Da Gaske Tinubu na ba 'Yan Adawa Kudi Su Sauya Sheka? Dan APC Ya Fito da Bayanai

Da Gaske Tinubu na ba 'Yan Adawa Kudi Su Sauya Sheka? Dan APC Ya Fito da Bayanai

  • Jagora a jam'iyyar APC mai mulki, AA Zaura ya yi magana kan zargin cewa ana bai wa mutane kuɗi domin su sauya sheka
  • Ya ce sauya sheƙar da ake yi daga jam’iyyu zuwa APC ya samo asali ne daga amincewa da shugabancin Bola Tinubu
  • AA Zaura ya yi magana ne yayin da aka yawaita cewa jam'iyya mai mulki na sayen 'yan adawa da makudan kudi zuwa APC

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Jagoran jam’iyyar APC kuma ɗan takarar Sanata a Kano a 2023, Alhaji Abdussalam Abdulkarim Zaura, da aka fi sani da AA Zaura, ya yi magana kan sauya sheka da ake yawan yi.

AA Zaura ya yi magana ne kan zarge-zargen da jam’iyyun ADC da PDP ke yi cewa ana bai wa mutane kuɗi domin su sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

An bukaci Tinubu ya tilasta Wike ya ba Yerima hakuri bayan zaginsa da ya yi

AA Zaura, Bola Tinubu
AA Zaura tare da shugaba Bola Tinubu. Hoto: Ishaka Maidudu
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa ya yi maganar neta bakin mai taimaka masa wajen yaɗa labarai, Dahiru Maihuddadu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

AA Zaura ya bayyana zargin a matsayin ƙoƙarin ɓata suna da rage karɓuwar da jam’iyyar ke samu a ƙasar nan tun bayan abin da ya kira karuwar martabar ta a ƙarƙashin Bola Ahmed Tinubu.

Zaura ya karyata zargin sayen 'yan adawa

AA Zaura ya bayyana batun cewa ana biyan mutane kuɗi don su shiga APC a matsayin abin da ba gaskiya ba.

A cewarsa:

“Zargin cewa ana bai wa mutane kuɗi domin su koma APC ba shi da tushe, kuma ba gaskiya ba ne.
"Abin da muke gani shi ne sauyin siyasa na gaskiya wanda ya samo asali daga cigaba da sauye-sauyen da gwamnatin shugaba Tinubu ta fara aiwatarwa.”

Ya kara da cewa gwamnati mai ci ta kafa ginshiƙai da suka sa jama’a da dama sun sake samun kwarin gwiwa ga tafiyar APC.

Kara karanta wannan

'El Rufa'i zai zama shugaban kasa,' Dan ADC ya yi mafarki kan zaben 2027

Shugabam APC, Farfesa Yilwatda
Shugaban APC da wasu 'yan jam'iyya a ofishinsa a Abuja. Hoto: All Progressive Congress
Source: Twitter

Zaura ya ce ana komawa APC ne musamman ganin an fara shirin farfaɗo da tattalin arziki da kuma sauye-sauyen da ake yi a mahimman bangarori.

'Tinubu ne ke jawo 'yan adawa' – Zaura

Zaura ya ce shirye-shiryen farfaɗo da tattalin arziki, gina sabbin abubuwan more rayuwa da tsarin damawa da kowa da kowa a harkokin gwamnati sun sa APC ta ƙara samun karɓuwa a ƙasar nan.

Ya ce:

“Shugaba Tinubu ya nuna bajinta wajen dawo da Najeriya kan turbar da ta dace. Wannan sabon kwarin gwiwar da jama’a ke samu shi ne ya jawo sababbin mambobi, ba kuɗi ko wani salo ba kamar yadda ake zargi.”

Ya ce jam’iyyar na aiwatar da manufofi da ke janyo ’yan siyasa masu tunani na ci gaban kasa, suna ganin APC ce hanyar da ta fi dacewa da cigaban Najeriya.

AA Zaura ya yi kira ga jam’iyyun adawa su koma siyasar da ta shafi bukatun jama’a maimakon yaɗa rade-radi da jita-jita marasa tushe.

Kara karanta wannan

Gwamna Caleb ya kammala shirin komawa APC, an ji abin da ya tattauna da Tinubu

Tinubu ya yi kira ga 'yan jarida

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga 'yan jarida a Najeriya game da masa adalci.

Shugaban ya bukaci masu sukar gwamnatinsa su rika magana cikin adalci da fitar da bayanai na gaskiya a kodayaushe.

Bola Tinubu ya bayyana haka ne yayin wani taron 'yan jarida karo na 21 da aka gudanar a birnin tarayya, Abuja.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng