Nentawe: Shugaban APC Ya Fadi Jihar da Jam'iyyar APC Za Ta Kwace a Zaben 2027
- Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya yi karbi wasu mambobin jam'iyyun adawa da suka sauya sheka zuwa APC a jihar Plateau
- Farfesa Nentawe Yilwatda ya yi jawabi kan irin karbuwar da jam'iyyar ke ci gaba da samu a jihar, inda ya ce hakan alamun nasara ne
- Shugaban na APC ya yi hasashe kan tagomashin da Shugaba Bola Tinubu da sauran 'yan takarar jam'iyyar za su samu a zaben 2027
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Plateau - Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi magana kan karfin jam'iyyar a jihar Plateau.
Farfesa Nentawe Yilwatda ya ce jam’iyyar na da cikakkiyar damar kwace mulki daga PDP a zaben gwamna na 2027 a jihar Plateau.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a ranar Asabar, a wajen taron tarbar masu sauya sheƙa daga PDP, LP, PRP, da NNPP zuwa APC a Jos, babban birnin jihar Plateau.

Kara karanta wannan
An samu rudani yayin da PDP ta zabi sabon shugaban jam'iyya na kasa a taron Ibadan
Me Nentawe ya ce kan karfin APC a Plateau?
Farfesa Nentawe Yilwatda ya ce karuwar goyon bayan da jam’iyyar ke samu ya sanya ta cikin kyakkyawan matsayi don samun nasara.
Yilwatda ya kara da cewa APC za ta lashe zaben shugaban kasa, na ‘yan majalisar dattawa, wakilai da na majalisar dokoki ta jiha a babban zabe mai zuwa.
“A yau a Plateau, akwai jam’iyya ɗaya tak, idan ba ka cikin APC, to ba ka cikin kowace jam’iyya. Ina alfahari da cewa muna da isasshen karfi, isasshen kuzari, da isasshen injin da zai ba mu damar lashe zaben gwamna."
"Muna da karfi a yankin tsakiya, Kudu da Arewa, kuma za mu yi gagarumar nasara. A 2027, Shugaba Tinubu, dan takarar gwamna na APC, sanatoci, ‘yan majalisar wakilai da na majalisar dokoki na APC za su ci zabe a Plateau.”
- Farfesa Nentawe Yilwatda
Farfesa Nentawe ya jaddada tasirin APC da karfinta, inda ya yi kira ga ‘yan sauran jam’iyyu da su shiga APC kafin lokaci ya kure musu.

Source: Twitter
Jiga-jigan APC sun je Plateau
Taron ya samu halartar shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu, gwamnonin Nasarawa da Benue, mataimakan gwamnonin wasu jihohi, da manyan jiga-jigan jam’iyyar.
Yilwatda ya karɓi tsofaffin sanatoci, ‘yan takarar gwamna, da mambobin majalisar wakilai da suka sauya sheka daga PDP, LP, PRP, NNPP da ADC.
“A madadin kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) da dukkan mambobin APC, muna maraba da ku cikin wannan babbar jam’iyya."
- Farfesa Nentawe Yilwatda
Gwamnan Taraba ya shirya komawa APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya kammala shirin sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki a Najeriya.
Gwamna Agbu Kefas ya bayyana cewa zai fita daga PDP tare da shiga APC a hukumance ranar Laraba, 19 ga Nuwamba, 2025.
Hakazalika, gwamnan ya bayyana cewa matakin da ya dauka na komawa APC ba don wani buri na kansa ba ne, sai don makomar al’ummar Taraba.
Asali: Legit.ng
