Gwamna Caleb Mutfwang Ya Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar YPP? Gaskiya Ta Fito
- Gwamnatin jihar Filato ta musanta labarin da ake yadawa cewa Gwamna Caleb Mutfwang ya sauya sheka daga PDP zuwa YPP
- Mai magana da yawun gwamnan, Gyang Bere ya bayyana jita-jitar da ake yadawa a matsayin karya mara tushe balle makama
- Ya ce Gwamna Mutfwang ya maida hankali wajen sauke nauyin da al'umma suka dora masa da cika alkawurran da ya dauka
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jos, Pleateu State - Wasu rahotanni da ake ta yadawa a kafafen sada zumunta sun nuna cewa gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya sauya sheka daga PDP zuwa YPP.
Rahotannin sun yi ikirarin cewa Gwamna Mutfwang ya bar PDP, sannan ya kaucewa komawa APC mai mulki, inda ya zabi shiga jam'iyyar YPP ta adawa.

Source: Facebook
Dagaske Gwamna Mutfwang ya bar PDP?
Sai dai gwamnatin jihar Filato ta karyata wannan labarin, tana mai bayyana cewa Gwamna Mutfwang na nan daram PDP, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Jumma’a a Jos, daraktan yada labarai na gwamnan, Gyang Bere, ya bayyana wannan ikirari a matsayin tsagwaron karya.
Ya zargi wasu bara gurbin yan siyasa da kirkiro wannan labari na karya domin yaudara da kuma dauke hankulan jama'ar jihar Filato.
Gyang Bere ya bayyana labarin a matsayin ƙagaggen rubutu mara ma’ana wanda ma bai cancanci a bi ta kansa ba, sai dai ya ce dole ne su fitar da bayani don kada a yaudari jama’a, musamman masu bibiyar kafafen sada zumunta.
Gwamnatin Filato ta yi bayani
A rahoton Punch, kakakin gwamnan ya ce:
“Domin kauce wa ruɗani, Gwamna Mutfwang bai koma jam’iyyar YPP ba. Idan har akwai wani sauyi da ya yi a siyasarsa, zai fito ya sanar da al’ummar Jihar Filato ta hanyoyin da suka dace.
Mista Bere ya kara da cewa Gwamna Mutfwang yana nan kan bakarsa ta cika alkawuran da ya dauka, tare da mai da hankali kan aiwatar da muhimman ayyuka da shirye-shiryen ci gaban jama’a a fadin jihar.
Sakon gwamnatin Filato ga jama'a
Gwamnatin ta bukaci jama’a, magoya baya da masu ruwa da tsaki da su yi watsi da wannan jita-jita gaba ɗaya, tare da kasancewa masu faɗakarwa da lura da ƙarerayin siyasa da ke yawo.
“A karkashin shugabancin Gwamna Mutfwang mai hangen nesa, jihar Filato ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali, ci gaba, da karfafa gwiwa fiye da da," in ji Bere.

Source: Facebook
A ƙarshe, gwamnati ta yi kira ga jama’a da su kasance masu haɗin kai wajen ci gaban Jihar Filato, duk da ƙoƙarin wasu na tada jijiyoyin wuya ta hanyar yaɗa bayanan ƙarya.
Gwamnan Filato na shirin komawa APC
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, na iya barin PDP a kowane lokaci daga yanzu domin komawa jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan.
Wasu majiyoyi da ke kusa da gwamnan sun yi ikirarin cewa Mutfwang ya yanke wannan shawara, kuma zai iya sanar da barin jam'iyyar PDP a kowane lokaci.
Wasu na kusa da Mutfwang sun ce shugaban kasa ne da kansa ya gayyace shi domin su hada kai wajen bunkasa jihar Filato da kasa baki daya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


