Ana Wata ga Wata: Jam'iyyar PDP Ta Sake Samun Matsala kan Babban Taronta na Kasa
- Mai shari’a Peter Lifu ya hana PDP gudanar da taronta na kasa, bayan korafin tsohon gwamnan jihar jigawa, Sule Lamido
- Lamido ya ce an hana shi sayen fom din neman kujerar shugabancin PDP, wanda ya saba wa dokokin gudanar da jam'iyyar
- Wannan hukunci ya rushe matakin da kotun Oyo ta dauka a 4 ga Nuwamba, 2025 inda ta amince PDP ta gudanar da taron
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta hana jam’iyyar PDP gudanar da taronta kasa da ake shirin gudanarwa a ranar 15 da 16 ga Nuwamba, 2025 a Ibadan.
Mai shari’a Peter Lifu ya bayar da sabon umarnin ne a ranar Talata, yayin da yake yanke hukunci kan karar da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya shigar.

Kara karanta wannan
Kotu ta bada belin tsohon Shugaban Faransa Sarkozy, ya fito bayan mako 3 a kurkuku

Source: Twitter
Lamido ya shigar da kara yana korafi cewa jam’iyyar ta hana shi damar sayen fom din neman shugabancin jam’iyyar, wanda hakan ya tauye masa ‘yancin shiga zabe, in ji rahoton Channels TV.
Mai shari’a Lifu ya ce PDP ta karya dokokin da suka tsara yadda ake gudanar da irin wannan taro, tare da kin bin sharuɗɗan da doka ta tanada.
PDP ta karya tsarin da doka ta tanada
A cewar mai shari’a Lifu, shaidun da Lamido ya gabatar sun nuna cewa jam’iyyar bata wallafa jadawalin taronta na kasa domin mambobinta su gani ba, wanda hakan ya saba wa doka.
Ya ƙara da cewa Sule Lamido zai fi shan wahala idan aka ci gaba da taron ba bisa doka ba, don haka ya fi dacewa a dakatar da wannan shirin taro.
“A tsarin mulki, wajibi ne a bi doka a duk wani abu da ake gudanarwa. Keta wannan ka’ida na iya zama barazana ga tsarin dimokuraɗiyya gaba ɗaya,” in ji mai shari’a Lifu.
Ya kuma bayyana cewa bisa ga sashe na 6 na kundin tsarin mulkin 1999, kotu tana da ikon tabbatar da adalci ba tare da tsoro ko son rai ba, kuma duk lokacin da kotu ta gaza yin aikinta, hakan zai iya haifar da rudani da rashin doka a ƙasar.
Kotu ta hana INEC zuwa taron PDP
A hukuncinsa, mai shari’a Lifu ya kuma hana Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) zuwa taron PDP don sa ido, ko amincewa da duk wani sakamako da jam'iyyar za ta fitar daga irin wannan taro da za a gudanar.
A baya, a watan Oktoba 2025, wata Babbar Kotu ta hana PDP ci gaba da shirinta na taron kasa, bisa karar da wasu mambobi uku na jam’iyyar suka shigar.
Mambobin su ne Austin Nwachukwu (shugaban PDP na Imo), Amah Abraham Nnanna (shugaban PDP na Abia), da Turnah Alabh George (sakataren kasa na PDP, Kudu maso Kudu).
Wadanda suka shigar da karar sun yi zargin cewa shirin taron ya sabawa dokar zabe da kundin tsarin jam’iyyar.

Source: UGC
Kotun Oyo ta ba PDP damar gudanar da taro
Amma kuma, a ranar 4 ga Nuwamba, kotun Oyo ta bai wa PDP damar ci gaba da shirinta na taron kasa bayan wani umarnin wucin gadi da mai shari’a Akintola ya bayar, bisa roƙon da Folahan Adelabi ya shigar.
Sai dai a ranar Litinin da ta gabata, mai shari’a Akintola ya dage sauraron ƙarar don bai wa ɓangarorin biyu damar gabatar da hujjoji kafin a ci gaba da shari’ar.
Sabon umarnin kotun tarayya a Abuja na nufin cewa duk wani shiri na taron PDP yanzu ya tsaya cik har sai an tabbatar da cikakken bin doka kamar yadda kundin tsarin jam’iyyar da dokar zabe suka tanada.
PDP ta sauya wurin babban taronta
Tun da fari, mun ruwaito cewa, PDP ta sauya wuri da lokacin gudanar da babban taron zaben shugabanninta na kasa, inda ta mayar da shi zuwa Ibadan.
Bayan dage taron daga Agusta zuwa Nuwamba, PDP ta ayyana cewa ta warware rikice-rikicenta tare da fatan komawa mulki a 2027.
PDP ta umurci NWC da ta gurfanar da ‘yan siyasar da suka sauya sheka bayan lashe zaɓe a jam’iyyar bisa tanadin tsarin mulki na kasa.
Asali: Legit.ng

