An Samu Rudani yayin da PDP Ta Zabi Sabon Shugaban Jam'iyya na Kasa a Taron Ibadan

An Samu Rudani yayin da PDP Ta Zabi Sabon Shugaban Jam'iyya na Kasa a Taron Ibadan

  • Babban taron jam'iyyar PDP na kasa ya kankama kamar yadda aka tsara a Ibadan, babban birnin jihar Oyo yau Asabar, 15 ga Nuwamba, 2025
  • Wasu rahotanni sun nuna cewa an AbinAmbasada Umar Damagum ya zama cikakken shugaban jam'iyyar na kasa
  • Sai dai daga baya an tabbatar da cewa wannan labari ba gaskiya ba ne domin Kabiru Tanimu Turaki aka zaba a wurin taron

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ibadan, jihar Oyo - Babbar jam'iyyar adawa ta kasa watau PDP ta fara daukar matakan da take ganin za su kawo karshen rigingimun cikin gida da take fama da su.

An fara yada labarin cewa wakilan jam'iyyar daga jihohi daban-daban a Najeriya sun zabi Ambasada Umar Damagum a matsayin cikakken shugaban PDP na kasa.

Shugabannin PDP.
Hoton Gwamna Ahmadu Fintiri, Bala Mohammed, Umar Damagum da wasu jiga-jigai a babban taron PDP a Ibadan Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

Ana zargin PDP ta zabi Damagum

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: An tsige dukkanin shugabannin PDP a Enugu da wasu jihohi 4

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa deleget sun zabi Umar Damagum ne a wurin gangamin PDP na kasa wanda ke gudana a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Wannan mataki ya biyo bayan kudirin da Shugaban PDP na jihar Edo, wanda shi ne shugaban kungiyar ciyamomin PDP na jihohi, Hon. Tony Abineri, ya gabatar a taron.

Ya gabatar da kudirin ne a madadin deleget 3,000 da suka halarci taron PDP na 2025 da ake gudanarwa a filin wasa na Lekan Salami Stadium, Adamasingba, Ibadan.

Kudirin, wanda Edward Marshal ya mara wa baya, ya dogara ne ga sashe na 32 na Kundin Tsarin Mulki na PDP da aka yi wa gyara.

Sai dai daga bisani PDP ta tabbatar da cewa wannan labari ba gaskiya ba ne, inda ta sanar da Kabiru Tanimu Turaki a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban jam'iyya.

Tsohon Sanatan Anambra ta Tsakiya, Ben Obi, ya bayyana cewa Turaki ya samu kuri’u 1,516 a yayin taron da aka yi a filin Lekan Salami, Ibadan, cewar Channels TV.

Ya ce Sanata Yakubu Danmarke ya samu kuri’u 275, yayin da kuri’u 43 suka lalace, a cewarsa, jimillar kuri’un da aka kada su 1,834 ne, amma Turaki ya yi nasara da tazara mai yawa.

Kara karanta wannan

PDP na dab da rasa Taraba, gwamna ya bayyana ranar da zai sauya sheka zuwa APC

PDP ta fuskanci matsaloli

Sai dai duk da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke na dakatar da taron, PDP ta fito ta bayyana cewa babu abin da zai hana ta gudanar da wannan taro a Ibadan.

A taron, wanda aka fara yau Asabar, PDP ta dauki matakai da dama domin warware rikicin da ya addabe ta, ciki har da zaben Turaki, tsohon ministan ayyuka na musamman a matsayin shugabanta na kasa.

Shugaban PDP, Kabiru Tanimu Turaki.
Hoton shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Kabiru Tanimu Turaki Hoto: PDP Nigeria
Source: Facebook

PDP ta kori Wike da wasu jiga-jigai

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta dauki matakin korar wasu daga cikin manyan jiga-jiganta, wadanda suke kawo hargitsi da rabuwar kai a tsakanin mambobinta.

Daga cikin wadanda jam'iyyar PDP ta tabbatar da korarsu akwai ministan Abuja, Nyesom Wike, da tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose.

Babbar jam'iyyara adawa ta Najeriya ta yanke shawarar sallamar wadannan jiga-jigai ne a wurin gangaminta na kasa wanda ke gudana a Ibadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262