Rikicin PDP: Saraki Ya Samo Mafita ga Babbar Jam'iyyar Adawa
- Tsohon gwamnan jihar Kwara, Bukola Saraki, ya yi tsokaci kan rikicin da ya addabi jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya
- Bukola Saraki ya bayyana cewa ba shawara ba ce mai kyau jam'iyyar ta gudanar da babban taronta na kasa a halin da take ciki yanzu
- Tsohon gwamnan ya bayyana cewa sulhu shi ne kadai abin da zai warware takaddamar da ake fama da ita a jam'iyyar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr. Bukola Saraki, ya yi tsokaci kan rikicin da ya addabi jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya.
Saraki ya bada shawarar a kafa kwamitin rikon kwarya domin ya karɓi ragamar jagorancin PDP, maimakon ci gaba da shirya babban taron kasa da aka tsara gudanarwa a Ibadan.

Source: Twitter
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan na jihar Kwara ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X bayan ya karbi bakuncin tawagar sulhu da kwamitin amintattu (BoT) na PDP ya kafa.

Kara karanta wannan
Bayan komawa APC, Gwamna Diri ya magantu kan tilastawa mataimaminsa dawowa jam'iyyar
PDP ta dare gida biyu
Jam’iyyar PDP dai ta rabu gida biyu tsakanin magoya bayan ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, da ke so a dakatar da taron, da magoya bayan Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, da ke son gudanar da shi kamar yadda aka tsara.
Dukkan bangarorin sun samu umarnin kotu da ke goyon bayan matsayinsu, abin da ya jefa ‘ya’yan jam’iyyar cikin rudani da rashin fahimta.
Saraki ya gana da tawagar BoT
Saraki, wanda ke jagorantar kwamitin sulhu na PDP, ya ce ci gaba da shirya taron duk da rikice-rikicen kotu, zai iya jefa jam’iyyar cikin mummunan hali kuma ya bar ‘yan takarar jam’iyyar cikin ruɗani da rashin tabbas.
“A ranar 12 ga Nuwamba 2025, na karɓi tawagar kwamitin sulhu na BoT karkashin jagorancin Ambasada Hassan Adamu (Wakilin Adamawa)."
"Sun nemi jin ra’ayina kan hanyoyin dawo da zaman lafiya a jam’iyyarmu. Mun tattauna sosai kan al’amuran da suka shafi babban taron kasa da aka tsara a Ibadan."
- Bukola Saraki
Wace shawara Saraki ya bada?
Ya ce ya gaya musu cewa babu wata matsalar siyasa da za a iya shawo kanta ta hanyar kotu, domin a cewarsa, batutuwan siyasa ana warware su ne da tattaunawa da fahimtar juna, ba da rikicin doka ba.
“A halin yanzu akwai hukuncin kotu masu cin karo da juna kan sahihancin taron da aka tsara. Don haka babu tabbacin cewa gudanar da shi ko sakamakonsa zai tabbata.”
"Shawarar da na ba tawagar BoT ita ce mafita daya tilo da muke da ita, ita ce jam'iyyar ta kafa kwamitin rikon kwarya da zai jagoranci al'amuranta a halin yanzu. Kuma dole a yi hakan cikin kwanaki biyu masu zuwa."
“Wannan ce hanya mafi dacewa don dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a PDP. Haka kuma, shi ne zai tabbatar da cewa ‘ya’yan jam’iyyar masu niyyar tsayawa takara suna da cikakken tabbaci da kwarin gwiwa.”
- Bukola Saraki

Source: Twitter
Saraki ya ja kunnen PDP
Saraki ya gargadi jam’iyyar cewa ci gaba da shirya taron na Ibadan kamar yadda aka tsara zai kara ta’azzara rikicin da ake ciki, yana mai cewa babu ɗan siyasa mai hangen nesa da zai so tsayawa takara a PDP ba tare da sanin ko takararsa za ta kasance sahihiya ba.
“A halin yanzu, babu ɗan siyasa mai hankali da zai nemi takara a dandalin PDP ba tare da sanin sahihancin zabensa ba. Don haka, ci gaba da shirya taron Ibadan zai kara hura wutar rikicin da ake ciki."
- Bukola Saraki
PDP ta sha alwashi kan taronta
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta sha alwashi kan babban taronta na kasa.
PDP ta bayyana cewa za ta ci gaba da shirye-shiryen gudanar da babban taronta na kasa duk da umarnin da kotu ta bada na dakatar da shi.

Kara karanta wannan
'PDP ta mutu,' Fayose ya fadi sunan gwamnan PDP da zai koma jam'iyyar APC a Arewa
Jam'iyyar ta bayyana cewa ba za ta bari 'hukuncin da aka sayo' ya kawo mata cikas a cikin harkokinta na cikin gida ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

