Kwara 2027: An Taso Mulkin Gwamna Musulmi a Gaba, Ana Neman Sauya Shi da Kirista
- Kungiyar Kwara Inclusion Advocates (KIA) ta sake kiran a samu gwamna Kirista a Kwara domin samar da adalci
- Ta ce tsarin mulki ya daɗe yana fifita bangare ɗaya wanda ke nuna rashin daidaito inda ta yi kiran samar da adalci gaba daya
- Kungiyar ta ja kunnen ‘yan siyasa su guji siyasar raba kawuna, tana cewa zaben 2027 zai nuna ko Kwara za ta rungumi adalci ko siyasar yaudara
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ilorin, Kwara – Kungiyar Kwara Inclusion Advocates (KIA), wacce ta haɗa ‘yan jihar Kwara da ke gida da ketare, ta sake kiran a samu gwamna Kirista.
Kungiyar ta bayyana damuwa kan rashin adalci da ake yi tana mai cewa akwai gazawar adalci a shugabancin jihar shekaru da dama.

Source: Original
Kwara: An bukaci samar da gwamna Kirista
Kungiyar ta bayyana haka ne a wani taron manema labarai ta yanar gizo da ta yi tare da manyan ‘yan jarida na siyasa a Lagos, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
KIA, wacce ta ƙunshi mambobi daga bangarori daban-daban na ƙabila da addini, ciki har da ‘yan Kwara na Amurka, ta ce wannan kira ya samo asali ne daga damuwa kan rashin wakilci da illarsa ga zaman lafiya da haɗin kai.
Shugabannin taron, Fola Abiodun Adekeye da Tunji Adeyemi, sun ce dogon lokaci da ake mulki ta hannun bangare guda ya janyo tashin hankali da raunin amana a jiha.
Kungiyar ta ce:
“Kwara na daga cikin jihohin da suka fi bambance-bambance a Najeriya, amma wannan bambanci bai bayyana a tsarin shugabanci kwanan nan ba.”

Source: Twitter
Gargadin da kungiyar ta yi a Kwara
KIA ta gargadi cewa irin wannan karkatarwa ba za ta dore ba, musamman ma idan aka yi amfani da ita wajen rarrabuwa, inda ta zama tushen rashin tsaro.
Kungiyar ta kuma ambaci gargadin Iyiola Oyedepo, wanda ya ce wasu ‘yan siyasa suna amfani da addini domin kare tasirinsu, cewar Vanguard.
Ta yi kira ga masu ruwa da tsaki su guji siyasar da ke ƙarfafa banbanci, tana mai cewa ba wai suna goyon bayan wani mutum ko jam’iyya ba, illa dai suna kira ne ga daidaito da adalci.
Kungiyar ta ce:
“Wannan tattaunawa ba ta bangare ɗaya bace, ita ce muradin ‘yan Kwara da dama na samun siyasa da ke girmama bambanci da karfafa haɗin kai.
“Zaben 2027 zai nuna ko Kwara za ta ci gaba da kasancewa misalin zaman lafiya da jituwa, ko kuwa za ta fada cikin siyasar tsoro da rikice-rikice.”
A karshe, KIA ta shawarci ‘yan siyasa da su guji tsaftace wasu dokoki daga tsarin mulki yayin da zaben 2027 ke karatowa.
Rikicin PDP: Saraki ya samo mafita ga jam'iyyar
A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Kwara, Bukola Saraki, ya yi tsokaci kan rikicin da ya addabi jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya.
Bukola Saraki ya bayyana cewa ba shawara ba ce mai kyau jam'iyyar ta gudanar da babban taronta na kasa a halin da take ciki yanzu.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa sulhu shi ne kadai abin da zai warware takaddamar da ake fama da ita a jam'iyyar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

