Taron Siyasa: Ƴan Takarar Gwamna, Ƴan Majalisun Tarayya Sun Sauya Sheka zuwa APC
- Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, shugaban APC na kasa, sun karɓi kusoshin 'yan siyasa da suka shiga APC
- Wadanda suka sauya shekar sun hada da Sanata Istifanus Gyang, kusoshin PDP, NNPP, LP, da 'yan takarar gwamna
- Akpabio ya ce zuwan Prof. Nentawe a matsayin Shugaban APC na kasa zai baiwa jam'iyyar nasara a babban zaben 2027
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Filato - Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, tare da shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, sun karɓi sababbin ’yan jam’iyya daga jam’iyyu daban-daban a Plateau.
Lamarin ya faru ne a babban dandalin taro na Jos Polo Field, inda dubban magoya baya suka hallara domin tarbar mutanen da suka sauya sheƙa daga PDP, LP, PRP, ADC da NNPP.

Source: Twitter
Fitattun ’yan siyasa sun sauya sheƙa
Wannan bayani ya fito ne daga wata sanarwa da mai magana da yawun Akpabio, Anietie Ekong, ya fitar a ranar Lahadi, in ji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta bayyana cewa daga cikin wadanda suka sauya sheƙar akwai Sanata Istifanus Gyang, wanda ya wakilci Plateau ta Arewa a Majalisar Dattawa.
Sauran sun hada da tsohon Darakta-Janar na yakin neman zaben PDP a 2023, Latep Dabang; dan takarar gwamna na Lp a 2023, Dr. Patrick Dakum; da tsohon dan takarar NNPP, Alfred Dabwam.
Sauran sun hada da Hon. Fom Dalyop, dan majalisa mai wakiltar Riyom/Barkin Ladi; Hon. Ajang Alfred Ilya, na Jos ta Kudu/Jos ta Gabas; da Hon. Daniel Asama Ago, na Bassa/Jos ta Arewa, tare da sauran masu sauya sheƙa da dama.
Akpabio: “Plateau gaba ɗaya APC ce daga yau”
Akpabio, wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a wajen taron, ya ce fitowar Prof. Nentawe a matsayin Shugaban APC ta kasa ya kawo sabuwar nasara ga jam’iyyar a Plateau.
Ya ce:
“Tunanina da idona sun tabbatar min cewa daga yau Plateau ta koma ta APC gaba ɗaya. Zuwa 2027, Plateau za ta ba APC nasara.”
Ya kara da cewa jam’iyyar ta samu manyan “kusoshi na siyasa,” ciki har da ’yan takarar gwamna da dama, ’yan majalisar tarayya na baya da na yanzu, da kuma jagororin PDP da LP da suka sauya sheƙa.

Source: Twitter
“Tinubu ya zabi jarumi mai gaskiya” — Akpabio
Akpabio ya yaba wa Shugaba Tinubu saboda nada Farfesa Nentawe, yana mai cewa shugabancin Nentawe ya fara nuna tasiri kafin ma a shiga babban zabe.
Ya ce:
“Shugaban kasa ya samo mutum mai jarumta da nagarta. Nentawe ya jawo nasarar APC a Plateau kafin ma a kai ga zabe."
Ya kuma kara da cewa gwamnatin Tinubu ta dauki dukkan matakai na ganin an magance matsalolin tsaro a garuruwan jihar Plateau.
Gwamnan Filato zai koma APC?
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Jagororin APC a Filato sun ce ba za su amince da duk wani yunkuri daga Gwamna Caleb Mutfwang na PDP a kan sauya sheka ba.
Wannan matsaya na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da rade-radin sauya shekar wasu gwamnoni daga PDP zuwa APC.
A wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a Crest Hotel, Jos, shugabannin jam’iyyar karkashin sun ce gwamnan bai da gurbi a cikinsu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

