Sabuwar Rigima Ta Kunno Kai a ADC, An Gargadi Atiku, Peter Obi da Sauransu
- Tsugunne ba ta kare ba kan rikicin shugabanci da ake fama da shi a jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya
- Wani bangare na jam'iyyar karkashin jagorancin Nafiu Bala, ya aika da gargadi ga Atiku Abubakar, Peter Obi da sauran 'yan hadaka
- Hakazalika, bangaren ya soki hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) kan amincewa da shugabancin Sanata David Mark
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wani sabon rikici ya sake kunno kai a jam’iyyar ADC mai adawa yayin da ake shirin tunkarar zaben 2027.
Wani ɓangare na jam’iyyar da ke goyon bayan shugaban rikon kwarya, Nafiu Bala, ya gargadi fitattun ’yan adawa ciki har da Atiku Abubakar, Peter Obi, da Nasir El-Rufa’i da su guji kokarin kwace jam’iyyar.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa kwamitin amintattu (BoT) na ADC ne ya fitar da gargadin ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamitin ya kuma nuna goyon baya ga Nafiu Bala, yana mai kiran hadakar da David Mark ke jagoranta da tsari marar inganci.
An nuna yatsa ga Atiku, Obi a ADC
Yayin taron manema labarai a Abuja, sakataren BoT, Chief Rufus Ekenmi, ya yi Allah wadai da abin da ya kira kokarin wasu mutane da suka shigo jam’iyyar ta bayan fage da sunan hadaka, don haifar da rashin biyayya a cikin ADC.
“BoT ya lura da takaici cewa ana kokarin kwace jam’iyyar ta hannun Atiku Abubakar, Peter Obi, Rotimi Amaechi, David Mark, El-Rufa’i, Rauf Aregbesola, Abubakar Malami (SAN), Babachir Lawal, Emeka Ihedioha, Liyel Imoke da wasu. Hakan ya sabawa doka kuma abin Allah wadai ne.”
- Chief Rufus Ekenmi
Kwamitin ya ba Nafiu Bala umarnin kafa kwamitin ladabtarwa domin hukunta duk mamban ADC da aka samu yana hulɗa da wadannan shugabanni, yana mai cewa jam’iyyar ba za ta yarda da duk wani rashin bin doka daga mambobinta ba.
Da yake mayar da martani kan goyon bayan da aka ba shi, Nafiu Bala ya yi alkawarin bin kundin tsarin mulkin jam’iyyar tare da jagoranci mai adalci da gaskiya.
Ya kuma zargi ’yan hadaka da karya dokokin jam’iyyar ADC ta hanyar kafa hedkwata ta bogi.
“Ya kamata a fayyace cewa kundin tsarin mulkin jam’iyya ya bayyana karara cewa ’yan jam’iyya nagari ne kaɗai da suka yi rijista suka kuma bi ka’ida ke da damar amfani da ofisoshin jam’iyya da sauran hakkoki.”
- Nafiu Bala
Shugaban rikon kwaryar ya kuma soki hukumar INEC kan amincewa da David Mark a matsayin shugaban ADC, duk da cewa ba dan jam’iyyar ba ne.

Source: Facebook
Wane martani jam'iyyar ADC ta yi?
Da aka nemi jin ta bakin su, mai magana da yawun jam’iyyar ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya ce ba sa son shiga wata muhawara da bangaren Nafiu Bala a bainar jama’a.
“Ba mu son shiga irin wannan tattaunawa. A maganar gaskiya ba mu san akwai wani bangare ba, ba mu son ci gaba da tankawa kan wannan batun."
- Bolaji Abdullahi
ADC ta kori mataimakin shugaban jam'iyya
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC reshen jihar Kaduna ta dauki matakin ladabtarwa kan wasu manyan jami'anta.
Kwamitin zartarwa na ADC reshen jihar Kaduna ya kori mataimakin shugaban jam’iyyar na jihar, Ahmed Tijani Mustapha.
Jam'iyyar ADC ta kori mataimakin shugaban ne tare da wasu manyan jami'ai takwas saboda zargin aikata manyan laifuffuka.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


