Ta Faru Ta Kare: PDP Ta Fatattaki Wike, Tsohon Gwamna da Wasu da Ke Kawo Mata Cikas

Ta Faru Ta Kare: PDP Ta Fatattaki Wike, Tsohon Gwamna da Wasu da Ke Kawo Mata Cikas

  • Jam'iyyar PDP mai adawa ta yi ta maza a taronta da aka gudanar a jihar Oyo inda ta sallami wasu daga cikin jiga-jiganta
  • Daga cikin wadanda jam'iyyar ta tabbatar da korarsu akwai ministan Abuja, Nyesom Wike, Ayodele Fayose da ke kawo mata cikas
  • Tsagin Wike ya yi ƙoƙarin dakatar da taron ta hanyar kotu, amma PDP ta samu hukuncin kotun Oyo da ya ba ta damar gudanar da taron

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ibadan, Oyo - Jam’iyyar PDP ta kori Ministan Abuja, Nyesom Wike, tare da wasu daga cikin jiga-jiganta saboda laifuffuka daban-daban.

Daga cikinsi akwai tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose da Samuel Anyanwu wanda shi ne tsohon sakataren jam’iyyar.

PDP ta sallami Wike, Fayose daga jam'iyyar
Ministan Abuja, Nyesom Wike na daga cikin da ake zargin na kawo cikas a PDP. Hoto: Lere Olayinka.
Source: Twitter

Daily Trust ta ce an dauki matakin ne yayin babban taron da ake gudanarwa a birnin Ibadan da ke Jihar Oyo.

Kara karanta wannan

An nemi gwamnonin jam'iyyar PDP 3 an rasa a babban taron da ake yi a Ibadan

Chif Olabode George ne ya gabatar da kudirin korar, kuma shugaban PDP na Bauchi, Hon. Samaila Burga, ya mara masa baya.

Yadda bangaren Wike ya so lalata taron

A gefe guda, tsagin da ke goyon bayan Wike ya yi ƙoƙarin dakatar da taron ta hanyar kotu, sai dai PDP ta samu hukuncin babbar kotun Oyo da ya tabbatar da sahihancin gudanar da taron.

Kafin taron, shugaban kwamitin amintattu na tsagin Wike, Mao Ohuabunwa, ya gargadi jama’a cewa duk wanda ya tafi Ibadan don taron ba zai amincewa da shi ba.

Ohuabunwa ya ce Anyanwu ya riga ya sanar da dage taron, kuma sun amince su bi dukkan hukuncin kotu da ya shafi taron Ibadan.

Ya kara da cewa:

“Ibadan wurin jama’a ne, mutane su je idan suna son yawon shakatawa, amma ba taron PDP ba."
PDP ta kori Wike, Fayose a jam'iyyar
Shugaban jam'iyyar PDP a Najeriya, Umar Damagum. Hoto: Peoples Democratic Party, PDP.
Source: Twitter

Tsagin Wike sun gargadi masu halartar taron

Shugaban rikon kwarya na tsagin, Abdulrahman Muhammad, ya kuma yi kira ga daliget su guji halartar taron, yana mai cewa suna ci gaba da karfafa jam’iyyar a jihohi 36 da Abuja don gina PDP mai karfi da hadin kai.

Kara karanta wannan

Sule Lamido ya janye karar da ya kai PDP kotu? An ji magana daga bakinsa

A nasa bangaren, Wike ya gode wa magoya bayansa kan yadda suke tsayawa jam’iyyar PDP a yankunansu.

Ya ce shi da tawagarsa za su ci gaba da bin doka, kuma ba zai taba cin amanar wadanda suka tsaya da kundin tsarin mulki na PDP ba, Punch ta tabbatar.

Ya ce:

“Zan ci gaba da goyon bayan ku. Ba zan yi muku rugu-rugu ko cin amana ba.

Gwamnoni 3 ba su halarci taron PDP ba

A baya, an ji cewa yayin da ake ci gaba da babban taron jam'iyyar PDP da ake gudanarwa a birnin Ibadan a jihar Oyo da ke Kudu maso Yamma a Najeriya.

Ana gudanar da taron ne duk da umarnin kotu na hana ta inda manyan jam'iyyar da gwamnoni suka halarta sai dai ba a na Taraba, Rivers da kuma Osun ba.

Sai dai akwai wasu gwamnonin jam'iyyar har guda uku da ba su samu zuwa ba yayin da wasu ake hasashen za su bar PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.