Me Ya Yi Zafi: Na Kusa da Atiku Ya Fice daga Jam'iyyar ADC
- Jam'iyyar ADC reshen jihar Adamawa na ci gaba da samun kanta cikin rikice-rikicen cikin gida da suka addabe ta
- Mataimakin sakataren yada labarai na kasa na jam'iyyar, Umar Jada, ya sanar da murabus dinsa daga cikinta
- Umar Jada wanda yake na kusa da Atiku Abubakar ne, ya haska dalilin da ya sanya ya fice daga jam'iyyar ADC
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Adamawa - Rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar ADC mai adawa reshen jihar Adamawa ya kara tsanani.
Manyan magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, sun fara ficewa daga jam’iyyar saboda sabani na cikin gida.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa daya daga cikin fitattun jiga-jigan jam’iyyar a jihar, Umar Jada, wanda aka fi sani da Calculate, ya yi murabus daga mukaminsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Umar Jada ya fice daga jam'iyyar ADC
Ya yi murabus ne daga mukaminsa na mataimakin sakataren yaɗa labarai na kasa da sakataren yaɗa Labarai na yankin Arewa maso Gabas na jam’iyyar, rahoton Daily Post ya zo da zancen.
A cikin wata takardar murabus da aka sanyawa hannu ranar 1 ga Disamba, 2025, wacce aka raba wa manema labarai a Yola ranar Talata, Umar Jada ya ce ya yanke shawarar ne bisa dalilai na kashin kansa.
"Na yanke wannan mataki mai wahala domin mayar da hankali kan wasu muhimman al’amuran rayuwa."
"Ina rubuto wannan takarda ne domin sanar da murabus dina daga matsayina na mataimakin sakataren yaɗa labarai na kasa da na yankin Arewa maso Gabas na ADC, daga yau.”
- Umar Jada
Meyasa mutumin Atikun ya rabu da ADC?
Ya ce shawarar tasa ta biyo bayan dogon tunani kan nauyin da yake dauke da shi da irin alkiblar da yake son rayuwarsa ta bi a wannan lokaci.
“Murabus din ya zo ne saboda dalilai na kashin kai. Duk da cewa ba abu ba ne mai sauki, amma dole nake ganin zan iya mayar da hankali kan wasu al’amura masu bukatar kulawa ta musamman.”
- Umar Jada
Umar Jada ya gode wa jam’iyyar bisa goyon baya a lokacin da yake kan mukami, inda ya ce aiki tare da jam’iyyar ya ba shi kwarewa da kyakkyawar gogewa a fagen siyasa.

Source: Facebook
Akwai rarrabuwar kai a jam'iyyar ADC
Sai dai bincike ya nuna cewa murabus dinsa na da alaka da rikicin da ke faruwa a Abuja, inda ake zargin cewa an hana magoya bayan Atiku ciki har da shugaban jam’iyyar na jihar, Shehu Yohanna, halartar taron kwamitin NWC da aka gudanar ranar Litinin.
Rahotanni sun bayyana cewa magoya bayan tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ne suka hana bangaren Atiku damar shiga taron, lamarin da ya kara ta’azzara rikicin da ya raba jam’iyyar gida biyu.
Atiku ya gana da shugabannin ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya gana da shugabannin jam'iyyar ADC na jihohin Najeriya.

Kara karanta wannan
Magana ta fara fitowa, An Ji Dalilan da suka jawo Gwamna Adeleke ya fita daga PDP
Atiku Abubakar ya gana da shugabannin ne bisa jagorancin shugaban jam'iyyar na Kogi, Ogga Kingsley, yayin wata ziyara da suka kai masa.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce tawagar ta ziyarce shi domin taya shi murnar zama sabon dan jam’iyyar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

