Zaben Anambra 2025: Abubuwa 7 da Suka Taimaka wa Gwamna Soludo Ya Doke APC, PDP
- Gwamna Charles Soludo na jam’iyyar APGA ya sake lashe zaben gwamnan jihar Anambra karo na biyu da kuri’u 422,664
- Gwamna Soludo ya ci zabe a dukkan kananan hukumomi 21, abin da ya faru sau biyu kacal a tarihin siyasar Anambra
- Legit Hausa ta zakulo manyan abubuwa 7 da suka taimaka Soludo ya ci zaben, ciki har da alakarsa da Shugaba Bola Tinubu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Anambra - Gwamna Charles Chukwuma Soludo, ya sake lashe zaben gwamnan Anambra karo na biyu, bayan samun kuri'u 422,664 a zaben da aka gudanar ranar Asabar.
Soludo, wanda ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar APGA, ya doke babban abokin hamayyarsa, Nicholas Ukachukwu na APC, wanda ya samu kuri'u 99,445.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa dan takarar jam’iyyar YPP, Paul Chukwuma, ya kare a matsayi na uku da kuri'u 37,753, yayin da George Moghalu na LP ya samu kuri'u 10,576.

Kara karanta wannan
Zaben Anambra: Dan takarar LP ya bayyana abin da ya hana shi lashe kujerar gwamna
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan zaben ya shiga tarihi, domin Soludo ya lashe zabe a dukkan kananan hukumomi 21 na Anambra — karo na biyu kacal da haka ta taba faruwa tun bayan nasarar tsohon gwamna Willie Obiano a 2017, wanda shima ya fito daga jam’iyyar APGA.
Dalilai 7 da suka ba Soludo nasara a zaben Anambra
Legit Hausa ta tattaro wasu manyan dalilai da suka sanya Gwamna Charles Soludo ya lashe zabe karo na biyu a Anambra.
1. Fa’idar zama gwamna mai ci ta taimaka masa
Daya daga cikin muhimman dalilan da suka taimaka wa Soludo wajen samun wannan nasara ita ce fa’idar kasancewarsa gwamna mai ci.
Tsohon gwamnan babban bankin kasa (CBN) ya shiga wannan zabe ne da cikakken goyon bayan gwamnati da tsarin siyasar jihar.
Yayin da yake mulki tun daga 2021, Soludo ya mallaki cikakken ikon jam’iyya a matakan kananan hukumomi da gundumomi, wanda ya bashi damar taimakawa al'umma da sarakuna.
Masana siyasa sun bayyana cewa ikon da gwamna yake da shi wajen shimfida ayyuka, yin gyare-gyare da kula da tsaro ya kara masa farin jini a tsakanin jama’a.
Haka kuma, kasancewarsa ba shi da abokin hamayya a zaben fitar da gwani na APGA, ya ba shi damar mayar da hankali kacokan kan babban zabe, maimakon rigingimu na cikin gida.
2. Ayyukan raya kasa da suka kara masa farin jini
A zangonsa na farko, Soludo ya kafa tarihin aiki a fannoni daban-daban kamar tsaro, gine-gine, ilimi, da kiwon lafiya.
Shirin Agunechemba Vigilante, wanda ya kaddamar a watan Janairu 2025, ya taimaka wajen dakile hare-haren ‘yan bindiga da masu tayar da kayar baya a yankunan Ihiala, Nnewi ta Kudu, da Aguata.
A bangaren gine-gine, gwamnatin sa ta gina da gyara hanyoyi da dama ciki har da gadar Ekwulobia, wadda ake dab da kammaluwa. Wannan ya kawo sauyi ga al’ummomin karkara da ke fama da matsalar hanyoyi.
Haka kuma, Soludo ya kafa tsarin ilimi kyauta ga daliban makarantun gwamnati da kuma kulawar haihuwa da jinya kyauta a asibitoci, abin da ya kara masa karbuwa a tsakanin iyalai marasa karfi.
Manufar sa ta “Solution Agenda” wadda ta mayar da hankali kan rage bambancin rayuwa da karfafa cigaban al’umma, ta sa mutane da dama suna kallonsa a matsayin shugaba mai hangen nesa.
3. Karfin jam’iyyar APGA a Anambra

Source: Original
Jam’iyyar APGA ta kasance ginshikin siyasa a jihar Anambra tsawon shekaru fiye da goma, tun bayan da Peter Obi ya kafa tarihi a 2006.
APGA ta kafa kyakkyawan tsarin kungiyoyi a kananan hukumomi da gundumomi 326, wanda ya tabbatar da cewa tana da tasiri sosai a harkokin zabe.
A wannan zaben, jam’iyyar ta kara amfani da karfinta ta hanyar kafa “Solution Marshals”, wata sabuwar cibiyar karfafa zabe da ke amfani da fasahar zamani wajen bibiyar masu zabe da karfafa fitowarsu a rumfunan kada kuri’a.
Wannan ya taimaka wajen tabbatar da cewa jam’iyyar ta yi nasara sosai a yankunan karkara da kananan hukumomi, inda yawanci ake yanke sakamakon zabe.
4. Goyon bayan ‘yan kasuwa da masu fada a ji
Siyasar Anambra ta sha bamban da ta sauran jihohi saboda yawan manyan ‘yan kasuwa masu kudi da kuma karfin fada a ji.
A wannan zabe, Soludo ya samu goyon bayan fitattun attajirai kamar Prince Arthur Eze, wanda ya yi alkawarin tallafa masa da dukkan karfinsa.
Tallafin da ya samu daga masana’antu, malamai, sarakuna da shugabannin addini ya kara masa martaba a idon jama’a.
Haka kuma, hadin kai tsakanin jam’iyyar APGA da manyan masu kudi ya tabbatar da yakin neman zabensa ya fi na abokan hamayya karfi da tsari.
Masu sharhi sun ce, irin wannan goyon bayan daga ‘yan kasuwa da attajirai yana nuni da aminci da kwarin gwiwa da suka gani a mulkinsa, wanda ya ba Soludo damar lashe zaben cikin natsuwa.
5. Dangantakarsa da Shugaba Tinubu ta taimaka
Ko da yake Soludo cikakken dan jam’iyyar APGA ne, amma ana ganin dangantakarsa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta taimaka masa wajen samun goyon bayan gwamnatin tarayya.
Tun lokacin da aka naɗa shi a matsayin mamba na kwamitin shawarwarin tattalin arzikin shugaban kasa a 2024, ya kara samun kusanci da gwamnati mai mulki.
Hakan ya rage masa adawa daga jam’iyyar APC, kuma ya nuna cewa ba ya gaba da gwamnati mai ci a matakin tarayya, in ji rahoton shafin All Africa.
Wani hoto da ya dauka yana sanya hula mai alamar Tinubu ya haifar da jita-jita game da sabuwar dangantaka mai amfani tsakanin su da kuma yiwuwar ko zai sauya sheka ne.
Wannan kusanci ya taimaka masa wajen samun saukin gudanar da zabe, domin gwamnati ta tarayya ta nuna karfin gwiwa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a lokacin zabensa.
6. Soludo ya ci moriyar tsarin rabon mulki
Siyasar jihar Anambra tana bin tsarin rabon mulki bisa yankuna, wanda ke baiwa kowanne yanki damar yin mulki a jere.
Soludo, wanda ya fito daga Anambra ta Kudu, ya ci moriyar wannan tsarin, domin jama’a sun ga dacewar barinsa ya kammala wa’adin mulki kafin a sauya yanki.
Idan wani dan takara daga wani yanki ne ya lashe, hakan zai karya tsarin da aka gina tsawon shekaru, wanda ya sa mutane da dama suka zabi ci gaba da tsarin Soludo domin tabbatar da daidaito.

Source: Twitter
7. Farar jini da goyon bayan jama’a a jiha
Rahotannin jaridar Premium Times sun nuna cewa Soludo ya samu goyon bayan jama’a a dukkan mazabun zabe, ciki har da wadanda ba daga yankinsa ba.
Masu zabe da dama sun bayyana cewa ayyukansa a shekaru hudu da suka gabata sun bambanta shi da sauran ‘yan takara.
Wani dan jarida mai suna David Eleke ya bayyana cewa:
“Anambra ta taba ganin gwamnatoci da dama, amma irin tsarin Soludo na gaskiya da bin doka ya bambanta da na baya.”
Wani mai sharhi kuma ya ce:
“Mutane sun zabe shi saboda suna ganin yana aiki. Idan ba ya aiki, da mutane ba su fito suka kada masa kuri’a haka ba.”
Abin da Soludo ya ce bayan lashe zabe
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Anambra, Farfesa Charles Chukwuma Soludo, ya yi tsokaci kan nasarar da ya sake samu a zabe.
Farfesa Charles Soludo ya yabawa mutanen jihar Anambra kan yadda suka sake ba shi damar mulkarsu har na tsawon shekara hudu masu zuwa.
Gwamnan ya bayyana cewa mutanen jihar ba su ga komai ba domin zai ci gaba da gudanar da ayyuka masu muhimmanci da inganta rayuwar jama'a.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng




