Ana Wata ga Wata: An Tsige Dukkanin Shugabannin PDP a Enugu da Wasu Jihohi 4

Ana Wata ga Wata: An Tsige Dukkanin Shugabannin PDP a Enugu da Wasu Jihohi 4

  • Jam’iyyar PDP ta sanar da tsige dukkan shugabanninta a jihohin Imo, Abia, Enugu, Akwa Ibom da kuma Rivers
  • Gwamna Seyi Makinde ya tabbatar da matakin ne a babban taron zaben jam’iyya da ake gudanarwa a Ibadan
  • PDP ta ce an dauki matakin ne domin karfafa tsari a cikin gida, magance rarrabuwar kai da tabbatar da daidaito

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ibadan - Jam’iyyar PDP ta tsige dukkan shugabanninta a jihohin Imo, Abia, Enugu, Akwa Ibom da Rivers.

An aiwatar da wannan mataki ne a yayin babban taron zaben jam’iyyar da ake gudanarwa a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, a ranar Asabar.

PDP ta tsige dukkanin shugabanninta a jihohi 5
Hoton taron jam'iyyar PDP da ke gudana a Ibadan, babban birnin jihar Oyo. Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

PDP ta tsige shugabanninta a jihohi 5

Gwamnan jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde, ne ya tabbatar da tsige shugabannin, kuma shi ne ya gabatar da kudirin yin hakan, in ji rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

An samu rudani yayin da PDP ta zabi sabon shugaban jam'iyya na kasa a taron Ibadan

Gwamna Makinde ya bukaci taron ya amince da sababbin shugabannin jam’iyyar a matakan da aka rigaya aka gudanar da zabuka a cikinsu.

Kudirin ya samu goyon baya daga Daniel Obiechina Okechukwu, mai binciken jam'iyyar na kasa kuma memba a kwamitin NWC na PDP.

Makinde ya bayyana cewa yanayin siyasa da ke gudana a jihohin Imo, Abia, Enugu, Akwa Ibom da Rivers ya nuna cewa babu makawa sai an sake gina jam’iyyar daga tushe.

“An rushe shugabannin jam’iyya” — Makinde

Ya ce ko da yake bai yi bayani dalla-dalla ba, matsayar ta PDP ta samo asali ne daga bukatar karfafa jituwa da sake inganta daidaito a cikin jam’iyya yayin da ake gyara tsarin siyasa a fadin Najeriya.

Makinde ya bayyana cewa:

“Dangane da jihohin Imo, Abia, Enugu, Akwa Ibom da Rivers, wannan taron ya amince da rushe dukkan tsarin shugabanci na jam’iyya tun daga matakin gunduma, karamar hukuma har zuwa matakin jiha.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: PDP ta fatattaki Wike, tsohon gwamna da wasu da ke kawo mata cikas

“Wannan taron ya amince da wallafa wannan matsaya domin ta zama sanarwar hukuma ga jama’a.”

Ya bayyana cewa PDP ta gudanar da tarukan zabenta a fadin kasar nan tsakanin shekarun 2024 zuwa 2025 domin zaben shugabanni a matakin gunduma, karamar hukuma, jiha da kuma matakin yankuna na siyasa da har ma na kasa.

Gwamna Seyi Makinde ya ce tsige shugabannin PDP a jihohi 5 ya zama dole don daidaita al'amuran jam'iyya.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya halarci wani muhimmin taro a Ibadan. Hoto: @seyiamakinde
Source: Facebook

PDP ta ce an yi zabuka bisa doka

Makinde ya jaddada cewa an gudanar da wadannan zabuka ne bisa tsarin Dokar Zabe ta 2022, kundin tsarin mulkin PDP da kuma ka’idodin jam’iyya.

Ya ce NEC da NWC sun amince da dukkan sakamakon zabukan da aka gudanar da kuma sababbin shugabannin da aka zaba.

Rushewar na nufin cewa za a kafa kwamitocin rikon kwarya ko tsarin wucin-gadi a jihohin nan domin gudanar da al’amuran jam’iyya har sai an shirya sababbin zabuka.

PDP ta zabi sabon shugaban jam'iyya na kasa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon minista, Kabiru Turaki ya lashe kujerar shugaban PDP na ƙasa bayan samun kuri’u 1,516 a taron Ibadan.

Kara karanta wannan

Ana cikin taron PDP na kasa a Ibadan, tsohon gwamna Abia ya fice daga jam'iyyar

Sabon shugaban ya yi alƙawarin dawo da mulkin jama’a cikin jam’iyyar, yana mai cewa “ba za a sake zalunci ko raini ba”

Sanatoci, gwamnoni da daruruwan jakadu daga jihohi 17 sun halarta, inda aka tabbatar da wasu sababbin shugabanni biyu a taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com