Babu zaman lafiya a PDP, ana zargin Shugabannin Jam’iyya da wawurar Naira Biliyan 10
- Prince Kassim Afegbua ya na zargin Jam’iyyar PDP da salwantar da kudi
- Afegbua ya ce an lakume duk kudin saida fam a karkashin Uche Secondus
- Uwar jam’iyya ta maida martani, ta ce babu wani wanda ya wawuri N10bn
Wata sabuwar rigima ta na neman kunno kai a jam’iyyar hamayya ta PDP inda ake tuhumar shugabannin jam’iyya da zargin satar makudan kudi.
Daily Trust ta ce ana zargin shugaban PDP na kasa, Prince Uche Secondus da ‘yan majalisar gudanarwarsa ta NWC da zargin satar kudin saida fam.
Rahoton ya ce ana zargin majalisar NWC da salwantar da Naira biliyan 10 da aka samu daga saida fam din tsaya wa takara a shekaru hudun da su ka wuce.
KU KARANTA: 'Yan siyasan Ibo da za su nemi kujerar Shugaban kasa a 2023
Wani daga cikin manyan jam’iyyar adawar ya kai wannan magana zuwa gaban hukumomin da ke yaki da masu satar dukiyar al’umma na EFCC da ICPC.
Prince Kassim Afegbua ya kai korafi inda yake zargin shugabannin jam’iyyarsa da salwantar da kusan Naira biliyan 10 da aka samu ta hanyar fansar fam.
A cewar Kassim Afegbua, an samu wadannan kudi ne daga wadanda su ka tsaya takarar shugaban kasa, gwamnoni, sanatoci, da ‘yan majalisa daga 2017.
PDP ta maida martani ta bakin sakataren yada labarai na kasa, Kola Ologbondiyan, wanda ya karyata wannan zargi ya ce babu gaskiya da hankali a ciki.
KU KARANTA: Boko Haram su na gab da shiga Abuja - Gwamna
Kola Ologbondiyan ya ce abin da jam’iyya ta samu Naira biliyan 4.6 ne kuma sun yi kasafin kudin abubuwan da ake bukata kamar yadda dokar batar da kudi ta ce.
Ologbondiyan ya ce kafin a amince da kasafin kudin jam’iyya, sai da aka bi ta hannun majalisar NWC, kungiyar gwamnoni, da kwamitin amintattu da sauran manya.
Uwar jam’iyya ta gabatar da wannan kasafi gaban majalisar koli ta NEC, wanda ta amince da kundin.
A farkon makon nan ku ka ji tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ziyarci jihar Sokoto, ya yaba da aikin Gwamnatin PDP a karkashin Aminu Waziri Tambuwal.
Gwamnan ya samu yabon Olusegun Obasanjo saboda irin ‘aikin’ da yake yi. Obasanjo ya jinjinawa Tambuwal, ya ce shugaba ne mai hangen nesa da gyara a al’ummarsa.
Asali: Legit.ng