Sanatoci Sun Yi Yunkurin Tsige Shugaban Majalisar Dattawa, Akpabio? Bayanai Sun Fito

Sanatoci Sun Yi Yunkurin Tsige Shugaban Majalisar Dattawa, Akpabio? Bayanai Sun Fito

  • Sanata Opeyemi Bamidele ya musanta ikirarin abokin aikinsa, Orji Kalu cewa an yi yunkurin tsige shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio
  • Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Bamidele ya ce babu wani shiri ko tunanin cire Akpabio, rahoton da ke yawo ba gaskiya ba ne
  • Wannan na zuwa ne bayan Sanata Orji Kalu ya tabbatar da cewa an yi yunkurin sauke Akpabio daga shugabanci amma ba a cimma nasara ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - An fara samun bayanai masu cin karo da juna kan zargin yunkurin tsige shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio.

Hakan ya biyo bayan ikirarin Sanata Orji Uzor Kalu, wanda ya tabbatar da cewa wasu sanatoci sun yi yunkurin cire Akpabio amma ba su samu nasara ba.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
Hoton shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio Hoto: Nigeria Senate
Source: Facebook

Sanata Bamidele ya karyata Kalu

Kara karanta wannan

Kalu: Dalilin wasu 'yan majalisa na yunkurin tsige Akpabio daga shugabanci

Channels tv ta ruwaito cewa shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele ya musanta labarin cewa an yi kokarin sauke Akpabio daga shugabanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Bamidele ya bayyana cewa rahotannin ba daidai ba ne kuma an ƙirƙire su ne don tayar da hankula a cikin majalisa.

Da yake jawabi a zauren majalisar a ranar Laraba, Bamidele ya bayyana cewa babu wata tattaunawa ko shiri da aka taba yi tsakanin ’yan majalisar dattawa kan batun tsige Akpabio.

Ya jaddada cewa Majalisar Dattawa na da cikakken haɗin kai kuma ta mai da hankali kan manyan batutuwan kasa maimakon ta bari labaran ƙarya su karkatar da hankalinta.

Shin an yi yunkurin tsige Akpabio?

“Babu wani yunkuri daga wani abokin aikinmu, ko wata tattaunawa da ta shafi shirin cire Shugaban Majalisar Dattawa daga mukaminsa.
"Mun haɗa kanmu wuri guda, kuma mun sha alwashin ba za mu bar duk wani abin da zai kawo mana rabuwar kai ba, saboda akwai muhimman batutuwan kasa da ke bukatar kulawar mu.
"Irin waɗannan rahotanni da ake yadawa an shirya su ne kawai don haifar da rudani."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Wasu sanatoci sun yi yunkurin tsige shugaban Majalisar Dattawa

- Sanata Bamidele.

Sanatocin APC 2 sun saba wa juna

Wannan bayanin na Sanata Bamidele ya saba da kalaman Sanata Orji Uzor Kalu, mai wakiltar Abia ta Arewa, wanda a baya ya ambaci cewa an yi yunkurin tsige Akapabio amma ba a ci nasra ba.

Sanata Akpabio da Bamidele.
Hoton shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Sanata Bamidele Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Sanata Bamidele ya sake tabbatar da cewa babu wani shiri ko yunkuri a cikin majalisar na tunanin cire daya daga cikin shugabanninta.

Ya kuma jaddada cewa majalisar dattawa na zaune lafiya, kwanciyar hankali, haɗin kai, da kuma mai da hankali kan gudanar da ayyukan da doka ta dora a kanta.

Majalisa ta amince da bukatar Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Dattawa ta amince da bukatar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta sake dauko wa Najeriya bashin makudan kudi.

Majalisar ta amince da bukatar karbo rancen ne a zamanta na ranar Laraba, 12 ga watan Nuwamba, 2025 bayan tafka muhawara kan rahoton kwamitin kula da ciyo bashi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tura manyan kusoshi zuwa Landan, an fara kokarin dawo da Sanata Ekweremadu Najeriya

A wasikar da ya rubuta, Shugaba Tinubu ya shaida wa Majalisar Dattawa cewa wadannan kudi za su taimaka wajen aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2025.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262