Ekwueme, Makarfi da Sauran Shugabanni 17 da PDP Ta Yi Tun daga 1998 da Yadda Suka Bar Kujera

Ekwueme, Makarfi da Sauran Shugabanni 17 da PDP Ta Yi Tun daga 1998 da Yadda Suka Bar Kujera

FCT, Abuja - Jam'iyyar PDP na daga cikin manyan jam'iyyun siyasa da ake da su a tarayyar Najeriya.

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Tun bayan kafuwarta a shekarar 1998, jam'iyyar PDP ta kasance daga cikin manyan jam'iyyun da ake damawa da su a kasar nan.

Mutanen da suka taba jan ragamar jam'iyyar PDP
Kabiru Tanimu Turaki, Umar Damagum da Sanata Iyorchia Ayu Hoto: Auwal Musa Muhammad Kaska, Kabiru Tanimu Turaki
Source: Facebook

Bayanai daga shafin yanar gizo na PDP, sun nuna cewa an yi rajistar ta shekarar 1998 tare da wasu jam’iyyu domin shirin komawa mulkin dimokradiyya bayan dogon zamanin mulkin soja.

A lokacin, wadanda suka kafa jam’iyyar sun yi hasashen cewa PDP za ta zama babbar jam’iyya mafi ƙarfi a nahiyar Afrika.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutanen da suka shugabanci PDP

Shugabanni da dama sun jagoranci ragamar jam'iyyar tun bayan da aka samar da ita a lokacin mulkin soja.

Sai dai, cikin shugabannin da ta samar, kaɗan ne suka bar kujerarsu cikin mutunci, yawancin su an raba su mukaminsu ne saboda rikice-rikice da sabani.

Kara karanta wannan

Atiku: "Ba a taba jam'iyyar da ta azabtar da 'yan Najeriya kamar APC ba"

1. Dr. Alex Ekwueme

Dr. Alex Ekwueme shi ne shugaban rikon kwarya na PDP lokacin da aka kafa ta a shekara 1998, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Ya jagoranci jam’iyyar na tsawon watanni uku kafin ya sauka domin neman takarar shugaban kasa a karkashin PDP.

2. Chief Solomon Lar

Chief Soloman Lar wanda ya ke tsohon gwamnan jihar Plateau, shi ne ya zama shugaban jam’iyyar PDP na farko.

Ya bar kujerar shugabancin PDP bayan dangantaka tsakaninsa da Shugaba Olusegun Obasanjo ta yi tsami.

Daga baya Chief Solomom Lar ya zama mamba a kwamitin amintattu na kasa (BoT) na PDP a shekarar 2004.

3. Chief Barnabas Gemade

Chief Barnabas Gemade ya karɓi shugabancin jam'iyyar PDP daga hannun Chief Solomom Lar a shekarar 1999.

Ya kammala wa’adin farko na shekara biyu, amma yunkurinsa na sake tsayawa takara bai yi nasara ba, saboda rashin jituwa da Shugaba Obasanjo.

Jaridar Vanguard ta ce Chief Barnabas Gemaade ya bar shugabancin PDP a babban taronnta na kasa na shekarar 2001.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya koma ADC

4. Chief Audu Ogbeh

Chief Audu Ogbeh wanda ya fito daga jihar Benue, ya hau kujerar shugabanci a shekarar 2001.

Chief Agbu ya jagoranci jam'iyyar PDP
Tsohon shugaban PDP na kasa, marigayi Audu Ogbeh Hoto: Audu Ogbeh
Source: Twitter

Tsohon ministan na noma ya yi murabus a watan Janairun 2005 bayan alaka tayi muni tsakaninsa da Shugaba Olusegun Obasanjo.

5. Ahmadu Ali

Ahmadu Ali ya fara shugabantar PDP a matsayin rikon kwarya bayan murabus din Chief Audu Ogbeh.

Daga baya an zabe shi a matsayin shugaban jam'iyyar PDP na kasa a shekarar 2005.

Ya kammala wa’adinsa har zuwa 2008 lokacin da aka maida kujerar shugabancin jam'iyyar zuwa yankin Kudu maso Gabas.

6. Prince Vincent Ogbulafor

Prince Vincent Ogbulafro ya hau kujerar shugabancin jam'iyyar PDP a shekarar 2008. An kore shi daga shugancin PDP a shekarar 2010 bayan rasuwar Shugaba Umaru Musa Yar’adua.

Prince Vincent Ogbulafor ya rasa mukaminsa ne bayan wata magana da ya yi a 2010, kan cewa tikitin takarar shugaban kasa zai koma Arewa a 2011, wadda wannan magana ba ta yi wa gwamnatin Goodluck Jonathan dadi ba.

Kara karanta wannan

Sabuwar rigima ta kunno kai a ADC, an gargadi Atiku, Peter Obi da sauransu

7. Dr. Ezekwesilieze Nwodo

Tsohon gwamnan jiihar Enugu, Dr. Ezekwesilieze Nwodo, ya hau kujerar shugabancin PDP a shekarar 2010.

An cire shi daga mukaminsa bayan zaben fidda gwanin da ya bai wa Goodluck Jonathan damar tsayawa takara.

8. Dr. Halliru Bello Mohammed

Dr. Halliru Bello Mohammed ya maye gurbin Dr. Ezekwesilieze Nwodo a matsayin shugaban rikon kwarya a 2011 bayan taron NEC karo na 56.

Ya rike kujerar shugabancin PDP ar sai da aka nada shi ministan tsaro a watan Yuli na shekarar 2011.

9. Alhaji Kawu Baraje

Alhaji Kawu Baraje ya rike shugabancin jam’iyyar a matsayin rikon kwarya daga 2011 har zuwa 2012.

Daga baya ya zama shugaban taware a kungiyar New PDP (nPDP) saboda rikicin cikin gida da ya addabi jam'iyyar.

10. Alhaji Bamanga Tukur

Alhaji Bamangu Tukur ya zama shugaban PDP a babban taronta na kasa na shekarar 2012.

Mulkinsa ya kasance cike da rikici wanda ya jawo ficewar gwamnoni biyar na PDP zuwa APC.

Kara karanta wannan

Ran APC ya baci, ta dura kan PDP bayan saboda taimakon Trump a Najeriya

Alhaji Bamanga Tukur ya sauka a Janairu 2014 bayan ya fuskanci matsin lamba daga jiga-jigan jam’iyyar.

11. Alhaji Adamu Mu’azu

Alhaji Adamu Mu'azu ya hau kujerar shugabancin PDP a watan Janairun shekarar 2014.

Tsohon gwamnan na jihar Bauchi ya yi murabus a ranar, 20 ga watan Mayun 2015 bayan PDP ta sha kaye a zaben 2015.

An zarge shi da rashin iya jagoranci wanda ya kai ga faduwar jam’iyyar a mataki na kasa.

12. Prince Uche Secondus

Prince Uche Secondus ya rike kujerar shugabancin PDP a matsayin rikon kwarya bayan murabus din Adamu Mu’azu a 2015.

Ya ki sauka bayan wa’adinsa na wata uku ya kare, sai dai babbar kotu a Abuja ta tunbuke shi daga kujerar bayan ta yi hukuncin cewa wa'adinsa.

13. Ali Modu Sheriff

An nada Ali Modu Sheriff a matsayin shugaban rikon kwarya na PDP a watan Fabrairun 2016 domin kammala wa’adin Adamu Mu’azu.

Shi ma ya ki barin kujera, lamarin da ya kara tsananta rikicin jam'iyyar PDP, a karshe aka yi waje da shi daga majalisar NWC.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: PDP ta fatattaki Gwamna Bala da wasu gwamnoni 2 daga jam'iyyar

14. Ahmed Makarfi

A ranar 21 Mayu 2016, Ahmed Makarfi ya zama shugaban kwamitin rikon kwarya na mutane bakwai a taron jam'iyyar da aka gudanar a birnin Port Harcourt na jihar Rivers.

Sanata Ahmed Makarfi ya rike mukamin shugaban PDP
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Makarfi Hoto: Ahmed Makarfi
Source: Facebook

An nada tsohon gwamnan na jihar Kaduna ne domin gyara jam’iyyar da sake dawo da zaman lafiya.

15. Iyorchia Ayu

Sanata Iyorchia Ayu ya zama shugaban PDP ne a babban taron jam'iyyar na shekarar 2021, tashar Channels tv ta kawo labarin.

Ya karbi ragamar shugabanci ne tare da sauran mambobin kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam'iyyar da aka zaba.

Jaridar Thisday ta ce Sanata Iyorchia Ayu ya rasa kujerar shugabancin PDP a shekarar 2023 bayan kotu ta tabbatar da dakatarwar da aka yi masa.

16. Umar Damagum

Ambassada Umar Iliya Damagum ya zama mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP na kasa a shekarar 2023.

Damagum ya shugabanci jam'iyyar PDP
Umar Iliya Damagum ya kasance shugaban jam'iyyar PDP Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

Jaridar BBC News Pidgin ta kawo rahoto cewa kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na PDP ne, ya sanar da nadin Damagum a ranar Talata, 28 ga watan Maris 2023.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Halin da ake ciki bayan jibge jami'an tsaro a hedkwatar PDP

Umar Damagum ya zama shugaban PDP na kasa yayin taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC), karon na 102, a ranar Litinin, 25 ga watan Agustan 2025.

17. Kabiru Tanimu Turaki

An zabi Kabiru Tanimu a matsayin shugaban jam'iyyar PDP na kasa a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamban 2025.

Jaridar The Punch ta ce an zabe shi ne yayin babban taron jam'iyyar na kasa da aka gudanar a birnin Ibadan na jihar Oyo.

Zaben nasa ya biyo bayan umarnin da kotu ta bada na hana gudanar da taron, wanda jiga-jigan jam'iyyar da dama suka kaurace masa.

An tsige shugabannin jam'iyyar PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta tsige dukkanin shugabanninta a jihohi uku.

Jam'iyyar PDP ta tsige shugabannin ne a jihohin Imo, Abia, Enugu, Akwa Ibom da Rivers da ke Kudancin Najeriya.

An dauki wannan mataki ne a yayin babban taron zaben jam’iyyar da aka gudanar a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamban 2025.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng