zaben shekarar 2027
- Tsofaffin shugabannin kananan hukumomi sun nuna goyon bayansu ga sanatan mai wakiltar Kano ta Arewa da ya fito takarar gwamna
- Har ya zuwa yanzu dai Sanata Barau bai fito fili ya bayyana cewa zai nemi kujerar Mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf a zabe mai zuwa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsofaffin shugabannin kananan hukumomi a jihar Kano sun bayyana cikakken goyon bayansu ga mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin.
Tsofaffin shugabannin kananan hukumomin sun bayyana goyon bayansu ga Sanata Barau ne a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2027.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce tsofaffin shugabannin kananan hukimomin da suka yi aiki tsakanin 2019 zuwa 2022 ne suka nuna goyon bayanau ga Sanata.

Kara karanta wannan
Ba wasa: Matakin da Gwamna Abba zai dauka don dakile hare haren 'yan bindiga a Kano
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Barau ya samu goyon baya
Tsofaffin shugabannin sun nuna amincewar ne yayin ziyarar ban-girma da suka kai majalisar tarayya da ke Abuja.
A cewar Malam Ismail Mudashir, mai ba wa Sanata Barau shawara kan harkokin yada labarai, an gabatar da kudurin amincewa da Sanata Barau a matsayin ɗan takarar gwamna a yayin ziyarar, rahoton The Nation ya tabbatar da hakan.
Ya ce tsohon shugaban karamar hukumar Rimin Gado, Barr. Dahiru Mannir Maigari, ya gabatar da kudirin amincewa da Barau, kuma tsohon shugaban ALGON a Kano, Hon. Baffa Mohammed Takai, ya mara masa baya.
Kudurin ya samu amincewa bayan tsohon shugaban karamar hukumar Madobi, Alhaji Mohammed Yahaya, ya sanya an kada kuri’ar murya.
Taron ya samu halartar wasu ‘yan majalisar dokokin jihar Kano guda biyu, Hon. Zubairu Hamza Masu (Sumaila) da Hon. Garba Yau Gwarmai (Tsanyawa/Ghari).
Da yake jawabi a madadin tsofaffin shugabannin, Alhaji Khalid Ishak Diso na ƙaramar hukumar Gwale ya roki Sanata Barau da ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna, yana mai cewa al’ummar jihar na jiransa.
“Yaushe za ka ayyana buri? Don Allah ka amsa kiran hidimtawa al'umma."
- Alhaji Khalid Iskak Diso

Source: Facebook
Sanata Barau Jibrin ya yi godiya
A martaninsa, Sanata Barau, ya gode musu tare da bayyana su a matsayin manyan jagororin siyasa a matakin kasa.
Ya ce Kano ta yi baya ne saboda rashin kyakkyawan jagoranci, sannan ya yi alkawarin mayar da martabarta a matsayin cibiyar kasuwanci da cigaba a kasa.
Haka kuma, wasu shugabanni daga Tsanyawa da Ghari suma sun nuna masa irin wannan goyon bayan, inda Hon. Garba Yau Gwarmai ya gabatar da kuduri, wanda Hon. Aminu Yakanawa ya mara masa baya.
Wannan goyon bayan ya yi kama da wanda wasu ‘yan majalisar dokokin jihar Kano masu ci da tsofaffi, suka bayar makonnin da suka gabata.
Barau ya karbi 'yan NNPP zuwa APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu mambobin jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano sun sauya sheka zuwa APC mai adawa.
Masu sauya shekar sun ce dalilansu na ficewa daga NNPP sun hada da nasarorin shugaban ƙasa Bola Tinubu da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin wajen ciyar da kasa gaba.
Sanata Barau Jibrin, wanda ya karɓe su, ya bayyana matakin da suka ɗauka a matsayin mai matuƙar kyau da dacewa, yana mai cewa jam’iyyar NNPP ta fara yin rauni a siyasar jihar Kano.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

