Matar Shugaban APC Ta Fara Gangamin Tazarcen Tinubu, Ta Yi Kira ga Matan Najeriya

Matar Shugaban APC Ta Fara Gangamin Tazarcen Tinubu, Ta Yi Kira ga Matan Najeriya

  • Matar shugaban jam’iyyar APC ta fara gangamin wayar da kan mata don tabbatar da nasarar sake zaben Shugaba Bola Tinubu a 2027
  • Ta bukaci mata a jam’iyyar su yi magana da murya daya wajen tallata manufofin Renewed Hope Agenda na shugaba Tinubu
  • Hakan ta faru ne yayin wani taro a Abuja karkashin kungiyar Women’s Leadership Network, inda aka jaddada bukatar karfafa mata

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Matar shugaban jam’iyyar APC, Martina Yilwatda, ta kaddamar da wani shiri na gangamin neman tazarcen Bola Tinubu a zaben 2027.

Ta yi magana tana kira ga mata su fara wayar da kai tun daga tushe don tallata manufofin Renewed Hope Agenda na Bla Tinubu.

matar shugaban APC Martina Yilwatda
Shugaban APC tare da matarsa, Martina Yilwatda. Hoto: @julietjok
Source: Twitter

Punch ta rahoto cewa Martina ta bayyana hakan ne a wani taro da kungiyar Women’s Leadership Network ta shirya a Abuja.

Kara karanta wannan

Dan Fodiyo: Majalisar shari'ar Musulunci ya roki Tinubu ya sauya shugaban INEC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar matar shugaban APC

Martina Yilwatda ta bayyana cewa lokaci ya yi da mata za su tashi tsaye wajen tabbatar da nasarar Shugaba Tinubu a karo na biyu.

Ta ce:

“Dole mu fara aiki tun yanzu don tabbatar da tazarcen Shugaban kasa Bola Tinubu, domin hakan ba zai yiwu ba sai da hadin kan mata ta hanyar cikakken gangamin wayar da kai.”

Ta kara da cewa gwamnati ta nuna goyon baya sosai ga mata ta fannin mukamai, tallafi da dama a hukumomi, don haka lokaci ya yi da za su maida martani ta hanyar nuna goyon baya a 2027.

“Ina rokonku ku ci gaba da yada sakon Renewed Hope Agenda na Shugaban kasa, domin ya yi abubuwa masu yawa ga mata da ‘yan Najeriya baki daya,”

Inji ta

Maganar ba mata mukami a Najeriya

Har ila yau, matar shugaban jam’iyyar ta bayyana cikakken goyon bayanta ga kudirin ware mukamai\kujeru ga mata da ke gaban Majalisar Dokoki.

Kara karanta wannan

'Wane hali muke ciki,' Tsohon hadiminsa ya nemi Tinubu ya yi bayani kan barazanar Trump

Ta yi magana tana mai cewa lokaci ya yi da za a tabbatar da dokar don kara wakilcin mata a majalisun kasa da na jihohi.

A cewar Martina:

“Duk abubuwan da kuka ambata za su tabbata ne idan muka hada kai da yin magana da murya daya. Ya kamata mu kawar da maganar cewa mata ba sa son juna,”

Ta kuma bukaci karin mata da su tsaya takara a mukamai daban-daban tare da mara wa junansu baya.

Shugaban APC na kasa a Najeriya
Sugaban APC a Najeriya, Farfesa Yilwatda. Hoto: All Progressive Congress
Source: Twitter

A nata bangaren, shugabar Women’s Leadership Network, Dr Fauziya Buhari-Ado, ta ce an kafa kungiyar ne domin karfafa wakilcin mata da matasa a siyasa da shugabanci.

Ta bayyana cewa mata da matasa ne ginshikin tattalin arzikin Najeriya, amma har yanzu ba su da isasshen wakilci a siyasa da harkokin gwamnati.

Momodu ya shawarci Tinubu kan Trump

A wani labarin, kun ji cewa fitaccen dan siyasa, Dele Momodu ya bukaci shugaba Bola Tinubu ya dauki mataki mai kyau game da barazanar Donald Trump.

Momodu ya yi kira ga Bola Tinubu da kada ya yi wa lamari kallo ta fuskar siyasa ko abin da ya yi kama da hakan.

Kara karanta wannan

A karshe, za a iya saka matatun man Najeriya a kasuwa domin sayar da su

Ya bukaci amfani da fitattun 'yan Najeriya da suka yi suna a duniya domin su tattauna da Trump ko za a yi nasarar shawo kan kalubalen.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng