'El Rufa'i zai Zama Shugaban Kasa,' Dan ADC Ya Yi Mafarki kan Zaben 2027
- Wani dan jam’iyyar, ADC Nuhu Abdullahi Sada ya bayyana mafarkinsa da ke nuna cewa Nasir El-Rufa’i zai zama shugaban ƙasa a 2027
- Ya ce mafarkinsa na da alaka da tafiyar siyasar da ake yi yanzu, inda wasu manyan ‘yan siyasa suka koma jam’iyyar ADC daga PDP da APC
- Hon. Sada ya bayyana cewa jam’iyyar ADC tana neman haɗin kai da sauya gwamnati a 2027 domin ceto Najeriya daga halin da take ciki
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Wani dan jam’iyyar ADC, Hon. Nuhu Abdullahi Sada, ya ja hankalin jama’a bayan ya bayyana mafarki da ya yi game da Malam Nasir El-Rufa’i da Rauf Aregbesola.
Sada ya ce duk lokacin da ya yi mafarki mai kyau, yakan zama gaskiya a zahiri saboda haka abin da ya gani zai iya tabbata.

Source: Twitter
A sakon da ya wallafa a X, ya bayyana cewa wannan karon, mafarkinsa ya nuna cewa El-Rufa’i zai zama shugaban ƙasa a 2027, yayin da Aregbesola zai kasance mataimakinsa.
Mafarkin El-Rufa'i ya ci zaben 2027
A cewarsa, mafarkin ya nuna El-Rufa'i da Aregbesola sun tafi aikin Umrah ƙasar Saudiyya sun shiga dakin Ka'aba tare da Sarkin Saudiyya da Yarima mai jiran gado.
Sada ya ce,
“Duk lokacin da na yi mafarki mai kyau, yakan tabbata a zahiri. Mafarkina na yau shi ne Malam Nasir El-Rufa’i ya zama shugaban ƙasa a 2027, Rauf Aregbesola kuma ya zama mataimakinsa.
"Na gan mu a ƙasar Saudiyya muna Umrah tare da Sarkin Saudiyya da Yarima mai jiran gado.
"Muna roƙon cigaban Najeriya, kuma Insha Allah wannan haɗin gwiwar za ta tabbata a 2027. Allah Ya sa hakan ya zama gaskiya. Amin.”
Ya ƙara da cewa mafarki ya dace da canjin siyasar a Najeriya, musamman yadda manyan ‘yan siyasa ke komawa jam’iyyar ADC domin haɗa kai wajen fitar da ƙasar daga halin da take ciki.
Legit ta tattauna da Hon. Sada
A tattauna wa da Hon. Sada ya bayyana cewa yana jam'iyyar ADC domin kalubalantar APC a zaben 2027.
“A halin yanzu muna aiki a ƙarƙashin jam’iyyar ADC. Kamar yadda kuka sani, siyasa tana tafiya da tsarin jam’iyya.
Alhaji Atiku Abubakar ya koma ADC daga PDP, haka kuma Rauf Aregbesola daga APC zuwa ADC — wannan shi ne wani mataki na haɗin kai da gyaran kasa.”
Ya jaddada cewa jam’iyyar ADC ba ta dogara da mutum guda ba, amma tana neman haɗin kan ‘yan Najeriya domin kawar da jam’iyyar APC daga mulki a shekarar 2027.
Burin ADC game da siyasar Najeriya
Sada ya bayyana burinsa cewa idan El-Rufa’i da Aregbesola suka zama ‘yan takarar ADC, za su tabbatar da bin tsarin siyasa da kundin tsarin mulki na Najeriya.

Source: Twitter
Sai dai ya ce ko da ba su samu tikitin takara ba, zai ci gaba da goyon bayan duk wanda jam’iyyar ADC ta tsayar domin kifar da Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Kara karanta wannan
Buhari ya fito a mafarkin wata mata da farin kaya, ta ba da labarin me ya fada mata
Dan majalisar Kano ya fita daga NNPP
A wani labarin, kun ji cewa dan majalisar wakilai daga jihar Kano ya fita daga jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar.
Hon. Sagir Ibrahim Koki ya sanar da fita daga NNPP ne a wata wasika da ya tura wa shugaban jam'iyyar a mazabarsa.
A wasikar, ya bayyana cewa ya fita daga NNPP ne domin samun damar yin aiki ga mutanen mazabarsa yadda ya kamata.
Asali: Legit.ng

