Kano: Ganduje, 'Yan APC Sun Fitar da 'Dan Takarar Shugaban Kasa da Suke So a 2027

Kano: Ganduje, 'Yan APC Sun Fitar da 'Dan Takarar Shugaban Kasa da Suke So a 2027

  • Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci tarurruka da shugabannin APC na Kano inda suka amince da Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban kasa
  • Ganduje ya umurci shugabannin kananan hukumomi da gundumomi su koma yankunansu domin bayyana goyon baya ga Tinubu a bainar jama’a
  • An samu manyan jiga-jigan jam’iyya a taron, sai dai wasu mutum biyu daga cikin fitattun ’yan siyasa ba su halarta ba, lamarin da ake ganin ya bar baya da kura

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa jam’iyyar za ta mara baya ga Bola Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a 2027.

Wannan sanarwa ta fito ne bayan jerin tarurruka da ya yi da shugabannin jam’iyyar daga matakin ƙananan hukumomi zuwa unguwanni.

Kara karanta wannan

APC ta kammala taron kwanaki 4, an tsara yadda za a samu nasara a zaɓen 2027

Yadda aka yi taron 'yan APC a Kano
Dr Abdullahi Ganduje na magana yayin taron 'yan APC a Kano. Hoto: Abdullahi Umar Ganduje
Source: Facebook

Ganduje ya wallafa a X cewa an shirya tarurrukan ne domin ƙarfafa haɗin kai a jam’iyyar da gina dabarun da za su tabbatar da nasara a babban zaben da ke tafe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron ya samu halartar jiga-jigan siyasar Kano, yayin da wasu kuma suka yi batan-dabo duk da matsayin su a jam’iyyar APC.

'Yan APC sun amince da Tinubu a 2027

Ganduje ya ce tarurrukan da aka yi daga dukkan kananan hukumomi 44 na jihar sun tabbatar da cewa shugabannin jam’iyyar suna da muradin ci gaba da mara baya ga Tinubu.

A cewarsa:

“Manufar waɗannan tarurruka ita ce tabbatar da cikakken haɗin kai a jam’iyyarmu daga sama har ƙasa, da kuma sake jaddada goyon bayanmu ga gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.”

Ya kara da cewa tsayar da Tinubu zai taimaka wajen kauce wa rikice-rikicen cikin gida da kuma ƙarfafa jam’iyyar kafin babban zabe.

Kara karanta wannan

Ba a gama da jihohin Kebbi da Neja ba, an sace mata a jihar Borno

Ganduje ya tabbatar da cewa shugabannin jam’iyyar a matakin ƙasa da jiha sun nuna goyon bayan su ga wannan matsaya.

Kiran Ganduje ga shugabannin APC

Ganduje ya umarci shugabannin kananan hukumomi da unguwanni su tabbatar ofisoshin jam’iyya suna bude tare da ci gaba da aiki yadda ya kamata.

Tsohon shugaban ya yi kira ga wakilan jam'iyyar su koma yankunansu su bayyana goyon baya ga shugaba Tinubu a bainar jama’a.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu yayin wani taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya kuma bayyana cewa za a karfafa tsarin rajistar jam’iyya ta yanar gizo, inda kowace ƙaramar hukuma za ta samar da kwararru uku na kwamfuta da za su taimaka wajen rajistar.

Manyan APC da suka hakarci taron

Taron ya samu halartar tsohon gwamnan Kano, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, da dan majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa.

Haka kuma, ɗan takarar gwamna a 2023, Nasiru Yusuf Gawuna da abokin takararsa Murtala Sule Garo, sun halarci zaman.

Shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, shi ma na cikin mahalarta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar daga sassa daban-daban na jihar.

Kara karanta wannan

An sake neman dalibai kusan 100 an rasa bayan hari a makarantar Neja

Barau bai je taron APC gidan Ganduje ba

Vanguard ta rahoto cewa an lura da rashin halartar mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Jibrin Barau.

Haka zalika karamin ministan gidaje Yusuf Abdullahi Ata wanda ake ganin yana tare da Barau Jibrin, bai iya zuwa wajen zaman ba.

APC ta gargadi ministan gidaje, Ata

A wani labarin, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas ya yi magana kan fara tallata 'yan takarar gwamna a 2027.

Abdullahi Abbas ya yi magana ne bayan ministan gidaje, Yusuf Abdullahi Ata ya yi kira da a marawa Barau Jibrin baya a neman takarar gwamnan jihar.

APC ta ce ba za ta lamunci wadanda ba su da hurumin magana kan jam'iyya ba su rika irin maganganun da ministan ya yi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng