Sabon Rikici Ya Barke a APC, Ana Kokarin Tilasta Shugaban Jam'iyya Ya Yi Murabus
- Shugabannin APC a Cross River sun mamaye sakatariyar jam’iyyar, inda suka nemi Alphonsus Eba ya yi murabus
- Sun zarg shugaban APC na jihar da aikata rashin gaskiya, nuna isa, da rashin biyan hakkokin shugabannin jam’iyyar
- Sai dai, Eba ya musanta zarge-zargen, inda ya ce an dakatar da biyan kudin ne saboda binciken zargin satar kudin jam’iyya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Cross River - APC a Cross River ta fada cikin rikicin cikin gida bayan jagororin jam’iyyar sun bukaci shugaban jam'iyya na jihar ya yi murabus.
An ce shugabannin APC a ƙananan hukumomi da sakatarori 35 sun yi zanga-zanga, suna neman Barrister Alphonsus Eba, ya sauka daga kujerar shugaba.

Source: Twitter
Calabar: Ana so shugaban APC ya yi murabus
Jaridar Punch ta rahoto cewa masu zanga-zangar sun mamaye babbar sakatariyar jam’iyyar da ke Calabar, babban birnin jihar a ranar Laraba.

Kara karanta wannan
'PDP ta mutu,' Fayose ya fadi sunan gwamnan PDP da zai koma jam'iyyar APC a Arewa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu zanga zangar suna ɗauke da kwalaye, wadanda aka yi wa rubutu daban daban, ciki har da “Dole Okadigbo ya yi murabus” da “Mun gaji da shugaba mai girman kai."
A cewar shugabannin, Eba ya nuna iko fiye da kima, ya gaza gudanar da ayyukansa cikin gaskiya kuma ya hana jami’an jam’iyya albashinsu tsawon watanni uku.
Sun kuma zarge shi da kokarin karɓe kuɗin da ake warewa don gudanar da ayyukan jam’iyya a ƙananan hukumomi da kuma tayar da fitina tsakanin shugabannin gundumomi da na jiha.
An zargi shugaban APC da rashawa
A cikin wata sanarwa da suka fitar bayan taronsu a Calabar, kungiyar shugabannin APC na kananan hukumomi da sakatarori ta ce Eba yana tafiyar da jam’iyyar ne a halin “danniya da son kai.”
Sun bayyana cewa yayin da mambobin kwamitin gudanarwa na jiha 36 ke karɓar ₦40m a wata, sama da jami’an jam’iyya 5,700 a matakin ƙasa suna raba ₦9.2m kawai.
Haka kuma, sun zargi Eba da rashin mika kudaden da aka tara daga sayen fom na zaben 2023 da sauran kudaden da suka kamata su shiga asusun jam’iyyar ta kasa.
Jaridar Tribune ta rahoto wani bangare na sanarwar ya ce:
“Abubuwan da Eba ke yi sun raba kawunan shugabanni kuma sun lalata tsarin jam'iyyar APC tun ma kafin a je zaben 2027.
“Ya kamata Eba ya yi murabus cikin mutunci domin ba da dama ga wani kwararre ya jagoranci jam’iyyar zuwa 2027."

Source: Original
“An dakatar da biyan kudi saboda bincike” - Eba
Da yake mayar da martani, Alphonsus Eba ya karyata zarge-zargen, yana cewa an dakatar da biyan kudaden ne kawai har sai an kammala bincike kan zargin satar kudaden jam’iyya da wasu shugabanni suka aikata.
Ya zargi shugabannin da satar sama da ₦60m da aka ware domin jami’an gundumomi, yana mai cewa wasu daga cikinsu na cinye kudaden ƙananan hukumomi ba tare da bahasi ba.
Ganduje: Shugaban APC ya yi murabus
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Abdullahi Ganduje ya yi murabus daga shugabancin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya bayan shekaru biyu a ofis.
An ce za a maye gurbinsa da wani mataimakin shugaban jam’iyya na ƙasa har zuwa lokacin babban taron jam’iyya da za a yi a Disamba.
Murabus din da ya yi ya biyo bayan matsin lamba daga yankin Arewa ta Tsakiya da kuma rikice-rikicen cikin gida da ke kara ƙaruwa, kamar yadda rahoto ya nuna.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

