Wata Sabuwa: Wasu Sanatoci Sun Yi Yunkurin Tsige Shugaban Majalisar Dattawa

Wata Sabuwa: Wasu Sanatoci Sun Yi Yunkurin Tsige Shugaban Majalisar Dattawa

  • Sanata Orji Uzor Kalu ya ce an yi yunkurin tsige shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio daga kan mukaminsa
  • Tsohon gwamnan jihar Abia ya tabbatar da cewa yunkurin bai cimma nasara ba saboda kan sanatoci a hade yake
  • Kalu ya kuma yi ikirarin cewa nan ba da jimawa ba Gwamna Charles Chikwuma Soludo na jihar Anambra zai dawo APC

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Sanatan Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu ya tabbatar da cewa wasu sanatoci sun yi yunkurin tsige Shigaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio.

Sanata Kalu, tsohon gwamnan jihar Abia ya bayyana cewa kan sanatoci a hade yake, wanda hakan ya ba su damar dakile yunkurin sauke Akpabio daga kujerarsa.

Sanata Orji Uzor Kalu.
Hoton sanatan Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu a zauren Majalisar Dattawa Hoto: Urji Uzor Kalu
Source: Twitter

Sanatan ya fadi haka ne yayin da yake hirada manema labarai a zauren Majalisar Dattawa da je Abuja yau Talata, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hanyoyin da Tinubu da Nuhu Ribadu suka bullo wa barazanar harin Amurka sun fara jan hankali

Sanatoci sun dakile shirin tsige Akpabio

Da yake ba da labarin abin da ya faru, Sanata Kalu ya tabbatar da cewa an yi ƙoƙarin cire Akpabio daga kujerarsa, amma aka gaza cimma burin.

“Eh, duk da cewa an yi yunkuri, amma ba mu bar hakan ta faru ba. Shi ya sa nake cewa kanmu a hade yake, mu iyali guda ne, kuma hakan ba zai taba faruwa ba,” in ji Kalu.

Ya jaddada cewa akwai hadin kai Majalisar Dattawa kuma ta mai da hankali kan aikinta na dokoki, musamman waɗanda za su taimaka wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen fitar da Najeriya daga ƙalubalen tattalin arziki.

“Ko da wata matsala ta gitta, mu a Majalisa mun mai da hankali wajen samar da dokokin da za su taimaka wa Shugaba Tinubu magance matsalolin tattalin arzikin da ‘yan ƙasa ke fama da su.
“Mun fi tunanin halin da al’umma ke ciki. Dokokin da muke yi suna da fa’ida ga talakawa, domin muna son tabbatar da cewa kowa zai iya cin abinci sau uku a rana,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Anioma: Shugaba Tinubu, Akpabio da sanatoci 97 sun goyi bayan kirkiro jiha 1 a Najeriya

Gwamna Soludo zai koma APC

A kan batun siyasa a yankin Kudu maso Gabas, Sanata Kalu ya yi hasashen cewa Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, na iya shigowa jam’iyyar APC nan ba da jimawa ba.

“Ina ganin bayan kammala abubuwan da je gabansa, Soludo mutum ne mai tunanin ci gaba irin mu, kamar ni, Shugaba Tinubu, Shugaban Majalisa Akpabio da sauran gwamnonin APC a Imo, Ebonyi, da Enugu.
"Don haka ba abin mamaki ba ne idan ya shigo cikinmu. A gaskiya an tabbatar min cewa zai koma APC. Ba shi da wani zaɓi illa ya zo ya haɗa kai da mu,” in ji Kalu.
Sanata Godswill Akpabio.
Hoton shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Kalu na burin zama shugaban kasa a 2039

A wani labarin, kun ji cewa Orji Uzor Kalu ya bayyana cewa da yiwuwar ya nemi kujerar shugaban kasa a 2039 bayan Arewa ta kammala wa'adin shekaru takwas.

Tsohon gwamnan jihar Abia ya kafa misali da Shugaba Donald Trump na Amurka yayin da aka tuna masa da batun shekarunsa a 2039.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima na da hannu a kafa Boko Haram? Ali Modu Sherrif ya fadi gaskiya

Sanata Kalu ya jaddada cewa yana da ƙwarewa, nagarta da gogewa da za su iya ba shi damar jagorantar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262