Anambra: An Jero Dalilan da Ake Ganin Sun Jawo Mummunan Faɗuwar APC, PDP da LP
- Masana sun bayyana dalilan da suka jawo jam’iyyun adawa suka sha kaye a zaben gwamnan Anambra 2025
- Rahotanni sun nuna PDP da LP sun shiga rikicin cikin gida, yayin da APGA ta ci gaba da nuna karfi
- Masu lura sun ce rarrabuwar kawuna, karancin kudi, rashin tsaro da ƙarancin fitowar jama’a sun hana yan adawa nasara
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Awka, Anambra - Hukumar INEC ta ayyana Gwamna Charles Soludo a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan da aka yi a Anambra.
Masana harkar siyasa sun bayyana dalilai masu yawa da suka jawo jam’iyyun adawa suka fadi a zaben gwamnan Anambra na shekarar 2025.

Source: Twitter
Anambra: Dalilan da suka jawo faduwar yan adawa
A sakamakon hukumar INEC, Gwamna Charles Soludo na APGA ya samu kuri’u 422,664, yayin da abokin hamayyarsa Nicholas Ukachukwu na APC ya samu 99,445, cewar Premiumi Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dan takarar LP, George Moghalu, ya samu kuri’u 10,576, sai John Nwosu na ADC da ya tashi da kuri’u 8,208 kacal.
An bayyana cewa daga cikin masu rajista miliyan 2.78, mutum 598,229 ne kawai suka fito kada kuri’a, wanda ke nuni da 21.4%.
Legit Hausa ta yi duba game da dalilai da suka jawo faduwar jam'iyyun adawa a zaben Anambra.
1. Babban tazarar da ya raunata jam'iyyun adawa
Gwamna mai ci, Charles Soludo na jam’iyyar APGA ya samu kuri’u 422,664 wanda hakan ya tabbatar da nasararsa.
Abokin hamayyarsa mafi kusa, Nicholas Ukachukwu na APC, ya samu kuri’u 99,445 sai George Moghalu na LP ya samu kuri’u 10,576, yayin da John Nwosu na ADC ya samu kuri’u 8,208.
An kuma samu fitowar masu kada kuri’a mafi rauni sosai, domin daga cikin masu rajista miliyan 2,788,864, mutum 598,229 ne kawai aka tantance, wanda ke nuni da kashi 21.4 kacal.

Source: Twitter
2. Rarrabuwar kawunan jam’iyyun adawa, rashin tsari
An ruwaito jam’iyyar LP tana cikin matsala sosai, sakamakon rikicin cikin gida, zabubbukan da aka yi sau biyu da rashin tabbataccen dan takara.
Haka kuma jam’iyyar PDP ta shiga rikicin shugabanci, ficewar mambobi da dama, da rashin amincewar jama’a da ita.
Rahotanni sun nuna cewa a wasu kananan hukumomi, PDP ta samu kuri’u kadan ƙwarai, saboda raguwar tasirin jam’iyya a ƙasa.

Source: Twitter
3. Karfi da kasancewar APGA a matsayin mai mulki
Gwamna Soludo ya yi amfani da matsayin sa na mai ci da kuma ayyukan da ake iya gani, musamman a fannoni kamar hanyoyi da ilimi, don samun goyon bayan jama’a.
Bugu da ƙari, jam’iyyar APGA tana da tsari mai karfi tun daga tushe a karkara, wanda ya ba ta damar yin nasara a dukkan kananan hukumomi 21 na jihar.
Hada matsayin gwamnati mai ci da kyakkyawan tsari a ƙasa ya baiwa APGA damar mamaye fagen siyasa gaba ɗaya, Punch ta tabbatar da haka.

Kara karanta wannan
Zaben Anambra: Dan takarar LP ya bayyana abin da ya hana shi lashe kujerar gwamna
4. Sayen kuri’u da zargin rashin gaskiya a zabe
An samu zarge-zargen yawaitar sayen kuri’u a wurare da dama, inda ake cewa ana biyan mutane daga ₦3,000 zuwa ₦20,000 don kuri’a ɗaya.
Wasu suka ce wakilan APGA suna ba da kusan ₦5,000 ga kowane mai jefa kuri’a, yayin da wakilan APC suka bayar da har zuwa ₦10,000.
Ko da yake ba a iya tabbatar da adadin da aka saya ba, wannan yawaitar raba kudi ta lalata amincin zabe, ta kuma baiwa masu kudi da iko fifiko.

Source: Facebook
5. Karancin fitowar masu kada kuri’a a zaben
A zaben 2025, fitowar masu kada kuri’a ta tsaya a 21.4% (598,229 daga cikin 2,788,864 masu rajista).
Wannan ba sabon abu ba ne a jihar, domin zabubbukan baya ma suna tsakanin kashi 20 zuwa 25, wani lokaci ma kasa da haka.
An danganta hakan da fargabar rashin tsaro, barazana daga ’yan tawayen yankin, da rashin kwarin gwiwa ga tsarin zabe.

Source: Twitter
6. Matsalolin tsaro da rashin amincewa da tsarin zabe
Rahotanni sun nuna cewa barazana, tsoro, da yanayin rashin kwanciyar hankali sun hana mutane fitowa kada kuri’a a wasu wurare.
Haka kuma an samu matsaloli a rajistar masu zabe, jinkirin kayan aiki, da rashin amincewa da hukumomin zabe.
Lokacin da jama’a ke jin tsoro ko ba su yarda da tsarin ba, yana wahalar da jam’iyyun adawa wajen motsa masu kada kuri’a, yayin da hakan ke taimakawa gwamnati mai ci.
Abubuwan sani game da Gwamna Soludo
A baya, an ji cewa Gwamna Charles Chukwuma Soludo na Anambra na daga cikin yan takara a zaben gwamnan gwamnan jihar.
Bayan fafatawa, hukumar zabe ta INEC ta sanar da cewa Gwamna Charles Soludo da ya yi takara karkashin jam'iyyar APGA ya yi nasara.
Wannan rahoton ya yi duna kan wasu muhimman abubuwa game da zababben gwamnan wanda ya dawo karo na biyu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


