Manyan PPD 2 Sun Ja Daga a kan Babban Taron Jam'iyya na Kasa
- Tsohon Shugaban majalisar dattawa, Dr. Bukola Saraki ya bukaci a dakatar da babban taron PDP da za a yi gobe a Ibadan
- Ya bayyana haka ne saboda akwai dambarwa a kan lamarin, wanda a cewarsa yanzu batun yana gaban kotun kasar nan
- Dr. Bukola Saraki ya yi kiran ne bayan wata tattauna wa da ya yi da kwamitin sulhu da kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP ya kafa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, ya yi kira da a dakatar da taron kasa na jam’iyyar PDP da aka shirya gudanarwa gobe a birnin Ibadan, Jihar Oyo.
Saraki ya bayyana cewa matsalolin siyasa da na doka da ke tattare da taron za su kara rura wutar rikicin da ke addabar jam’iyyar.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce Saraki ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya rattaba wa hannu bayan ganawarsa da kwamitin sulhu da kwamitin amintattun PDP ya kafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Saraki na son a dakatar da taron PDP
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Bukola Saraki ya bayyana takaici a kan yadda kokarin wasu daga cikin 'yan jam'iyyar na ganin an samu daidaito ya tashi a wofi.
Ya kara da cewa ba a samun abin da ake so ta hanyar kotu a siyasa, inda ya ce zaman tattaunawa tsakanin bangarori daban-daban shi ne hanyar samun zaman lafiya mai dorewa.

Source: Facebook
A cewarsa:
“Dole mu zauna a teburin sulhu mu warware sabani. Yin gaba zuwa kotu zai kara dagula al’amura.”
Saraki ya ce bayar da shawarar dakatar da taron saboda sauke nauyin da ya rataya a wuyansa na kare muradun mutanensa da tabbatar da daidaito a dimokradiyya.
Ya shawarci PDP ta kafa kwamitin rikon kwarya cikin kwanaki biyu domin sanyaya rayukan jama’a da daidaita jam’iyyar.
Wabara ya dage kan taron PDP
Sai dai shugaban kwamitin amintattun PDP, Sanata Adolphus Wabara, ya ce babu wani abu da zai hana gudanar da taron jam'iyya na kasa.
Wabara ya ce gwamnoni, 'yan kwamitin gudanarwa da na amintattu sun amince da gudanar da taron, sai dai idan kotu ta bayar da umarnin dakatarwa.
A cewarsa, yawancin rikicin PDP na tasowa ne daga son zuciya da burin jagoranci da wasu ke yi har zuwa shekarar 2031.
Da ya ke magana da Legit Yusuf Dingyadi, tsohon mai magana da yawun Umar Damagun ya bayyana takaici a kan yadda wasu ke son kawo tangarda ga taron PDP.
Ya ce:
"Karar da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya kai kotu don hana taro da hukuncin da kotun ta yi a Abuja, ni ina ganin wani yunkuri ne ake so a bi, a ce ba za a yi wannan taro ba domin biyan wani bukata."

Kara karanta wannan
Anioma: Shugaba Tinubu, Akpabio da sanatoci 97 sun goyi bayan kirkiro jiha 1 a Najeriya
"Wannan ya saba wa ainihin hukuncin da kotun koli ta yi na cewa kotuna su daina shisshigi a lamarin da ya shafi hukuncin cikin gida na jam'iyya."
Yusuf Dingyadi ya bayyana cewa babu abin da zai babban taro, ganin cewa wa'adin shugabannin PDP na yanzu zai kare a watan Disamba.
PDP ta mutu, cewar Fayose
A baya, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bayyana damuwarsa kan yadda babbar jam’iyyar adawa, PDP, ta shiga halin koma-baya da rikici mai tsanani.
Fayose ya ce ficewar manyan 'ya'yan jam’iyyar da rashin daidaito a shugabanci sun tabbatar da cewa PDP ta rasa karfi da tasirinta a siyasar Najeriya kamar yadda ta ke da shi a baya.
Tsohon gwamnan ya kuma ja hankalin ‘yan jam’iyya kan yadda matsalolin da ake fama da su ke kokarin kai jam'iyyar kasa domin daukar matakain farfado da ita kafin ta mutu murus.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

